GABATARWA.



WWW.TAFARKINSUNNAH.BLOGSPOT.COM

WANNAN SHAFI YANA DAUKE DA HADISAN ANNABI(SAW)ACIKIN HARSHEN HAUSA. IDAN ANGA MUNYI KUSKURE ASANAR DA MU.ALLAH YAYI MUNA JAGORA AMEEN!



DAMIN AIKO DA GYARA KO KARIN BAYANI;
{tafarkinsunnah@gmail.com]

Nov 24, 2011

ARBA'UNA HAADITH (49) HADISI NA ARBA'IN DA TARA


An karɓo daga Umar ɗan Khaɗɗab (R.A) daga Annabi yace, da ace kuna dogara ga Allah haƙiƙanin dogaro da Shi da Allah ya azurta ku kamar yadda yake azurta tsuntsaye. Suna sammako da yunwa amma suna dawowa
 da yamma suna ƙoshe. Imam Ahmad (# 01,52) da Tirmizi (#2344) da Nasa’i a cikin Sunnan Alkubra (J 8/ sh 79) da Ibnu Majah (#4164) da Ibnu Hibban ya inganta shi (730) da Hakin (418) Tirmizi yace, hadisi ne ingantacce.


SHARHI;


Tsuntsu ba ya ajiye abincin gobe. In yaje yau. Yayi kiwo shi kenan gobe kuma ya bar ta ga hannun Allah. A nan ba wai ana nufin kada mu ma mu ajiye abincin gobe ba, ba haka hadisin yake nufi ba. Abi da hadisin yake nufi ,irin yadda tsuntsu ya ɗauka cewa in ya fita da safe, Allah zai bashi to lallai ka ɗauka cewa in ka fita ka nema, lallai Ubangiji na iya baka irin yaddayake wa tsuntsu Ma’ana ya zamanto zuciyarka ta rayayu da cewa Allah zai baka, ban daShi ba mai baka, kuma gaɓɓanka suna aiki tuƙuru don neman abin gurin Allah. Wannan shine tawakkalin da ake so.


(FASSARA DA SHARHI DA GA BAKIN GARIGAYI SHEIK JA’AFAR MAHAMUD ADAM {R} ).

No comments:

Post a Comment

KITABUT-TAUHID (Babi Na Goma Sha Biyar15)

  SHARHI Babukan da suka wuce sun yi magana a kan yana daga dangin shirka neman taimako wajen wanin Allah. Wannan babi kuma zai nuna maka ...