GABATARWA.



WWW.TAFARKINSUNNAH.BLOGSPOT.COM

WANNAN SHAFI YANA DAUKE DA HADISAN ANNABI(SAW)ACIKIN HARSHEN HAUSA. IDAN ANGA MUNYI KUSKURE ASANAR DA MU.ALLAH YAYI MUNA JAGORA AMEEN!



DAMIN AIKO DA GYARA KO KARIN BAYANI;
{tafarkinsunnah@gmail.com]

Nov 18, 2011

ARBA'UNA HAADITH (42) HADISI NA ARBA'IN DA BIYU

An karɓo daga Anas ɗan Malik (R.A) ya ce, “Na ji Manzon Allah (ﷺ),  yana cewa, Allah Maɗaukakin Sarki yana cewa, “Ya kai ɗan Adam! Lallai ba za ka bauta min ba, kuma ka sanya rai game da rahamata ba, face sai na gafarta maka ban damu ba. Ya kai ɗan Adam! Da a ce zunubanka zasu cika sashen sama gaba ɗaya, sannan ka nemi gafarata, sai in gafarta maka. Ya kai ɗan Adam!

Da a ce zaka zo min da cikin ƙasa gaba ɗaya zunubai ne, sannan ka gamu dani, ba tare da ka haɗa ni da kowa ba, Ni kuma zan kawo maka gafara, cikin ƙasa.” Tirmizi ne ya  rawaito shi (#3540) ya ce, hadisi ne mai kyau, ingantacce.


SHARHI;

Wannan hadisi yana nuna falalar tauhidi ta yadda idan mutum ya mutu ba ya shirka Allah yana gafarta masa zunubansa amma wanann ba ga kowa bane, sai wanda Allah ya ga damar ya gafartawa.
(FASSARA DA SHARHI DA GA BAKIN GARIGAYI SHEIK JA’AFAR MAHAMUD ADAM {R} ).

1 comment:

KITABUT-TAUHID (Babi Na Goma Sha Biyar15)

  SHARHI Babukan da suka wuce sun yi magana a kan yana daga dangin shirka neman taimako wajen wanin Allah. Wannan babi kuma zai nuna maka ...