Posts

KITABUT-TAUHID (BABI NA UKU 3)

Duk Wanda Ya Tabbatar Da Tauhidi Zai Shiga Aljanna Ba Tare Da Hisabi Ba _______________ SHARHI;
Wannan babin kamar cukon babin baya ne. Babin baya ya yi bayani akan falalar tauhidi da yadda yake kankare zunubai. Wannan kuma zai yi bayanin cewa, duk wanda ya tabbatar da tauhidi, haƙiƙanin tauhidi, to zai shiga aljanna ba tare da hisabi ba, wato babu ƙididdugar ayyuka, kuma babu azaba. Ana tashi ƙiyama,

KITABUT-TAUHID (BABI NA BIYU 2)

Falalar Tauhidi Da Yadda Yake Kankare Zunubai
     Da fadin Allah; الذين آمنوا ولم يلبسوا إيمانهم بظلم أولئك لهم الأمن وهم مهتدون ”Waɗanda suka yi imani, ba su garwaya imaninsu da zalunci ba, lallai su ne suke da amintuwa, kuma su ne shiryayyu.”(1) (An'aam: 82) __________________ SHARHI;
(1)Wannan aya ta zo a daidai inda aka ba da ƙissar Annabi Ibrahim (AS) na muƙabala da ya yi da mutanensa da hana su bautar gumaka, sai ake tambaya cewa, da su mushirikan da Annabi Ibrahim waye a kan shiriya? Sai Allah ya ba da amsa

KITABUT-TAUHID (BABI NA ƊAYA 1)

KITABUT-TAUHID(1) Da fadin Allah Ta’ala; (وما خلقت الجن والإنس إلا ليعبدون) "Kuma ban halicci aljanu da mutane ba, sai domin su bauta mini."  (Zaariyaa; 56)(2)­­­ __________________________
SHARHI (1)  Abin da tauhidi yake nufi shi ne kadaitawa, Wato daga Kalmar wahhada, Malam a nan ya na nufin Kitabut-tauhidillahi wato llttafin kaɗaita Allah. Kaɗaita Allah, kuma

KITABUT-TAUHID (SHIMFIƊA):

Tauhidi, shi ne ginshikin al’amari gabaɗaya. Domin tabbatar datauhidi ne Allah  ya saukar da Iittattafai, kuma ya turo da manzanni. Sallah, azumi, zakka, hajji, kyautatawa iyaye, kyautatawa makwabta da duk Waɗansu

ARBA'UNA HAADITH (50) HADISI NA HAMSIN

An karɓo daga Abdullahi ɗan Busur, (R.A) yace wani mutum (mazaunin karkara ) yazo wurin Annabi (SAW)  yace ya Manzon Allah shari’oi sun yi mana yawa a bamu wani babu gamamme da zamu riƙe. Sai Annabi (SAW) yace "kada harshenka ya bushe wajen

ARBA'UNA HAADITH (49) HADISI NA ARBA'IN DA TARA

An karɓo daga Umar ɗan Khaɗɗab (R.A) daga Annabi yace, da ace kuna dogara ga Allah haƙiƙanin dogaro da Shi da Allah ya azurta ku kamar yadda yake azurta tsuntsaye. Suna sammako da yunwa amma suna dawowa

ARBA'UNA HAADITH (48) HADISI NA DA TAKWAS

An karɓo daga Abdullahi ɗan Amru (R.A) daga Annabi (SAW) ya ce, “abubuwa guda huɗu wanda suka kasance tare da shi ya kasance munafiki, wanda siffa ɗaya ta kasance tare da shi daga huɗun nan, to lallai siffa ta munafinci na tare da shi, har sai ya bar ta, idan yayi magana, ya zamanto ya yi ƙarya, Idan ya yi alƙwari, sai ya

ARBA'UNA HAADITH (47) HADISI NA ARBA'IN DA BAKWAI

An karɓo daga Miƙdamu ɗan Ma'adi Yakrib (R.A) ya ce "Naji Manzon Allah (SAW) yana cewa, "Dan Adam bai taɓa cika wani boki ba, ko wani ƙoƙo mafi sharri, sama da cikinsa ba. Ya ishi ɗan Adam waɗansu 'yan lomomi, wanda za su tsaida masa gadon bayansa (Yunwa ba zata galabaita shi ba). Idan dole (sai ya ci abinci da yawa), sai

ARBA'UNA HAADITH (46) HADISI NA ARBA'IN DA SHIDA

An karɓo daga ɗan Abu Burda, daga babansa, daga Abu Musal Ash’ariy (R.A) ya ce, Annabi (SAW) ya tura shi ƙasar Yemen, sai ya tambaye shi dangane da wani abin sha da ake yi a can, sai ya ce, “Menene abin?” Sai ya ce, “Albit’u da Almizru.” sai aka ce da Abu Burda, “Menene Albit’u?” sai ya ce,

ARBA'UNA HAADITH (45) HADISI NA ARBA'IN DA BIYAR

An karɓo daga Jabir ɗan Abdullahi (R.A) ya ce, “Naji Manzon Allah(SAW) a shekarar buɗe Makka, a lokacin (Manzon Allah(SAW) ) yana Makka, yana cewa “Lallai Allah da Manzonsa sun haramta sayar da giya da mushe da alade da gunki.” Sai aka ce, Ya Manzon Allah(SAW)! Ba mu labari game da kitsen mushe, ana shafawa a jikin jirgin ruwa, ana shafawa a fata, ana kunna fitilu da shi, (shin ya halatta ko bai halatta ba?).”

ARBA'UNA HAADITH (44) HADISI NA ARBA'IN DA HUDU

An karɓo daga A’isha (R.A) ta ce, Manzon Allah (SAW) ya ce, “Shayarwa tana haramta abin da haihuwa take haramtawa.” Bukhari (#2646) da Muslim (#1444) suka rawaito shi.
SHARHI;

Ma’ana, idan mace ta haife ka

ARBA'UNA HAADITH (43) HADISI NA ARBA'IN DA UKU

An karɓo daga ɗan Abbas (R,A) ya ce, Manzon Allah (SAW) ya ce, “Ku riskar da kowanne rabon gado sananne ga ma’abotan wannan rabon, abin da ya ragu, to a ba namiji wanda

ARBA'UNA HAADITH (42) HADISI NA ARBA'IN DA BIYU

An karɓo daga Anas ɗan Malik (R.A) ya ce, “Na ji Manzon Allah (SAW) yana cewa, Allah Maɗaukakin Sarki yana cewa, “Ya kai ɗan Adam! Lallai ba za ka bauta min ba, kuma ka sanya rai game da rahamata ba, face sai na gafarta maka ban damu ba. Ya kai ɗan Adam! Da a ce zunubanka zasu cika sashen sama gaba ɗaya, sannan ka nemi gafarata, sai in gafarta maka. Ya kai ɗan Adam!

ARBA'UNA HAADITH (41) HADISI NA ARBA'IN DA DAYA

An karɓo daga Abu Muhammad Abudullahi ɗan Amru ɗan As (R.A) ya ce, Manzon Allah (SAW) ya ce, “Ɗayanku ba ya zama mumini, har sai son zuciyarsa yana biyayya ga abin da na zo da shi.” Hadisin ne ingatacce, mai kyau, mun rawaito shi a cikin littafin Hujja da sanadi ingantacce.
SHARHI;
Wanna hadisi an karɓo shi daga Abu Muhamad, shi ne Abdullahi ɗan Amru ɗan As, ɗaya daga cikin ‘Abadila’ (wato waɗanda ake kira Abdullahi ) a cikin sahabbai,

ARBA'UNA HAADITH (40) HADISI NA ARBA'IN

An karɓo daga Abdullahi ɗan Umar (R.A) ya ce, Manzon Allah (SAW) ya dafa kafaɗata ya ce, “Ka kasance a duniya tamkar kai baƙo ne, ko kuma wanda yake kan hanya.” Ɗan Umar (R.A) yana cewa, “Idan ka kai yamma, kar ka yi jiran safiya, idan kuma ka wayi gari, to kar ka jira yamma. Ka riƙi aiki alheri lokacin lafiyarka, saboda lokain rashin lafiyarka. Ka riƙi aiki alheri lokacin rayuwarka, saboda ka

ARBA'UNA HAADITH (39) HADISI NA TALATIN DA TARA

An karɓo daga ɗan Abbas (R.A) ya ce Manzon Allah (SAW) ya ce, “Allah Ya yafe wa al’ummata, abin da ta yi dakuskure, da mantuwa, da abin da aka tilasta ta.” Hadisi ne mai kyau Ibnu Majah ne ya rawaito shi (#2045) da Baihaƙi a cikin Sunan.
SHARHI;
Waɗannan abubuwa guda uku an yafe wa

ARBA'UNA HAADITH (38) HADISI NA TALATIN DA TAKWAS

An karbo daga Abu Hurairata, (R.A) yace, manzon Allah yace Allah ta’ala yace duk wanda yayi gaba da waliyyina to na bashi sanarwa yazo yayi yaki dani. Bawana ba zai kusance ni ba, da wani abu da na fi kauna, sama da abin da na wajabta masa. Bawana ba zai gushe ba yana kusanta ta da nafiloli har sai na zamanto ina kaunarsa, idan na kaunacee shi, sai na kasance jinsa, da yake ji dashi, da ganinsa da yake gani dashi da hannunsa da yake damka dahsi da kafarsa da yake tafiya da ita.

ARBA'UNA HAADITH (37) HADISI NA TALATIN DA BAKWAI

An karbo daga Dan Abbas (R.A) daga manzon Allah (S.A.W) ciki irin abin abin da ya rawaito daga Ubangijisa yace, Allah ya riga ya rubuta ayyukan alheri da munanan ayyuka, wanda duk ya himmatu zai aikata awani kyakkywan aii sai bai samu aikatawa ba, Allah zai rubuta masa kyakkywana aikin guda dyaa cikakke,

ARBA'UNA HAADITH (36) HADISI NA TALATIN DA SHIDA

An karbo daga Abu hurairata (R.A) daga Annabi yace, wanda duk yakutar wa mumini wani bakin ciki daga bakin cikin duniya to Allah zai kautar da masa da wani bakin ciki daga bakin cikin irin bakin kiyama duk wanda ya kawo sauki ga wanda yake cikin tsanani, Allah zai kawo masa sauki a duniya da lahira, wanda ya suturce musulmi to Allah zai yi masa sutura a duniya d alahira lallai Allah yana cikin taimakon bawa matukar bawan ya kasance mai taimakon dan uwansa musulmi wanda duk ya kam wani tafarki yana neman ilmi a wannan tafarkin Allah zai saukaka masa hanyar shiga aljanna

ARBA'UNA HAADITH (35) HADISI NA TALATIN DA BIYAR

An karbo daga Abu Hurairata (R.A) y ace Manzon Allah Annabi (S.A.W). y ace “Kada ku rika yi wa juna hassada, kada ku yi kore kada ku kiyayya da juna, kada ku juya wa juna bayanku, kada sashenku ya yi ciniki a cikin cinikin dan uwansa. Ku kasance bayin Allah ‘yan uwan juna. Muslim dan uwan muslim ne, kada ya zalunce shi, kada

ARBA'UNA HAADITH (34) HADISI NA TALATIN DA HUDU

An karbo daga Abu Sa’id Al-Khuduriy (R.A) y ace “Na ji Manzon Allah Annabi (S.A.W).” yana cewa “Duk wanda ya ga abin ki, to ya gusar da shi da hannunsa, in ba shi da iko, ya gusar da shi da harshensa, in ba iko, to ya ki abin a zuci, wannan shi ne mafi raunin imani.(1)” Muslim ne ya rawaito shi (#49).

SHARHI;

Malamai suke ce, wannan hadisi

ARBA'UNA HAADITH (33) HADISI NA TALATIN DA UKU

An karbo daga Abdullahi dan Abbas (R.A) ya ce, Manzon Allah Annabi (S.A.W). ya ce, “Da za’a bai wa mutune dukkan da’awarsu, da wadansu sun yi da’awar dukiyar wadansu da jininsu’ sai dai hujja tana kan mai da’awa, rantsuwa kuma a kan wanda ya yi musu.”(1) Baihaki ne ya rawito shi a cikin litaffinsa sunan (J 10/sh 252). Wani sashi na hadisin yana cikin Bukhari da Muslim.

SHARHI;

Ma’ana, da duk da’awar da mutane za su yi, za’a dauka a ba su

ARBA'UNA HAADITH (32) HADISI NA TALATIN DA BIYU

An karbo daga Abu Sa’id, Sa’ad dan Malid dan Sinan Al-Khudiry (R.A) y ace Manzon Allah (S.A.W) y ace “Ba cuta babu cutarwa.”(1) Ibnu Majah ne ya rawaito shi, (#2341) da Darakuduni (#228) da waninsu Musnadan. Haka Imamu Malik ya rawaito shi a cikin Muwaddi (J2/sh 746) daga Amru dan Yahya Mursalan, bai ambaci Abu sa’id ba.

ARBA'UNA HAADITH (31) HADISI NA TALATIN DA DAYA

An karbo daga Abu Abbas Sahlu dan sa’ad Assa’idi (R.A) y ace “Wani mutum ya zo wajen Annabi (S.A.W) ya ce “Ya Manzon Allah! Nuna min aikin da idsan na aikata shi, Allah zai kaunace ni, mutane ma za su kaunace ni.” Sai (Annabi (S.A.W) ya ce ”Ka yi zuhudu cikin lamarin duniya, sao Allah ya kaunace ka, kuma ka nisanci abin da ke hunnun mutane,