GABATARWA.



WWW.TAFARKINSUNNAH.BLOGSPOT.COM

WANNAN SHAFI YANA DAUKE DA HADISAN ANNABI(SAW)ACIKIN HARSHEN HAUSA. IDAN ANGA MUNYI KUSKURE ASANAR DA MU.ALLAH YAYI MUNA JAGORA AMEEN!



DAMIN AIKO DA GYARA KO KARIN BAYANI;
{tafarkinsunnah@gmail.com]

Aug 27, 2022

KITABUT-TAUHID (Babi Na Goma Sha Biyar15)

 

SHARHI

Babukan da suka wuce sun yi magana a kan yana daga dangin shirka neman taimako wajen wanin Allah. Wannan babi kuma zai nuna maka dalilan da suke nuna cancantar Allah da bauta shi kaɗai, Da kuma dalilan

da ke nuna kasawar wanin Allah wajen a bauta masa. Zai kawo siffofi da suke nuna cancantar Allah a bauta masa shi kaɗai da siffofi da suke nuna duk wanda ba Allah ba, yana da rauni bai dace a bauta masa ba. Abin da wannan babi da mai bi masa za su nuna mana kenan.

 

************************

Da faɗin Allah;

Shin suna haɗa Allah da wani, wanda ba ya halittar komai, alhalin su ne ake halittawa. Kuma ba sa iya taimaka musu, kuma ko da kawunansu ba sa iya taimakawa? (Al-Araaf 191-192)

Jul 13, 2022

KITABUT-TAUHID (Babi Na Goma Sha Hudu14)

 Yana Daga Shirka Neman Taimakon Wanin Allah Ko Roƙon Wanin Allah

________________

SHARHI

Mun riga mun san duk wani nau'in ibada da ake yi wa Allah (SWA), to idan a ka yi wa wani ba Allah ba, to ya zama shirka kenan. A nan Malam ya ce neman tsari wato istigatha" da wanin Allah shirka ne, kenan istigatha' ibada ne wanda ba wanda za a yi wa sai Allah. Kuma kamar yadda Allah ya yi umarni da sallah haka ya yi umarni da istigatha'wato neman tsari, kamar yadda ya ce:

"Idan wani mai zungura daga shaiɗan ya zungureka to ka nemi tsari daga wajen Allah, haƙiƙa shi (Allah) mai ji ne kuma masani." (Fussilat:36)

Don haka neman tsari ibada ce ba a yi da kowa

KITABUT-TAUHID (Babi Na Goma Sha Biyar15)

  SHARHI Babukan da suka wuce sun yi magana a kan yana daga dangin shirka neman taimako wajen wanin Allah. Wannan babi kuma zai nuna maka ...