GABATARWA.



WWW.TAFARKINSUNNAH.BLOGSPOT.COM

WANNAN SHAFI YANA DAUKE DA HADISAN ANNABI(SAW)ACIKIN HARSHEN HAUSA. IDAN ANGA MUNYI KUSKURE ASANAR DA MU.ALLAH YAYI MUNA JAGORA AMEEN!



DAMIN AIKO DA GYARA KO KARIN BAYANI;
{tafarkinsunnah@gmail.com]

Nov 15, 2011

ARBA'UNA HAADITH (32) HADISI NA TALATIN DA BIYU


An karɓo daga Abu Sa'id, Sa'ad ɗan Malik ɗan Sinan Al-Khudriy (R.A) ya ce, Manzon Allah () ya ce, "Ba cuta, babu cutarwa." Ibnu Majah ne ya rawaito shi (#2341) da Daraƙuzuni (#228) da waninsu Musnadan. Haka Imamu Malik ya rawaito shi a cikin Muwaɗɗa (J2/sh 746) daga Amru ɗan Yahya daga babansa daga Annabi () Mursalan, bai ambaci Abu Sa'id ba. Amma hadisin yana da hanyoyin da sashinsu yana ƙarfafa sashi.


SHARHI               
Waɗansu malamai suka ce, abin da ake nufi da gaɓar, "Ba cuta...." shi ne kada ka cuci wani, don ka amfana da wannan cutar tasa, "....babu cutarwa." kuma tana nufin kada ka cuce shi, ko da ba za ka amfana da wannan abin ba. Misali mutum yana da kuɗi, sai ka je ka sace masa, ka zo ka yi amfani da su. Wannan shi ne darar, ka cutar da wani don ka amfana. Dirar kuma, mutum ne yana da dukiya ko kadara, sai ka je ka ƙona ta, ka raba shi da ita, ba don ka amfana da ita ba. Wannan shi ne dirar. Wannan hadisi ne da yake an kafa ƙa'idojin fiƙihu da shi da dama. A ƙarƙashin wannan hadisi, dukkan dangin cutarwa, shari'a ta haramta shi, duk abin da za ka yi ya zamanto ka musguna wa ɗan Adam ɗan uwanka musulmi, to shari'a ba ta yarda ba.


No comments:

Post a Comment

KITABUT-TAUHID (Babi Na Goma Sha Biyar15)

  SHARHI Babukan da suka wuce sun yi magana a kan yana daga dangin shirka neman taimako wajen wanin Allah. Wannan babi kuma zai nuna maka ...