GABATARWA.



WWW.TAFARKINSUNNAH.BLOGSPOT.COM

WANNAN SHAFI YANA DAUKE DA HADISAN ANNABI(SAW)ACIKIN HARSHEN HAUSA. IDAN ANGA MUNYI KUSKURE ASANAR DA MU.ALLAH YAYI MUNA JAGORA AMEEN!



DAMIN AIKO DA GYARA KO KARIN BAYANI;
{tafarkinsunnah@gmail.com]

Nov 24, 2011

ARBA'UNA HAADITH (48) HADISI NA DA TAKWAS


An karɓo daga Abdullahi ɗan Amru (R.A) daga Annabi (ﷺ),  ya ce, “abubuwa guda huɗu wanda suka kasance tare da shi ya kasance munafiki, wanda siffa ɗaya ta kasance tare da shi daga huɗun nan, to lallai siffa ta munafinci na tare da shi, har sai ya bar ta, idan yayi magana, ya zamanto ya yi ƙarya, Idan ya yi alƙwari, sai ya
zamanto ya saɓa, Idan an yi rigima dashi, sai ya ƙetare dokar Allah, idan kuma aka ƙulla alƙawari, to zai yaudare ka. Bukhari (#34) da Muslim(#58) suka rawaito shi.

SHARHI;


Waɗannan siffofi guda huɗu in sun taru ga mutum, to ya zama munafiki, in kuwa ɗaya ce, to wanan ya zama yana da siffa ta munafunci.To amma abin da ake nufi da munafunci a nan gurin, munafuncin aiki. Don munafunci iri biyu ne: akwai Annifaƙul Amali,
munafunci a cikin aiki, da Kuma Annifaƙul I’itiƙadi, munafunci na zuci, wanda yake nufin mutum ya bayyana musulunci a zahiri, amma a zuciyarsa yana nan kan addininsa na kafirci. To duk mai wannan ba musulmi ba ne, ko da ya rantse. Don munafukai masu irin wannan, sai da suka zo wajen Annabi (ﷺ),  suka rantse suka ce sun yarda da shi amma Allah ya ƙaryata su Allah yace,
اذا جاء ك المنفقون قالو انك لر سو ل الله و الله يعلم انك لر سو له و
الله ان المنفقين لكذ بون ( المنا فقون:
(Idan Munafukai suka zo wajenka, suka ce, "Mun shaida kai Manzon Allah ne!” Allah ya san kai manzonsa ne, Allah ya shaida haƙiƙa Munafukai ƙarya suke ) (Al-munafuƙun 1)
و من الناس من يقول ءامنا با الله وباليوم الا وم هم ب مو منين: البقرة.
(A cikin mutane akwai waɗanda za su ce, "Mun yi imani da Allah da ranar ƙarshe"alhali su ba Muminai ba ne) [Al-Baƙara: 8]
To wannan shi ne munfuncin zuci, ƙudure kafirci a zuciya, amma mutum yana bayyana musulunci a harshensa, wannan ba musulmi ba ne, kuma irin waɗannan su ne Allah yace akansu,
ان المنفقون فى الدرك الاسفل من النار ولن تجد لهم نص) النساء:
(Hakika munafukai suna ƙasan wuta, kuma ba zaka sami wani mataimaki a tare da su ba.) [Annisa’i]
ان المنفقون بخد عو ن الله وهو خد عهم و اذ قا مو الى الصوة قامو كسالى يراءون الناس ولا يذ كرو ن الله الا قليلا) النساء:
(Haƙiƙa munafukai suna yaudarar Allah, Amma Allah yana mayar musu da yaudararsu akansu, idan suka tashi yin sallah, sai su tashi suna kasala, suna yi (Sallar) don mutane su gani, ba sa ambaton Allah, sai zan kaɗan) [Annisa’i:142]
Duk ayar da tazo ta nuna dawwama a cikin wuta ga munafukai, to da irin waɗannan munafukai take.
Kashi na biyu shi ne, munafunci a aikace, zuciyarka da imani, amma kana da wani aiki wanda bai kamata a ce kai musulmi ne kake yi ba, aikin irin aikin munafukai ne. To irin wannan, idan mutum ya yi, sai a ce ya yi aikin munafunci, amma ba ma cewa shi munafuki ne, mu saukar da faɗin Allah a kansa, "Haƙiƙa munafukai suna ƙasan wuta...." wannan ba ta shafe shi ba. Saboda kar mutum ya yi amfani da wannan hadisin, ya kafirta ‘yan uwansa, ba tare da ya fahimta ba, dole sai ya ware, Annifaƙul I’itiƙadi, wanda ya yi shi ya zama kafiri, amma Annifakul Amali, duk wanda ya yi shi yana nan a matsayinsa na musulmi, amma fasiƙin musulmi ne.

(FASSARA DA SHARHI DA GA BAKIN GARIGAYI SHEIK JA’AFAR MAHAMUD ADAM {R} ).

No comments:

Post a Comment

KITABUT-TAUHID (Babi Na Goma Sha Biyar15)

  SHARHI Babukan da suka wuce sun yi magana a kan yana daga dangin shirka neman taimako wajen wanin Allah. Wannan babi kuma zai nuna maka ...