GABATARWA.



WWW.TAFARKINSUNNAH.BLOGSPOT.COM

WANNAN SHAFI YANA DAUKE DA HADISAN ANNABI(SAW)ACIKIN HARSHEN HAUSA. IDAN ANGA MUNYI KUSKURE ASANAR DA MU.ALLAH YAYI MUNA JAGORA AMEEN!



DAMIN AIKO DA GYARA KO KARIN BAYANI;
{tafarkinsunnah@gmail.com]

Nov 15, 2011

ARBA'UNA HAADITH (36) HADISI NA TALATIN DA SHIDA


An karɓo daga Abu Hurairata (R.A) daga Annabi () ya ce, "Wanda duk ya kautar wa da mumini wani baƙin ciki, daga baƙin cikin duniya, to Allah zai kautar masa da wani baƙin ciki daga cikin irin baƙin cikin ƙiyama, duk wanda ya kawo sauƙi ga wanda yake cikin tsanani, Allah zai kawo masa sauƙi a duniya da lahira, wanda ya suturce musulmi, to Allah zai yi masa sutura a duniya da lahira. Lallai Allah yana cikin taimakon bawa matuƙar bawan ya kasance mai taimakon ɗan uwansa musulmi. Wanda duk ya kama wani tafarki yana neman ilimi a wannan tafarkin, Allah zai sauƙaƙa masa hanyar shiga aljanna. Babu wasu mutane da za su taru a cikin wani ɗaki cikin ɗakunan Allah, suna karanta littafin Allah, suna darasinsa a tsakaninsu da juna, face sai nutsuwa ta sauka a kansu, rahama ta lullube su, (Mala'iku sun kewaye su), sai kuma Allah ya ambacesu a fadarsa. Wanda duk aikinsa ya yi sanɗa da shi, to dangantakarsa ba za ta yi gaggawa da shi ba." Muslim ne ya rawaito shi (#2699) da Wannan lafazi.


SHARHI                        
Manzon Allah () ya ce, "Wanda duk ya kautar wa mumini Wani baƙin ciki...." daga dangin wani baƙin ciki da ke iya samun mutum a nan duniya, "....to Allah zai kautar masa da wani baƙin ciki...." daga cikin irin baƙin cikin da kan iya riskar bawa a gobe ƙiyama. Misali wani mutum mumini yana fama da matsala ta rayuwa, sai ka taimaka masa, ka yaye masa wannan baƙin cikin: An rubuto masa magani a asibiti, ba shi da kuɗin da zai saya, sai ka je ka sayo ka ba shi: An ba shi notis a gidan haya, sai ka zo ka ba shi kuɗin da ake bin sa, Ko aka sallame shi daga gidan haya, sai ka zo ka ba shi kuɗin da ake bin sa, ka ƙara masa kuɗin hayar na wata huɗu a kai, masu zuwa. Duk wanda ya yi wannan, Allah zai yaye masa wani baƙin ciki daga cikin dangin baƙin ciki da ke iya samun mutum a ranar tashin ƙiyama. Sai a can lahira, ba a nan zai yaye masa ba, a can zai yaye masa, a inda ba mai yayewa, sai shi (Allah). Sannan Manzon Allah () ya sake cewa, "....duk wanda ya kawo sauƙi...." ga duk mutumin da yake cikin tsanani, "....Allah zai kawo masa sauƙi a duniya da lahira...." Misali, mutum ne yake cikin wani tsanani, sai ka ba shi sauƙi: Kamar mutum ne ana bin sa bashi, sai ka taimaka masa ya biya. Ka ga cikin tsanani kenan yake, kai kuma sai ka taimaka masa. Ko kuma lokacin biya ya yi, babu abin biya, sai ka ƙara masa lokaci, ka ce bari sai wata na gaba in ya yi, ka biya, ko wata biyu masu zuwa, ko wata uku masu zuwa. Domin ba a cewa bari sai lokacin da ka samu ka kawo, ba a yin wannan, dole sai an ƙayyade lokaci. Sai dai in ya kasa, sai a ƙara masa wani lokacin, ba a yin bashi da cewa in ka samu ka kawo, Allah yana cewa,
(Idan (mutum) yana cikin tsanani, to a yi masa jinkiri zuwa lokacin da ya samu, wanda kuwa ya yafe, to wannan shi ya fi alheri). [Al Baƙara: 280]. Faɗin Manzon Allah () cewa, "....wanda duk ya kama wani tafarki yana neman ilimi a wannan tafarkin, Allah zai sauƙaƙa masa hanyar shiga aljanna...." wannan yana nuna falalar neman ilimi kenan. Duk wanda ya kama hanyar neman ilimi, to sai Allah ya sauƙaƙa masa shiga aljanna, ta cikin ruwan sanyi, ba wahala. Duk wanda ya tsaya a jahilci kuwa, to sai an rufe masa ƙofar gidan aljanna. A nan ba ya nufin sai ka zamanto tun da safe zuwa dare kana neman ilimi, alal-aƙalli ka taso daga ƙarfe biyar, ka je ka koyi Alƙur'ani, ka je ka koyi hadisan Annabi (), ko ka ɗauki Ahalari, ka je ka koya, ba ƙaramin alheri ba ne. Kada ka ce kai ka yi girma da koyon karatu, wannan ita ce hanyarka ta shiga aljanna.

A ƙarshen hadisin, Manzon Allah () ya ce, "....Wanda duk aikinsa ya yi sanɗa da shi, to dangantakarsa ba za ta yi gaggawa da shi ba." a ranar tashin Alƙiyama. Abin nufi, a nan gidan duniya za a ce, wane ɗan wane ne za a yi masa alfanna, a lahira babu alfarma, sai dai wa ya zo da imani da aiki nagari! Ba mai tsira, sai wanda yake ya je wa Allah da imani da aiki nagari. wannan shi ake buƙata! Don haka duk dangantakar mutum, ba za ta ƙara masa komai ba. Shi ya sa Annabi () yake cewa, "Ku 'ya'yan Banu Abdulmuɗɗalib! Ku tsamar da kanku daga wuta, domin ba zan amfana muku komai ba. Ku 'ya’yan Banu Hashim! Ku tsamar da kanku daga wuta. Ya Faɗimatu bintu Muhammad! Tambaye ni abin da kike so a cikin dukiyata, ba zan iya wadatar miki da komai ba ranar alƙiyama. [Duba: Sahih Al Bukhari (#2753) Sahih Muslim (#204)]. Don haka dangantaka ba ta amfani a gidan lahira, sai in ka yi aiki na-gari. In ka ga dangantaka ta yi amfani, to an shiga aljanna. Idan ɗa da iyayensa sun shiga aljanna, wani yana benen sama, kamar uba yana sama, yaro na benen ƙasa, sai a ce bari a daɗaɗa wa ubannin, sai a tura ɗan ya je wajen ubansa, duk da ɗan bai yi aikin da zai je gurin da uban yake ba. Allah ya ce,

(Waɗanda suka yi imani, kuma zuciyarsu ta bi su a kan (imanin) mun riskar da su tare da su). [Aɗɗur: 21] Amma in uba yana cikin aljanna, ɗa ya yi aikin da za a kai shi wuta, to ba a fito da shi daga wuta don mahaifinsa, matuƙar ya
mutu yana kafurci, zai dawwama a wuta, mahaifinsa ba zai iya tsamo shi ba.

No comments:

Post a Comment

KITABUT-TAUHID (Babi Na Goma Sha Biyar15)

  SHARHI Babukan da suka wuce sun yi magana a kan yana daga dangin shirka neman taimako wajen wanin Allah. Wannan babi kuma zai nuna maka ...