GABATARWA.



WWW.TAFARKINSUNNAH.BLOGSPOT.COM

WANNAN SHAFI YANA DAUKE DA HADISAN ANNABI(SAW)ACIKIN HARSHEN HAUSA. IDAN ANGA MUNYI KUSKURE ASANAR DA MU.ALLAH YAYI MUNA JAGORA AMEEN!



DAMIN AIKO DA GYARA KO KARIN BAYANI;
{tafarkinsunnah@gmail.com]

Nov 18, 2011

ARBA'UNA HAADITH (43) HADISI NA ARBA'IN DA UKU

An karɓo daga ɗan Abbas (R,A) ya ce, Manzon Allah (ﷺ),  ya ce, “Ku riskar da kowanne rabon gado sananne ga ma’abotan wannan rabon, abin da ya ragu, to a ba namiji wanda

ya fi kusanci.” Bukhari (#6732) da Muslim (#1615) ne suka rawaito shi.
SHARHI;


Abin da wanna hadisi yake nufi shi ne, rabon gado kashi biyu ne: Akawai waɗanda ake basu da farali, wato masu rabo sananne, wanda shi kuma ya kasu kashi shida: ko a ce a baka rabin dukiya (1/2), ko ɗaya bisa hudu (1/4) na dukiya, ko ɗaya bisa takwas(1/8) na dukiya, ko ɗaya bisa uku (1/3) na dukiya, ko biyu bisa ukun (2/3) na dukiya, ko ɗaya bisa
shida (1/6) na dukiya. Wannan shi ne farali guda shida! Duk wanda suke da rabin dukiya sanannu ne, mutane ne kasha biyar, ban da su ba a ba kowa; waɗanda ake ba kasha ɗaya bisa huɗu na dukiya, su ma waɗannan sanannu ne; kashi ɗaya bisa takwas na dukiya, su ma sanannu ne; kashi biyu bisa uku; ko kashi ɗaya bisa shida, duk waɗannan sanannu ne, ayoyin Alkur’ani sun yi bayaninsu. To wannan shi ne farali! abin da ba wannan ba, sai a ce masa asibci, shi ne mutumin da ba a ce ɗauki kaza bisa kaza ba. Lallai zai ci gado, amma ba a ce ɗauki kaza bisa kaza ba, shi dai yana cikin masu cin  gado. Idan waɗanda aka ce su ɗauki kaza bisa kaza an ba su, abin da ya yi ragowa nasa ne gaba ɗaya, ko shi da masu matsayi irin nasa, su raba, namiji yana da rabon mata biyu.
(FASSARA DA SHARHI DA GA BAKIN GARIGAYI SHEIK JA’AFAR MAHAMUD ADAM {R} ).

No comments:

Post a Comment

KITABUT-TAUHID (Babi Na Goma Sha Biyar15)

  SHARHI Babukan da suka wuce sun yi magana a kan yana daga dangin shirka neman taimako wajen wanin Allah. Wannan babi kuma zai nuna maka ...