GABATARWA.



WWW.TAFARKINSUNNAH.BLOGSPOT.COM

WANNAN SHAFI YANA DAUKE DA HADISAN ANNABI(SAW)ACIKIN HARSHEN HAUSA. IDAN ANGA MUNYI KUSKURE ASANAR DA MU.ALLAH YAYI MUNA JAGORA AMEEN!



DAMIN AIKO DA GYARA KO KARIN BAYANI;
{tafarkinsunnah@gmail.com]

Nov 24, 2011

ARBA'UNA HAADITH (50) HADISI NA HAMSIN


An karɓo daga Abdullahi ɗan Busur, (R.A) yace wani mutum (mazaunin karkara ) yazo wurin Annabi (ﷺ),   yace ya Manzon Allah shari’oi sun yi mana yawa a bamu wani babu gamamme da zamu riƙe. Sai Annabi (ﷺ),  yace "kada harshenka ya bushe wajen
ambaton Allah "Ahmad ne ya rawaito shi (#188, 190).

SHARHI;

Wannan hadisin yana nuna cewa, wani mutum mazaunin karkara yazo wurin manzon Allah (ﷺ),  yace dashi ya manzon Allah shari’oi sun yi mana yawa an ce kayi kaza, ka bar kaza, don haka a faɗi wani guda ɗaya wanda zamu riƙe wanda ba gudu baja da ya sai anyi shi ko ana cikin me, Sai Annabi (ﷺ),  yace, kada harshenka ya bushe wajen ambaton Allah in dai kana son abin da zaka rike ba wahala kayi, komai kuɗinka komai talaucinka zaka iya yi ko kana da muƙami ko baka dashi kana kwance, a gadon asibiti ko a gida kake
matuƙar kana da rai zaka iya yi yace, to ga zikirin Allah abin da ake nufi ka zamanto mai ambaton Allah a tsaye ko ayaune, Allah yana cewa,
"الذين يذ كرو ن الله قيما وقعودا و على جنو بهم و يتفكرو ن فى خلق السمولت ولارض ) ال عمران."
Ma'ana (Waɗanda suke ambaton Allah atsaye da zaune, da in suna kwance kuma suna tunani akan halittar sammai da ƙassai) (Ali Imran 191)
Wannan shi ne cikon hadisi na hamsin idan an ƙara guda takwas waɗanda Ibnu Rajab Alhambali ya ƙara kenan, kuma wannan shi ne ƙarshen wannan fassarar llittafi mai albarka na Arba’una Hadis abin da duk muka faɗa na dai-dai Allah ya bamu lada a kai, wanɗa mukai kuskure, to Allah ya yafe mana.

(FASSARA DA SHARHI DA GA BAKIN GARIGAYI SHEIK JA’AFAR MAHAMUD ADAM {R} ).


1 comment:

KITABUT-TAUHID (Babi Na Goma Sha Biyar15)

  SHARHI Babukan da suka wuce sun yi magana a kan yana daga dangin shirka neman taimako wajen wanin Allah. Wannan babi kuma zai nuna maka ...