GABATARWA.



WWW.TAFARKINSUNNAH.BLOGSPOT.COM

WANNAN SHAFI YANA DAUKE DA HADISAN ANNABI(SAW)ACIKIN HARSHEN HAUSA. IDAN ANGA MUNYI KUSKURE ASANAR DA MU.ALLAH YAYI MUNA JAGORA AMEEN!



DAMIN AIKO DA GYARA KO KARIN BAYANI;
{tafarkinsunnah@gmail.com]

Nov 8, 2011

ARBA'UNA HAADITH (29) HADISI NA ASHIRIN DA TARA

An karɓo daga Mu'azu ɗan Jabal (R.A) ya ce, "Na ce, Ya Manzon Allah! Ba ni labarin wani aiki da zai shigar da ni aljanna, ya kuma nisantar da ni daga wuta.“ Sai ya ce, "Haƙiƙa ka yi tambaya game da abin da yake mai girma, sai dai abu ne mai sauƙi ga wanda Allah ya sauƙaƙe shi gare shi. Ka bauta wa Allah, ba tare da ka haɗa shi da wani ba, kuma ka tsayar da sallah, kuma ka ba da zakka, kuma ka azumci Ramadan, sannan ka ziyarci ɗakin Allah." Sannan sai (Annabi ) ya ce, "Shin ba zan shiryar da kai ƙofofin alheri ba? Azumi garkuwa ne, sadaƙa kuma tana shafe kurakurai, kamar yadda ruwa yake kashe wuta, haka sallar mutum a cikin yankin dare. Sannan ya karanta (faɗin Allah), "...gefen jikinsu yana nisantar gurin kwanciyarsu. . . " har ya kai inda (Allah yake cewa ’Ya'amaluun' sannan sai Annabi ) ya ce, "Ba zan ba ka labarin kan al'amarin ba, da ginshikinsa da ƙololuwar Samansa?" Sai na ce "Eh!" sai ya ce, "Kan al'amarin (shi ne) musulunci, ginshiƙinsa kuwa salla, ƙololuwar samansa kuwa jihadi." (Sai Annabi  ) ya ce, "Ba zan ba ka labarin abin da yake mallakar kusan gaba ɗaya ba?" sai na ce "Ba ni labari." sai ya kama harshensa ya ce, "Ka riƙe wannan." Sai na ce, "Shin yanzu za a kama mu da maganar da muka yi?" sai (Annabi ) ya ce, "Da ma mahaifiyarka ta rasa ka! Akwai abin da yake jefa mutane wuta a kan fuskokinsu (ko ya ce) kan hancinsu, sai sakamakon abin da harshensu ya faɗa." Tirmizi (#2616) ya ce, hadisi ne mai kyau, ingantacce.


SHARHI
Wannan hadisi daga Mu'azu ɗan Jabal (R.A) ya ce, "....Ba ni labarin wani aiki da zai shigar da ni aljanna, ya kuma nisantar da ni daga wuta...." Wannan ne ya sa ake cewa fatawar sahabbai ta sha bamban da tamu, saboda su kullum nema suke ina inda za a shiga aljanna, ina inda za a sami tsira da tsari daga wuta. Haka za ka ji kullum suna tambayar Annabi (), sai Annabi () ya zana musu dangogi masu yawa, don idan ka kasa yin wancan, ka yi wannan.

Dangane da faɗin Annabi () cewa, "Haƙiƙa ka yi tambaya game da abin da yake mai girma, sai dai abu ne mai sauƙi ga wanda Allah ya sauƙaƙe shi gare shi....." wannan shi ya sa ake son kullum ka roƙi Allah tabbatuwar shiriya a kan tafarki madaidaici. Duk yadda ka kai da son gaskiya da begenta, in ba Allah ne ya yi ma gam-da katar ba, ba za ka dace da ita ba. Faɗin Annabi () kuwa cewa, "....Azumi garkuwa ne...." yana nufin azumi na nafila. Don azumin wajibi ya riga ya gabata a can, a wani hadisin ya ce, "....azumi garkuwa ne zai kare mutum daga wuta...." [Duba Tirmizi (#764)] saboda haka Annabi ke kwaɗaitar da mu da yawaita azumin nafila, bayan mun sauke na farilla. Azumin nafila kuwa yana da yawa: Litinin da alhamis ana yi; shida cikin Shawwal bayan ƙaramar sallah kenan, wanda yake kankare zunubin shekara ɗaya gaba ɗaya; azumin Tasu'a da Ashura, tara da kuma goma ga watan Muharram, shi ne farkon azumin da aka wajabta a musulunci, daga baya aka wajabtar da Ramadan, shi wancan aka mai da shi ya zama mustahabbi; azumi uku a kowane wata, musamman ma sha uku da sha hudu da sha biyar ga wata. A taƙaice duk wannan dangogin azumi, azumi ne na nafila da zai taimaka wa mutum. Azumin nafila idan za ka yi sama da haka, ka ga kana da ƙarfin da za ka yi sama da abin da muka ambata, to sai ka yi azumi yau, gobe ka ƙi yi, jibi ka yi, gata ka huta, citta ka yi. Wannan shi ne Siyamu Dawud da Annabi () ya ce, "Azumin da Allah ya fi so, shi ne azumin Annabi Dawud, ya yi yau, ya huta gobe, jibi ya yi, gata ya huta." [Duba: Sahih Al Bukhari (#1131) da Sahih Muslim (#1159)]. Saboda haka ba sunna ba ne ka je ka jeranta azumi kwanakj masu yawa na nafila! Sai dai ka yi yau gobe ka huta, jibi ka yi, gata ka huta, haka Annabi () ya koya wa sahabbai. Ba jarumta ba ne don ka yi wata biyu a jere ko wata uku a jere, ka saɓa wa sunnar Annabi () ba ka sani ba. Shi addinin musulunci ba wai jarumta ko gwaninta yake so ba, a'a! abin da ake so ka yi, sai ka yi, shi kenan magana ta ƙare, komai ƙankantarsa, kada ka raina shi. Sadaƙa ma a nan, ana nufin ta nafila, domin maganar zakka, ta riga ta gabata a baya.

Sallar mutum a cikin wani yanki na dare, wato ƙiyamullaili kenan, za ka yi cikin jam'i, za ka yi kai kaɗai, za ka yi kai da matarka, duk wanda ka sami dama ka yi. Sai dai ƙiyamullaili a cikin jam'i ya fi falala, sama da ka yi kai kaɗai. Wannan ita ce fatawar da muka tafi a kai, don akwai haidisi a kai, inda Annabi () ya ce, "Duk wanda ya tsaya da liman, suka yi sallar dare, har liman ya yi sallama, sannan kai ma ka yi sallama, za a rubuta maka kamar ka sallaci daren gaba ɗaya." [Tirmizi (#806) da Nasa'i (#1605) da Ibnu Majah (#1327) suka rawaito shi]. Amma idan kai kad‘ai ne, to sai ka yi adadin da ake buƙata, sannan za a ce ka yi ƙiyamullaili, amma matuƙar a bayan liman ne, ko raka'a huɗu ya yi, ya tafi gida, ko shafa’i da wutiri kaɗai kuka yi da liman ya tafi gida, za a rubuta maka ka sallaci dare gaba-ɗaya, ka ga ba za ka haɗa da wanda ya yi shi kaɗai ba.

Faɗin Manzon Allah () ga Mu‘azu cewa, sakilatka ummuka jumloli ne da ba a nufin zahirin ma'anarsu. Larabawa sun saba suna amfani da su, shi ya sa ba a yin fassara ta kai-tsaye a kan irin wannan, sai ya kasance ka fassara su da abin da bai dace ba. Fassara ta kai-tsaye, sakilatka ummuka yana nufin da ma dai mahaifiyarka ba ta haife ka ba. Ka ga ba zai yiwu Annabi () ya faɗa masa haka ba! Amma su Larabawa sukan faɗi haka ga mutumin da bai fahimci wani abin da ya kamata ya fahimta ba, su ce, "Wane! Wane irin tunani ne gare ka? Ina hankalinka ya tafi har ka kasa fahimtar abin da muke nufi?“ Kamar haka ne Annabi yake nufi.

Faɗin Manzon Allah () cewa shin, "....akwai abin da yake jefa mutane wuta a kan fuskokinsu...." ko ya ce, "....kan hancinsu...." face girbe-girben harsunansu? wannan yana nuna illar munanan maganganu ga mutane, kamar gori ko kazafi ko faɗin abin da bai dace ba da shari'a, wannan galibi shi ke jawo a jefa mutum a wuta, fuska ta fara zuwa, ko karan-hancinsa ya fara zuwa. Shi harshe da shi ne waɗancan za su gyaru; ta iya yiwuwa ka yi sallah, wanda ana zaton tana nisantar da mutum daga wuta, ta kai shi aljanna; ka yi azumi‘; ka yi zakka; ka yi dukkan abin da ake buƙata, amma harshenka ba ka kula da shi ba, ka zagi wannan, ka cuci wancan, ka yi da wannan, da makamancin wannan, sai a tashi ranar ƙiyama ba ka da komai na ladan waɗannan abubuwan, duk an ɗauka an ba waɗannan, kamar yadda hadisin Abu Huraira yake nunawa. Ya ce, Annabi () ya ce, "Kun san waye matalauci?" sai suka ce, "Wanda ba shi da kuɗi, ba shi da haja." Sai Annabi () ya ce, "Wannan ba shi ne matalauci ba. Matalauci a lahira, shi ne wanda zai zo ranar tashin ƙiyama ga sallah, ga azumi, ga hajji, ga zakka, amma ya zagi wancan, ya zubar da mutuncin wane, ya zubar da jinin wannan, sai a dinga ɗaukar ladansa a ba wa waɗancan mutanen, har ayyukan alheri na ladansa su ƙare, mutane ba su gama zuwa ba, suna neman bashi a wurinsa, sai a ɗebi ayyukansu na zunubi a ɗora masa, daga ƙarshe sai a kai shi wuta." [Duba Sahihi Muslim (#2581)].

2 comments:

  1. Asalamu alaykum, Allah ya kara mana imani ya kuma sa mudace Ameen,sadai kuma dan yi gera a rubutun angode

    ReplyDelete

KITABUT-TAUHID (Babi Na Goma Sha Biyar15)

  SHARHI Babukan da suka wuce sun yi magana a kan yana daga dangin shirka neman taimako wajen wanin Allah. Wannan babi kuma zai nuna maka ...