GABATARWA.



WWW.TAFARKINSUNNAH.BLOGSPOT.COM

WANNAN SHAFI YANA DAUKE DA HADISAN ANNABI(SAW)ACIKIN HARSHEN HAUSA. IDAN ANGA MUNYI KUSKURE ASANAR DA MU.ALLAH YAYI MUNA JAGORA AMEEN!



DAMIN AIKO DA GYARA KO KARIN BAYANI;
{tafarkinsunnah@gmail.com]

Nov 18, 2011

ARBA'UNA HAADITH (45) HADISI NA ARBA'IN DA BIYAR

An karɓo daga Jabir ɗan Abdullahi (R.A) ya ce, “Naji Manzon Allah(ﷺ),  a shekarar buɗe Makka, a lokacin (Manzon Allah(ﷺ),  ) yana Makka, yana cewa “Lallai Allah da Manzonsa sun haramta sayar da giya da mushe da alade da gunki.” Sai aka ce, Ya Manzon Allah(ﷺ), ! Ba mu labari game da kitsen mushe, ana shafawa a jikin jirgin ruwa, ana shafawa a fata, ana kunna fitilu da shi, (shin ya halatta ko bai halatta ba?).”


sai ya ce “A’a! wannan haramun ne.” Sannan sai manzon Allah (ﷺ),  ya ce, “Allah Ya la’anci yahudawa, Allah Ya haramta musu kitse, sai suka ƙawata shi, sannan suka sayar da shi, suka cinye kuɗinsa. Bukhari (#2236) da Muslim (#1581) suka rawaito shi.

SHARHI;


Bai halatta ka sayar da giya ba! Kar ka ce ba na sha shi kenan, sayarwa ma zunubi ne. haka ma mushe; ragonka ya mutu yanzu yanzu nan, sai wani arne kusa da kai ya ce, ka sayar masa, sai ka ce ai tunda arne ne, bari in sayar masa, wannan bai halatta ba. Sai dai ka je ka jefar a wani wuri, in ya je ya ɗauka, wanna ba da yawunka ba. Ko ya zama kana sayar da alade, duk wannan bai halatta ba. Ko ya zama kana sayar da gumaka, su ma bai halatta ba. Gumaka su ne irin mutum-mutumi da za a yi, na mutum ko na wata dabba ko na tsuntsu, wannan duk haramun ne. Bai halatta ba ka yi wani hoton ɗan ga-ruwa ya ɗauko garwar ruwa biyu, bature ya yi sha’awa, ya gani ya saya. Ko kazo kayi wani abu ka ƙasa, ko wani tsuntsu ko kada ko akwaɗo, duk abin da kayi shi, in dai halitta ne (mai rai), ya zama gunki, bai halatta ka sayar dashi ba. Haka nan kazo ka yi zane na wani babban mutum, ka yi art ɗinsa, ka kai masa, duk haramun ne, bai halatta ba. Amma ‘yar tsana wadda ake don wasan yara, wannan ya halatta. Za ka iya saka ka ajiye a gida don yara su yi wasa, akwai hadisin da ya nuna haka, hadisin Aisha. Idan yara sun girma sun gama wasa, sai a ɗauke ta a jefar, in an sami wani ɗan ƙaramin yaron sai a sayo masa, wannan ya halatta.
    Ibnu Rajab Al-Hambali yana cewa, “Dukkan wani littafi da zai yi jagorancin ka zuwa ga bautar wanin Allah, to irin wannan littafin cinikayya da shi haramun ne.” littafin da yake cike da saɓon Allah, kamar litttafai irin na batsa, kamar mujallu irin na batsa, kamar nobel da suke ɗauke da labarai na laifi, haramun ne sayar da su. Haka nan hotunan ‘yan kokawa, manya-manyan hotuna, wani ƙaton ɗan kokawa ka gan shi kamar alade a jiki, ka zo ka saya ka rataya a gidanka, duk haramun ne, ko hotunan mata duk haramu ne, bai halatta ba.
  Sai akace Manzon Allah (ﷺ), ! Bamu labari game da kitsen mushe, ana shafawa ajikin jirgin ruwa…” ma’ana jikin katakon da kayi kwalkwalen da dashi, ta yadda wannan katakon ba zai lalace ba. Sannan wannan kitsen na mushe,”… ana shafawa a fata don ta yi laushi, a yi amfani da ita, ko ruwa ya doke ta ba zata lalace ba. Sannan waɗansu sukan kunna fitilar aci balbal da wannan kitsen na mushe, shin waɗannan ya halatta ko bai halatta ba? Sai Annabi (ﷺ),  ya ce,”….Wannan haramun ne.” To anan sai malamai su kai saɓani; shin sayarwa aka hana, ko amfani dashi? waɗansu suka ce, a nan wurin Annabi (ﷺ),  yana haramta yin amfani da wannan kitsen ne ta wannan hanya. waɗansu suka ce ba amfani da shi aka haramta ba, sayarwa ne ya haramta, don tana iya yiwuwa a haramta maka abu, amma ba’a haramata maka shi ba ta wata kafar. Misali ya halatta ka ajiye kare a gida don ya yi maka gadi amma bai halatta maka cinikin kare ba, sai dai wani ya baka kyauta, ko ka je kama a wani wuri.
Sannan sai Annabi (ﷺ),  ya ce, Allah ya la’anci yahudawa, Allah ya haramta masu kitse, sai suka ƙawata shi, sannan suka sayar da shi, suka cinye kuɗinsa.” Ma’ana, sunyi amfani da haramun, su suna ganin cin aka haramta musu, don haka idan sun sayar, ba wani abu. Su yahudawa kullum suna dabara wajen halatta abin da yake haramun, to sai Annabi (ﷺ),  ya nuna Allah Ya la’ance su.
(FASSARA DA SHARHI DA GA BAKIN GARIGAYI SHEIK JA’AFAR MAHAMUD ADAM {R} ).

No comments:

Post a Comment

KITABUT-TAUHID (Babi Na Goma Sha Biyar15)

  SHARHI Babukan da suka wuce sun yi magana a kan yana daga dangin shirka neman taimako wajen wanin Allah. Wannan babi kuma zai nuna maka ...