GABATARWA.



WWW.TAFARKINSUNNAH.BLOGSPOT.COM

WANNAN SHAFI YANA DAUKE DA HADISAN ANNABI(SAW)ACIKIN HARSHEN HAUSA. IDAN ANGA MUNYI KUSKURE ASANAR DA MU.ALLAH YAYI MUNA JAGORA AMEEN!



DAMIN AIKO DA GYARA KO KARIN BAYANI;
{tafarkinsunnah@gmail.com]

Nov 15, 2011

ARBA'UNA HAADITH (37) HADISI NA TALATIN DA BAKWAI


An karɓo daga ɗan Abbas (R.A) daga Manzon Allah () cikin irin abin da ya rawaito daga Ubangijinsa, ya ce, "Allah ya riga ya rubuta ayyukan alheri da munanan
ayyuka, wanda duk ya hinmatu zai aikata wani kyakkyawan aiki, sai bai samu aikatawa ba, Allah zai rubuta masa kyakkyawan aiki guda ɗaya cikakke. Idan ya himmatu zai aikata wani kyakkyawan aiki, kuma ya aikata shi, to Ubangiji zai rubuta masa lada goma, izuwa ninki ɗari bakwai, zuwa ninkininki da yawa. In ya himmatu zai aikata mummunan aiki, kuma bai aikata ba, Allah zai rubuta masa kyakkyawan aiki cikakke a wurinsa. Idan ya himmatu da mummunan aiki, kuma ya aikata shi, Allah zai rubuta masa mummunan aiki guda ɗaya” Bukhari (#6491) da Muslim (#131) a cikin sahihan littattafansu.


SHARHI
A cikin wannan hadisi za mu fahimci yalwar rahamar Allah Ta'ala, ta yadda rahamarsa ta fi azabarsa yalwa, yardarsa ta fi fushinsa. Kuma wannan hadisi, hadisi ne ƙudusi, cikin irin abin da Annabi () yake rawaitowa daga Allah kai-tsaye. Allah Maɗaukakin Sarki ya ce, "Allah ya riga ya rubuta (dangogin) ayyukan alheri ..... " da kuma dangogin ayyuka na ɓarna wanda mutune za su yi. Allah ya rubuta da Alƙalaminsa na ƙudura cewa, ranar kaza, wane zai yi kaza, rana kaza, wane zai aiwatar da kyakkyawan aiki. Don haka "....wanda duk ya himmatu ya aikata wani kyakkyawan aiki, sai bai samu aikatawa ba...." a zuciyarsa ga niyya, niyyar ya riga ya yanke lallai sai ya yi kaza, sai wani abu ya zo ya hana shi aikatawa, to duk da bai aikata ba, "....Allah zai rubuta masa kyakkyawan aiki guda ɗaya cikakke...." duk da bai samu damar yi ba, saboda wannan niyyar tasa."....Idan ya himmatu zai aikata wani kyakkyawan aiki...." kuma ya sami dama ya aikata aikin,"....to Ubangiji zai rubuta masa lada...." ɗaiɗai guda goma. Za kuma a iya ninkawa har zuwa ninki ɗari bakwai, har zuwa ninki mai yawa sama da ɗari bakwai. Sannan "....Idan ya himmatu zai aikata mummunan aiki....” kuma bai sami damar aikatawa ba, "....Allah zai rubuta masa kyakkyawan aiki cikakke a wurinsa...." Ma'ana mummunan aiki ne ka zo za ka yi, sai ka tuna wani nassi na hadisin Annabi () wanda ya haramta wannan abin, ko wani ya faɗakar da kai, sai ka fasa, wannan fasawar da ka yi, za ta sa a rubuta maka kyakkyawa, saboda ba ka yi wancan mummunan ba. Amma "....Idan ya himmatu da mummunan aiki, kuma ya aikata shi, Allah zai rubuta masa mummunan aiki guda ɗaya." Ma'ana, ba za a ninka masa yadda aka ninka lada ba. Wannan yana nuna yalwar rahamar Ubangiji, saboda Allah ba zai amfanu da komai ba wajen azabtar da mu.

Wannan hadisi ya kasa mutane kashi huɗu: Na ɗaya, wanda ya yi niyyar alheri, amma bai samu damar aikatawa ba, za a rubuta masa lada ɗaya cikakke. Na biyu, wanda ya yi niyyar yin alheri, ya kuma aikata, za a ninninka masa lada sau goma, har zuwa sau ɗari bakwai ko ma sama da haka. Na uku, wanda ya yi niyyar yin mummunan aiki, amma bai aikata ba, za a rubuta masa lada ɗaya. Na huɗu, wanda ya yi niyyar yin mummunan aiki, kuma ya je ya aikata, za a rubuta masa mummuna guda ɗaya. Babu matsala cikin kashi na ɗaya da na biyu da na huɗu, amma wanda ya yi niyyar zai aikata mummuna, kuma bai aikata ba, sai aka ce za a ba shi lada, to wannan in muka ɗauki wannan a haka, za mu ga wani nassin kuma wanda yake karantar da wani abu daban dangane da mutanen da suka yi nufin za su aikata ɓarna a garin Makka. Annabi () ya haramta yaƙi a Makka, haka Allah ma ya haramta wannan a hurumin Makka. Ko ciyawa da ke garin, ba a yarda mutum ya ƙetare mata iyaka ba, haka ko tsuntsu ya shiga garin, ba a yarda ka farauce shi ba, ko dabba ta shiga wurin, ba a yarda ka farauce ta ba, to ballantana ka ce za ka aikata Wani mummunan aiki na zina ko na caca ko wani abu a wajen, Allah ya ce,

(Wanda duk ya yi nufin ɓarna a cikinsa ( wato garin Makka) za mu ɗanɗana masa azaba mai tsanani) [Al-Hajj: 25] Nufata kawai mutum ya yi, niyya a zuci zai aikata mummunan aiki a garin, Allah ya ce, "....za mu ɗanɗana masa azaba mai tsanani." ’ko da bai aikata ba. To amma wannan, ya keɓanta da Makka, hukunci ne ga wanda yake cikin Makka kaɗai, amma in a wani garin ne ka yi nufin aikata wani mummunan aiki, ba ka kuma aikata ba, to za a ba ka lada, amma a can Makka ka yi niyya, ko ba ka aikata ba, akwai zunubi, saboda alfarmar wajen.

Ibnu Kasir ya ce, wanda ya zo zai yi mummunan aiki kashi uku ne: Imma dai ya zamanto ka zo za ka aikata mumunan aikin, amma ba ka aikata ba, saboda wa'azi, ko ka tuna wata aya, ko wani hadisi, sai ba ka aikata ba. To wannan shi ne za a ba ka kyakkyawa guda ɗaya. Ko kuma ya zamanto ka himmatu, ka tafi wani wuri za ka yi ɓarna, da ka tafi a hanya, sai wani abu ya bijiro maka, ko wani ya tsare ka da hira, sai ka manta abin da ya fito da kai daga gida, sai ka dawo gida, wannan ba ka da lada, ba ka da zunubi. Ko kuma ka himmatu lallai sai ka aikata mummunan aiki, amma sai aka fi ƙarfinka, ka tarar da wani ɗan ta'adda ya fi ka ta‘addanci, abin da za ka yi na wannan saɓon ya hana ka, to wannan duk da ba ka sami damar yi ba, amma da niyya: nan, sai an ba ka zunubi, saboda ba tsoron Allah ne ya sa ka janye ba, abubuwa ne suka fi ƙarfinka. Guda uku aka kasa su, kuma haka suke.

Dangane da wannan nufi na zuci, Ibnul ƙayyim ya ce matakai ne guda huɗu, kamar yadda ya kawo a littafinsa Ɗariƙul Hijrataini. Imma abu ya zo ta fuskar umani, Shaiɗan ya jefo maka tunanin yaya zan yi kaza, ya kawo maka tunanin aikin, ba tare da ka yi niyyar aikatawa ba, in ba ka yi abin ba, ba za a ba ka lada ko zunubi ba a kan wannan. So ake ka yi ƙoƙari ka ture wannan aikin kafin a je mataki na biyu. Wannan matakin na farko shi ake cewa alkhawaɗir; abu ne kawai ya ɗarsu a zuciya, ba tare da ka ɗauki wani mataki a kai ba. Mataki na biyu, shi ne ka sami Irada, ka ji kana sha'awar abin, to wannan sai ka yi ƙoƙari ka ture wannan abin, kar ya kai mataki na uku, shi-ne sai a sami alƙasdu, wato ka nufaci abin za ka yi. Mataki na huɗu shi ne, attasmim, wato ya zamanto zuciyarka ta makance dole sai ka yi, To a matakin farko in ka fasa, ba lada, ba zunubi a kansa; a mataki na biyu, ka sanya irada za ka yi, sai ka tuna Allah ka fasa, to wannan akwai lada, idan ya kai wancan mataki na makancewar zuciya, dole sai ka yi, sai ba ka sami yi ba, to wannan shine sai an sa wa mutum zunubi. Waɗansu malamai suka ce, matakan guda hudu ne; akwai khaɗir; sai hadisun nafsi sai hammu, sai azmu, suka ce duk waɗannan guda huɗun, na farko ba a kama mutum da laifi a kansu, a azmu ne ake kama mutum da laifi.

No comments:

Post a Comment

KITABUT-TAUHID (Babi Na Goma Sha Biyar15)

  SHARHI Babukan da suka wuce sun yi magana a kan yana daga dangin shirka neman taimako wajen wanin Allah. Wannan babi kuma zai nuna maka ...