GABATARWA.



WWW.TAFARKINSUNNAH.BLOGSPOT.COM

WANNAN SHAFI YANA DAUKE DA HADISAN ANNABI(SAW)ACIKIN HARSHEN HAUSA. IDAN ANGA MUNYI KUSKURE ASANAR DA MU.ALLAH YAYI MUNA JAGORA AMEEN!



DAMIN AIKO DA GYARA KO KARIN BAYANI;
{tafarkinsunnah@gmail.com]

Nov 15, 2011

ARBA'UNA HAADITH (40) HADISI NA ARBA'IN


An karɓo daga Abdullahi ɗan Umar (R.A) ya ce, Manzon Allah (ﷺ),  ya dafa kafaɗata ya ce, “Ka kasance a duniya tamkar kai baƙo ne, ko kuma wanda yake kan hanya.” Ɗan Umar (R.A) yana cewa, “Idan ka kai yamma, kar ka yi jiran safiya, idan kuma ka wayi gari, to kar ka jira yamma. Ka riƙi aiki alheri lokacin lafiyarka, saboda lokain rashin lafiyarka. Ka riƙi aiki alheri lokacin rayuwarka, saboda ka
amfana lokacin mutuwarka.” Bukhari ne ya rawaitoshi. (#6416).

SHRHI;

Manzon Allah (ﷺ),  ya ce, “Ka kasance a gidan duniya tamkar baƙo ne…”
wanda yazo balaguro, yana sa ran komawa, kar ka baje kayanka na koli, ko kuma ka kasance tamkar, “….wanda yake kan hanya….” ba ka riga ka sauka ba. Ibnu Umar (RA) yana cewa, “Idan ka kai yamma, kar kayi jiran safiya….” Ma’ana in ka kai yini da ranka, aka zo aka maka tallar aikin alheri, kana ikon yi, kar ka jinkirta shi, ka ce bari in bari sai gobe, ba ka da tabbacin kaiwa goben. “Haka nan, “….Idan kuma ka wayi gari, to kar ka jira yamma….” Abin nufi, sai ga wani aikin alheri ya bijiro, kada shaiɗan ya zo ya ce, “A’a! Bari sai da yamma na yi.” ka aiwatar dashi a wannan lokacin, don ba kai kake da yammar ba. Don lokacin ɗan Adam guda uku ne: wanda ya wuce, wanda kake ciki yanzu, da wanda zai zo nan gaba. Wanda ya wuce, ya wuce, ba zai taɓa dawowa ba; wanda kake ciki yanzu, shine naka; wanda zaizo nan gaba, gaibu ne, ba ka san me zai zo da shi ba, zai zo kana lafiya ko baka da lafiya, zai zo kana da rai, kana da hali, ko baka da hali, ba san me zaka samu kanka ciki ba.Wannan lokacin da kake ciki, shi ne tabbas.
Cewar, “…Ka riƙi aikin alheri lokacin lafiyarka…” yana nufin don ka amfana da shi, in rashin lafiya ya kama ka. Saboda idan mutum ya saba yana yin aikin alheri lokacin lafiyarsa, idan rashin lafiya ta zo, ba zai yi asarar niyyar nan tasa ba, za a riƙa bashi lada, tunda dai bai sami damar yi ba. Wannan duk ana nuna wa mutum lokacin ribatar al’amari, ƙoƙarin ribatar lokaci. Malamai suna cewa idan Annabi(ﷺ),  ya fuskantar da magana zuwa ga wani daga cikin al’ummarsa, wannan mutum bashi kaɗai abin ya shafa ba, ya shafi kowanne musulmi, mace ko namiji, har zuwa alkiyama ta tashi. Don haka kar ka ce ai wannan ya nuna cewa ana iya yi wa mutum daya magana, amma ana nufin kowa da Abdullahi ɗan Umar (RA) kaɗai ake, mu nan gurin ba da mu ake ba. Wannan ya nuna cewa ana iya yi wa mutum Magana, amma ana nufin kowa da kowa. Sannan hadisin yana nuna mutum ya yi tanadi, saboda zuwam mutuwa, don gidan duniya ba gida ne na wanzuwa ba, in ma ka yi nufin ka wanzu ko ka daɗe a ciki, ba yadda za a yi ka dawwama.

(FASSARA DA SHARHI DA GA BAKIN GARIGAYI SHEIK JA’AFAR MAHAMUD ADAM {R} ).

No comments:

Post a Comment

KITABUT-TAUHID (Babi Na Goma Sha Biyar15)

  SHARHI Babukan da suka wuce sun yi magana a kan yana daga dangin shirka neman taimako wajen wanin Allah. Wannan babi kuma zai nuna maka ...