GABATARWA.



WWW.TAFARKINSUNNAH.BLOGSPOT.COM

WANNAN SHAFI YANA DAUKE DA HADISAN ANNABI(SAW)ACIKIN HARSHEN HAUSA. IDAN ANGA MUNYI KUSKURE ASANAR DA MU.ALLAH YAYI MUNA JAGORA AMEEN!



DAMIN AIKO DA GYARA KO KARIN BAYANI;
{tafarkinsunnah@gmail.com]

Mar 14, 2010

ARBA'UNA HADITH {1} HADISI NA FARKO

SAURARI MUQADDIMA DA SHARHIN HADISI NA (1) DAGA BAKIN MARIGAYI SHEIK JAFAR MAHMUD ADAM



An karɓo daga Sarkin Muminai, baban Hafs, Umar bin Khaɗɗabi ya ce, na ji Manzon Allah (ﷺ) yana ccwa,
"Lallai kaɗai, ayyuka suna tare da niyyoyinsu, kuma lallai kowane mutum yana samun sakamakon abin da ya yi niyya
(azuciyarsa). Wanda duk hijirasa ta kasance saboda Allah da Manzonsa, to hijirarsa tana ga Allah da Manzonsa, wanda kuma hijirarsa ta kasance saboda duniya da zai samu, ko don wata mace da zai aure ta, wannan sakamakon hijirarsa na nan kan abin da ya yi hijira zuwa gare shi." Shugabannin masu hadisai ne suka rawaito shi. Su ne, Muhammad ɗan Isma'ila ɗan Ibrahim dan Mugirata (fan Bardizbah Al-Bukhari' Al-Ju'ufiy. (#1, 54). da Abul Husaini Muslimu ɗan Hajjaju ɗan Muslimu Alƙushairiy Annaisaburiy (#1907) a cikin ingantattun littattafansu, waɗanda su ne mafi ingancin littattafai da aka rubuta.
SHARHI

 Wannan hadisi yana ɗaya daga cikin hadisai mafiya shahara daga cikin hadisan Annabi(ﷺ): Mutum daya ne ya ji wannan hadisi daga bakin Annabi (ﷺ), shi ne Umar ɗan Khaddab; mutum ɗaya ne ya ji shi daga Umar ɗan Khaddab, shi ne Alƙama bin Waƙƙas Allaisiyyi; haka ma mutum ɗaya ne ya ji shi daga wajen Alkama, shi ne Muhammad bin Ibrahim Attaimiyyi; mutum d'aya ne tak, ya ji shi daga wajen Muhammad bin Ibrahim Attaimiyyi, shi ne Yahaya bin Sa'id Al-Ansariyyi. Daga kan wannan bawan Allah, Yahya bin Sa'id Al-Ansariyyi ne wannan hadisi ya shahara. Domin shi ɗaya, sama da mutum ɗari biyu ne suka rawaito hadisin a wajensa. Wannan ita ce hanyar da ta inganta cikin hanyoyin wannan hadisi. Wasu malamai sukan rawaito shi daga Sa'ad bin Abi waƙƙas, amma bai inganta ba, wannan ita ce (kaɗai) hanya ingantacciyya da ta tabbata. Daga cikin mutanen da suka ji wannan hadisi a wurinsa, akwai Imamu malik bin Anas, da Ishak bin Rahawaihi, da Ahmad bin Hambal, da Shu'uba, da Sufyan bin Sa'id Assauriy, da Sufyan bin Uyayna.
Imamul Bukhari ya mayar da wannan hadisi ya zamanto shi ne gabatarwar littafinsa Sahihul Bukhari. Bayan bismillah, sai ya kawo wannan hadisin don ya mayar da shi gabatarwa ta littafinsa, domin ya nuna wa mutane cewa, kowane irin aiki da za ka yi, ba shi zamantowa abin ƙirgawa a wajen Allah, sai in ya zamanto ka yi shi da kyakkyawar niyya, kuma domin ya nuna mafi tsadar ikhlasi a cikin ayyuka. Malamai da dama sun yi magana kan matsayin wannan hadisi, har Abdurrahman bin Mahdi yake cewa, "Da zan sami damar wallafa littafi mai babi-babi na hukuncehukunce, to da sai na mayar da wannan hadisi ya zamanto shi ne gabatarwar kowane babi." Imamush. Shafi'i yana cewa, "Shi wannan hadisi shi ne sulusin ilimi gaba daya." Abin da ake nufi da sulusin ilimi, kashi ɗaya bisa ukun ilimi, sannan ya ci gaba da cewa, "Zai iya shiga babi ɗaiɗai har guda saba'in daga cikin babin
fikihu. [Duba: Jami'ul Ulum Wal Hikam Na Ibnu Rajab 1/23. Fathul Bari 1/10 - 11].
Lafazin Hafs da ya zo a wannan hadisi, a larabce, ɗaya ne daga cikin sunayen zaki, sukan ce masa_HaIfs, sukan ce Asad, sukan ce masa Aglab, sukan ce Hizabr. Zaki yana da sunaye daidai har guda ɗari idan ka duba ƙamus. Ana ce wa Umar ɗan Khaɗɗab Abu Hafs, saboda jaruntakarsa, kuma yana alfahari da wannan alkunya ta Abu Hafs, domin Annabi (ﷺ) ne ya yi masa alkunya da cewa Abu Hafsin.
Dangane kuwa da lakabin Amirul Mu’uminina, Umar ɗan khaɗɗab shi ne mutum na farko daga cikin sahabbai wanda suka yi shugabanci a bayan Annabi (ﷺ) da ake yi wa lakabi da Amirul Mu ’uminina (R.A). Dangane da faɗinsa (ﷺ) cewa, "Lallai kaɗai, ayyuka suna tare da niyyoyinsu....", a nan wurin duk aiki ne, ake yi wa niyya ko kuma akwai waɗanda ba a yi musu niyya? Waɗansu malamai sun ce akwai waɗanda ake yi musu niyya, akwai waɗanda ba a yi musu niyya. Abin da ake nufi da 'ayyuka' a nan kuwa, shi ne ayyukan da suka shafi shari'a kai-tsaye, kamar alwala da sallah da zakka da azumi da dukkan aikin da yake ibada ne tsantsa. To irin waɗannan ayyuka su ne suke bukatar niyya. Amma akwai ayyukan da suka shafi dabi'arka ta ɗan Adam ta yau-da-gobe, kamar zama da tashi da kwanciya da kishingiɗa da cin abinci da shan ruwa da yin wanka da sanya tufafi, da dai sauransu. Waɗannan duk sunansu ayyuka, amma ba sa buƙatar niyya. Don za ka zauna, ba wani buƙatar niyyar zama, don za ka tashi, ba buƙatar sai ka yi niyyar tashi. Ashe lafazin ‘ayyuka‘ a nan, ba ayyuka gaba ɗaya ake nufi ba, abin da ake nufi shi ne dukkan ayyukan da suke sharia ce ta ce a yi su. To irin waɗannan ayyuka,
su ne suke buƙatar niyya. [Duba Jami'ul Ulum Wal-Hikam Na Ibnu Rajab 1/ 26].
Hadisin ya yi maganar hijira, abin da ake nufi da hijira shi ne mutum ya yi ƙaura daga garin kafirci zuwa garin musulunci. Wannan shi ne asalin hijira, wannan hijirar wajibi ce, kuma abu ne mai falalar gaske, shi ya sa ko cikin Alkur‘ani Ubangiji Ta'ala
ya kasa sahabban Annabi (ﷺ) kashi biyu, akwai Al-Muhajirun, akwai Al-Ansar. Su Al-Muhajirun ɗin, kullum aka zo kawo labari su ake fara gabatarwa. To irin wannan hijirar, idan mutum yana son ya yi ta, ya samu lada, to dole sai ya kasance ya yi ta domin Allah, kuma ya yi ta domin koyi da Manzon Allah (ﷺ). Wannan shi ne ma'anar fadin Manzon Allah (ﷺ) cewa, "....Wanda duk hijirarsa ta kasance saboda Allah da Manzonsa...." Wani zai iya cewa, to ai ana yin abu ne domin Allah kaɗai, don me aka raɓa Manzon Allah (ﷺ) ba ciki? Ibnul Kayyim a cikin littafmsa Zadul Ma'ad ya fassara wannan hadisi ya ce, faɗin Manzon Allah (ﷺ) cewa, "Wanda duk hijirarsa ta kasance saboda Allah...." yana nufin da tauhidi, cewar, "....da Manzonsa....", yana nufin don ɗa'a ga Manzon Allah (ﷺ). Don haka hijira zuwa ga Allah ita ce, ƙaura zuwa gare shi ta hanyar tauhidi; hijira zuwa ga Manzon Allah (ﷺ) ita ce kaura zuwa gare shi ta fuskar ɗa'a da biyayya, tunda shi ne ya ba da umarnin a yi hijira ɗin, amma ba wai don shi zai ba da lada ba, Yadda ba a bauta wa kowa sai Allah, haka ma ba'a yi wa kowa biyayya ta gaba ɗaya, sai Manzon Allah (ﷺ).
Fadin Annabi (ﷺ) cewa, “....wanda hijirarsa ta kasance saboda duniya da zai samu, ko don wata mace da zai aure ta, wannan sakamakon hijirarsa na nan kan abin da ya yi hijira zuwa gare shi." yana nufin dukkan wanda ya yi hijira daga wani gari zuwa wani gari, ya zamanto abin da ke cikin zuciyarsa shi ne don ya ci ribar abu iri kaza na duniya, to wannan abin shi kaɗai ne abin da wahalarsa ta hijira za ta ƙare a kai, ko ya sami abin ko bai samu ba, ba shi da lada dai a wurin Allah. Haka nan wanda ya yi hijira domin auren wata, shi ma wannan abin shi kaɗai ne abin da hijirarsa za ta faru ta ƙare a kai, ko ya sami auren ta ko bai sami auren ta ba, ba shi da ladan komai a wajen Allah Ta'ala.
Wasu malamai sukan rawaito hadisi cewa, akwai hadisin wani sahabi da ake cewa Muhajiru Ummu Kaisi, wanda yana neman wata baiwar Allah cikin muminai da aure, sai ta yi hijira ta tafl Madina, shi ko da bai da niyyar zuwa Madina, da ta yi hijira shi ma sai ya nade kayansa ya yi hijira, ya taho Madina. To wai sanadiyyarsa ne sai Annabi (ﷺ) ya fadi wannan hadisi. Wannan  bayani bai inganta ba daga Annabi (ﷺ), wannan hadisi ne da'ifi. [Don Karin bayani duba: Fathul Bari 1/10]
A nan wurin da Annabi (ﷺ) ya fadi ayyuka, sai ya buga misali a kan ɗaya daga cikin ayyukan da ake yi musu niyya, sai ya kawo hijira, don kai kuma, ka yi ta kawo sauran ayyukan da za su iya shiga ƙarƙashin kalmar ayyuka. Buga misali ne Annabi (ﷺ) ya yi, abin ya faru, ko bai faru ba, ya buga misali ne da shi. Duk wanda ya yi hijira don Allah, to ga sakamakonsa, duk wanda ya yi hijira don wani abu, sai ya faɗi dangogin abubuwan da mutane ke buƙata a rayuwarsu.
Niyya tana da Ɓangarori guda biyu: Ɓangaren farko, shi ne ɓangaren da ya shafi flƙihu zalla. A nan wurin ana kawo niyya ne saboda rarrabe tsakanin ibada da ibada, kamar rarrabe tsakanin azahar da la‘asar. Idan muka yi la'akari game da waɗannan salloli biyu, za mu ga raka'o'i hudu ake yi, tsarin karatu ɗaya ake yi, siffar da ake yin su duk iri ɗaya ce, abin da yake bambance wannan azahar ce, wannan la'asar ce, shi ne niyya! Saboda haka ana zuwa da niyya saboda bambance tsakanin ibada da ibada; tsakanin farilla da nafila; tsakanin kaffara da bakance, duk niyya ce take bambance waɗannan. Sannan ana zuwa da ita don bambance tsakanin ibada da al'ada. Wani zai iya ƙin cin abinci saboda yana yajin cin abinci, kamar yadda 'yan kurkuku suke a wani gari, ya ce, yau wannan wunin gaba-ɗaya, ba zai ci abinci ba, awa goma sha biyu, an kawo masa abincin safe bai ci ba, an kawo masa abincin rana bai ci ba, har dare ya yi bai ci ba, yanzu ya yi awa goma sha biyu cur. Kai kuma ka tashi da niyyar yin azumi ka yi awa goma sha biyu cur, bambancin da ke tsakaninka da shi a nan, shi ne ta fuskar niyya!  Sai babinta na biyu, shi ne alaƙar niyya ɗin da wanda aka yi aiki dominsa, shi ne Allah. Idan ka yi niyyar sallar azahar a irin tsarin da ake niyya, ka sallaci raka'a huɗu, sallah ta inganta, yanzu sai ka yi niyya kashi ta biyu, kafin maganar lada ta zo, ita ce kyakkyawar niyya tsakaninka da Allah. Ya zamanto ka yi wannan sallar don neman kusancin Allah Ta'ala. To wannan niyya a wannan ɓangarenta na biyu, ba ta shiga babukan fiƙihu, tana Shiga babukan tauhidi ne. Malamai da dama sun yi wallafewallafe a kan niyya ta ɓangaren tauhidi, kuma dukkaninsu suna kafa hujja da faɗin Annabi (ﷺ) a cikin wannan hadisin, "Lallai kadai, ayyuka suna tare da niyyoyinsu...." Wannan ɓangaren fiƙihu kenan! Amma faɗinsa (ﷺ) "....Kuma lallai kowane mutum yana samun sakamakon abin da ya yi niyya (a zuciyarsa)...." wannan ɓangaren da ya shafi tauhidi kenan. [Duba: Jami'ul Ulum Wal Hikam Na Ibnu Rajah 1/28]
Faɗinsa Manzon Allah (ﷺ) cewa, "....Kuma lallai kowane mutum yana samun sakamakon abin da ya yi niyya (a zuciyarsa)...." yana nufin, abin da ka niyyata, shi ne abin da za ka samu. Idan ka yi niyya ta gari tsakaninka da Ubangiji, to Allah zai ba ka lada, idan kuma ba ka da niyya ta gari, to ba ka da lada a gurin Allah. Rashin bambance wannan, zai haifar maka da matsala da dama: Sai a ce mutum ya yi sallah ta isar masa, amma ba lada, sai ka yi mamaki, to saboda ya yi niyyar da ta shafi bambance aiki da aiki, amma niyyar da ta shafi wanda ake yin aikin dominsa, ba ta yi kyau ba.
Malamai suna cewa, idan mutum ya yi aiki, ya nufaci wani a cikin aikin (wato ya yi riya), wannan ba shi da lada a wajen Allah. To amma abin na iya zama kashi biyu: Ta iya yiwuwa, farkon lokacin da za ka yi aikin, ka yi shi domin Allah. Ka tashi niyyar domin Allah, kana cikin aiki kafin ka ƙarasa, sai riya ta shigo. Wannan riyar da ta shigo a tsakiyar sallarka, kafin ka ƙarasa, bayan a farko niyyarka ka yi domin Allah, domin samun kusancin Allah, ba ta isa ta rusa maka aikinka ba, aikinka na nan da cikakken ladanka a wajen Allah.
Don haka sai waɗansu malamai suka ce, ayyuka iri biyu ne, ko dai aikin da yake farkonsa da ƙarshensa suna haɗe da juna, kamar sallah, raka'ar ƙarshe tana hade da ta farko. Suka ce aiki irin wannan, wanda ƙarshensa yana haɗe da farkonsa, to in ka yi kyakkyawar niyya da farko, to ko riya ta shigo, ba ta isa ta rusa maka shi ba, saboda in farkon ya inganta, to ƙarshen ma zai tafi a haka. Amma aikin da ƙarshensa ba ya hade da farkonsa, kamar karatun Alkur'ani; misali kana cikin karatun Alkur'ani da kyakkyawar niyya, ka yi hizifi biyu da kyakkyawan karatunka don Allah sai wani ya zo karatun ya burge shi yana sauraro, sai ka ƙara koda muryarka don ka burge shi, to wannan hizifi biyun da ka yi, ka samu wannan, amma daga ayar da ka fara koɗa muryarka, aikin ya rushe, saboda ƙira‘ar farko, ba ta da alaka da ƙarshenta, inda ka yi kyakkyawar niyya kana da lada, inda ka yi mummunar niyya kuma, ba ka da lada.
Idan kuma ya zamanto aikin ba ka fare shi ba, kana zaune ba ka da niyyar yin sa, sai kawai ka tashi ka yi shi domin wani, to wannan an yi ittifaƙi ba ka da ladan komai a ciki, kuma malamai da dama sun ce musulmi ba shi da wannan dabi'a, duk wanda kuwa ya yi wannan, to ana jin tsoron wannan ya fitar da shi daga cikin musulunci, musamman idan wannan aiki ya zamanto wajibi ne yin sa, kamar sallah. Mutum ba ya sallah kwata kwata, sai ya ga wasu abokansa sun zo, ko ya ga wani mutum ,da yake jin nauyinsa ya zo, ko wanda yake jin kunyarsa ya zo, sai ya tashi ya yi sallah, kawai domin waɗannan kar su tuhumce shi da cewar ba ya sallah, amma a zuciyarsa ba ruwansa da ita, to wannan mutum ba musulmi ba ne, akwai jin tsoron ya shiga ƙarkashin faɗin  Allah Ta'ala,
(Duk waɗanda suke nufin duniya (da ayyukansu) da kayan adonta, to za mu cika musu ayyukansu a cikinta, ba za a tauye musu ba. Su ne waɗanda ba su da komai a lahira sai wuta, abin da duk suka aikata ya rushe, haka abin da suka aikata ya lalace) [Hudu:15 -16].
Ba ya hallata ga mutum ya ce zai yi lafazi da niyya. Niyya abu ne a zuci, har ma da dama a cikin malamai sun ba da fatawar cewa yin lafazi da niyya bidi'a ne. [Duba Jami'ul Ulum Wal Hikam Na Ibnu Rajah 1/63]. Don haka da zarar ka zo sallah ko azumi, abin da ake bukata, shi ne ƙudurcewa a cikin zuciyarka, irin sallar da za ka yi. Azahar ce ko la'asar ce, za ka yi ta ne kai kadai ko jam’i ne, wannan duk za ka haIarta wa zuciyarka ne, ba sai bakinka ya furta haka ba. Da niyyar azumi da niyyar aikin haji, da niyyar sallah da kowace niyya ba a furta ta da baka, ana kudurcewa ne a zuci. Da ka ƙudurce a zuci shi kenan, ka shiga sallah! Sai muƙaranatun niyyar. Wato ya zamanto da ibadar da niyyar sun haɗu da juna, lokacin da za ka shiga cikin ibadar. Misali, lokacin da ka zo za ka yi azahar, ka fuskanci gabas bakinka na ccwa Allahu Akbar! zuciyarka na ƙudurce irin sallar da za ka yi, azahar ce ko la'asar ce. Wannan shi ne muƙaranatun niyya! Haƙiƙaanin al'amarin shi ne, in ka gabatar da niyya a zuci, sannan ka yi kabbara, sallarka ta yi, in ka cuɗanya niyya da kabbara, sallarka ta yi. Abin da ba zai yiwu ba, shi ne ka yi kabbara, sannan kuma daga baya ka shigar da niyya, wannan ba zai yiwu ba.

KITABUT-TAUHID (Babi Na Goma Sha Biyar15)

  SHARHI Babukan da suka wuce sun yi magana a kan yana daga dangin shirka neman taimako wajen wanin Allah. Wannan babi kuma zai nuna maka ...