GABATARWA.



WWW.TAFARKINSUNNAH.BLOGSPOT.COM

WANNAN SHAFI YANA DAUKE DA HADISAN ANNABI(SAW)ACIKIN HARSHEN HAUSA. IDAN ANGA MUNYI KUSKURE ASANAR DA MU.ALLAH YAYI MUNA JAGORA AMEEN!



DAMIN AIKO DA GYARA KO KARIN BAYANI;
{tafarkinsunnah@gmail.com]

Nov 15, 2011

ARBA'UNA HAADITH (35) HADISI NA TALATIN DA BIYAR


An karvo daga Abu Hurairata (R.A) ya ce, Manzon Allah (ﷺ) ya ce, "Kada ku riqa yi wa juna hassada, kada ku yi kore, kada ku yi qiyayya da juna, kada ku juya wa juna bayanku, kada sashenku ya yi ciniki a, cikin cinikin xan uwansa. Ku kasance bayin Allah, 'yan uwan juna. Musulmi xan uwan musulmi ne, kada ya zalunce shi, kada ya kunyatar da shi, kada ka yi masa qarya, kada ya wulaqantar da shi. Tsoron Allah yana nan (har sau uku)." Yana nuna kirjinsa, "Ya ishi mutum sharri, ya rinqa tozartar da xan uwansa musulmi. Jinin kowanne musulmi da dukiyarsa da mutuncinsa, haramun ne a kan musulmi“ Muslim ne ya rawaito shi (#2564).

                      
SHARHI

Abin da ake nufi da 'hassada', shi ne ka riqa burin ina ma ni'imar da wane yake ciki, ta taho, ta bar shi; ina ma dukiyar wane ta ragu, jarinsa ya lalace; ka rinqa jin ina ma muqamin da aka bai wa wane ya zo ya rasa, to wannan ita ce hassada. Kuma siffa ce ta yahudu, sun fi kowa sanin Annabi (ﷺ) da siffofinsa, amma hassada ta hana su yin imani da shi. Don haka, ka yi qoqarin ka wanke zuciyarka daga yi wa xan uwanka musulmi hassada. Ko da mutum yana qoqarin yin takara da kai kan wasu al'amura na duniya, kai kar ka yi takara da shi. Lallai mutum ya kasance ya tarbiyatar da kansa a kan haka. Lafazin ‘kore' da ya zo a wannan hadisi, shi ne kana da rumfa a kasuwa, kana sayar da jakunkuna, sai na zo zan sayi jaka, muna cikin ciniki, ka ce naira dari biyu, ni kuma ina cewa naira tamanin, kawai sai wani xan kore ya zo ya xauki irin wannan jakar ya ce, "Don Allah ka sayar min da wannan jakar xari da hamsin." Shi wanda ya zo ya yi hakan xin, ya yi ne fa don saboda ni. Ya ce, "Xari da hamsin, ka sayar?" Ya ce, a'a! ya ce, "To xari da sittin da biyar.", wai dole sai ya zurma ni na shiga, a yi da kyar a sayar masa xari da saba'in. Bayan kuwa ciniki ne na bogi, na qarya, ba gaskiya ba ne, don kawai ni in kai xari da saba'in, farashinta kuwa naira tamanin. To wannan shi ne 'kore', kuma duk malamai sun yi ittifaqin haramcinsa. Dangane da yiwuwar cinikin kuwa, waxansu suka ce ya yiwu, waxansu kuma suka ce bai yiwu ba. Sai dai mafi ingancin magana, cinikin ya yiwu, don shi wanda ya zo wannan tayi, ai ba da shi muka yi ciniki ba. wannan shi ne abin da Imamu Malik bin Anas ya ce. Amma idan daga baya ka gane cewa wancan xan kore ne, to kana da dama ka fito, ka mayar ka ce ba ka so a ba ka kuxinka, kuma dole ne a ba ka. In kuma ka ce shi kenan kai ka haqura, kana son abin haka, ba komai, ya halatta.
Abu na uku: Annabi (ﷺ) ya ce, kar ku zamanto masu qiyayya da juna. Ka je kana fushi da wani, shi ma yana fushi da kai, wannan ma ba a so. Abin fushi idan ya faru, to a yi qoqari a rarrashi zuciya ta haqura. Da Manzon Allah (ﷺ) ya ce, ...kada ku juya wa juna bayanku "yana nufin kar ku qaurace wa junanku, ku yanke mu'amala da Juna. In dai an fara mu'amala kar a yanke ta, a ci gaba, sai in an riga an cuce ka ne, to idan aka zo za a sake zaunawa, sai ka ce "A'a! Ai rannan ka cuce ni, ba zan yarda ba." sallah dai mu yi tare, da azumi komai ma mu yi tare. Sai kuma Manzon Allah (ﷺ) ya ce, "....kada sashenku ya yi ciniki a cikin cinikin xan uwansa...." Abin nufi, idan mu biyu muna da haja ta kasuwanci da muke sayarwa, idan kwastoma ya shigo rumfata muna tsaye muna cinikayya, na sa masa suna yana tayi, to bai halatta ba ka zo ka juye kwastoman nan ka ce, "Zo mana in sayar maka qasa da yadda ya ba ka." Vangare na biyu, idan ni saye nake a wani wuri, na zo ina sayen kaya, an sa min suna ina yin tayi, bai halatta ba wani shi ma ya shigo, ya ce shi ma zai sayi wannan kayan, sai har ni na bari, ba a daidaita da ni ba.

Daga qarshe sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce, "....Ku kasance bayin Allah 'yan uwan juna, musulmi xan uwan musulmi ne, kada ya zalunce shi, kada ya yi masa qaya, kada ya kunyatar da shi." ko ka qi taimakonsa. In ya nemi taimakonka, ka taimaka masa, "....kada ya wulaqatar da shi...." wai don talaka ne. Ka ba shi matsayinsa da ya dace da shi. Aisha (R.A) tana cewa, "An umarce mu, mu sauke kowane mutum a matsayinsa." Manzon Allah (ﷺ) ya qarasa da cewa, "....Ya ishi mutum sharri, ya rinqa tozartar da xan uwansa musulmi...." Sharri ne babba tozartar da xan uwanka musulmi, don talaucinsa ko don qaramin ma'aikaci ne, ko don xan makaranta ne, ka xauka ba komai ba ne.

2 comments:

KITABUT-TAUHID (Babi Na Goma Sha Biyar15)

  SHARHI Babukan da suka wuce sun yi magana a kan yana daga dangin shirka neman taimako wajen wanin Allah. Wannan babi kuma zai nuna maka ...