GABATARWA.



WWW.TAFARKINSUNNAH.BLOGSPOT.COM

WANNAN SHAFI YANA DAUKE DA HADISAN ANNABI(SAW)ACIKIN HARSHEN HAUSA. IDAN ANGA MUNYI KUSKURE ASANAR DA MU.ALLAH YAYI MUNA JAGORA AMEEN!



DAMIN AIKO DA GYARA KO KARIN BAYANI;
{tafarkinsunnah@gmail.com]

Nov 24, 2011

ARBA'UNA HAADITH (47) HADISI NA ARBA'IN DA BAKWAI


An karɓo daga Miƙdamu ɗan Ma'adi Yakrib (R.A) ya ce "Naji Manzon Allah (ﷺ),  yana cewa, "Dan Adam bai taɓa cika wani boki ba, ko wani ƙoƙo mafi sharri, sama da cikinsa ba. Ya ishi ɗan Adam waɗansu 'yan lomomi, wanda za su tsaida masa gadon bayansa (Yunwa ba zata galabaita shi ba). Idan dole (sai ya ci abinci da yawa), sai
ya kasa cikinsa kasha uku, kashi ɗaya abinci, kashi na biyu ruwan sha, kashi ɗayan ya bar wa numfashi."
Ahmad (J4/ sh 132) da Tirmizi (#2380) da Ibnu Majah (3349) Tirmizi ya ce, Hadisi ne mai kyau.

SHARHI;



Wannan shi ne ladabin cin abinci kenan da Annabi (ﷺ),  ya koyar da mutane. Annabi (ﷺ),  ya ce, ka kasa cikin ka uku. Don haka sai malamai suke cewa, wannan abin da Annabi (ﷺ),  ya bayar shin umarni ne na wajibi idan an ƙi bin sa an yi saɓo, ko kuma shiryarwa ce? idan ka kama wannan abu, ka kasa cikinka uku, zai fi dacewa, kuma ya tabbatar da lafiya, kuma kana da ladan biyayya ga Annabi (ﷺ),  dangane da abin da ya yi na shiryarwa, amma in ka cika cikinka, ka tashi ba ka son komai,ba ka yi wani zunubi ba. Akwai malaman da suke da wannan ra’ayi na ƙarshe cewa, ka ɗauki abin da aka fi so, amma in ka cika cikinka ba komai. Suka ce ai Abu Hurairata (RA) ya cika cikisa a gaban Annabi (ﷺ),  kuma Annabi (ﷺ),  bai ce masa komai ba. Abu Hurairata (RA) yana jin yunwa sai aka kawo sadakar nono kofi ɗaya. Abu Hurairata (RA)  ya ce, so nake Manzon Allah (ﷺ),  ya ce, "Shanye!" ko ya ɗan kurɓa ya ba ni kawai sai Annabi (ﷺ),  ya ce, "Jeka ka kirawo wane da wane, suna nan a zaune." Ya ce, ya nono kofi ɗaya a ce in kirawo wane da wane. Sai ya yi haƙuri ya je ya ce "Annabi (ﷺ),  ya ce, ku zo!" Sannan aka ce masa, ba wa wane ya sha, miƙa wa wane shi ma. Duk sai da kowa yasha ya ƙoshi, sai Annabi (ﷺ),  ya ba Abu hurairata (RA) ya ce, "Sha!"  Ya ce, "Na sha, na sha." Annabi (ﷺ),  ya ce, "Ƙara dai!" Har yace wallahi ya ma’aikin Allah, babu wani wuri da ya rage, babu, ya cika, ya gama. Ka ga a nan a gaban Annabi (ﷺ),  Abu Hurairata (RA) ya cika cikinsa, ba bin da ya rage a ciki. To shi ne suka ce, in da haramun ne Annabi (ﷺ),  ba zai bashi dama ya yi wanan ba (Duba Bukhari #6452).

(FASSARA DA SHARHI DA GA BAKIN GARIGAYI SHEIK JA’AFAR MAHAMUD ADAM {R} ).

No comments:

Post a Comment

KITABUT-TAUHID (Babi Na Goma Sha Biyar15)

  SHARHI Babukan da suka wuce sun yi magana a kan yana daga dangin shirka neman taimako wajen wanin Allah. Wannan babi kuma zai nuna maka ...