GABATARWA.



WWW.TAFARKINSUNNAH.BLOGSPOT.COM

WANNAN SHAFI YANA DAUKE DA HADISAN ANNABI(SAW)ACIKIN HARSHEN HAUSA. IDAN ANGA MUNYI KUSKURE ASANAR DA MU.ALLAH YAYI MUNA JAGORA AMEEN!



DAMIN AIKO DA GYARA KO KARIN BAYANI;
{tafarkinsunnah@gmail.com]

Nov 15, 2011

ARBA'UNA HAADITH (39) HADISI NA TALATIN DA TARA


An karɓo daga ɗan Abbas (R.A) ya ce Manzon Allah (ﷺ),  ya ce, “Allah Ya yafe wa al’ummata, abin da ta yi dakuskure, da mantuwa, da abin da aka tilasta ta.” Hadisi ne mai kyau Ibnu Majah ne ya rawaito shi (#2045) da Baihaƙi a cikin Sunan.

SHARHI;

Waɗannan abubuwa guda uku an yafe wa Al’ummar Annabi (ﷺ), . Kuma wannan ɗaya ne daga cikin abin da yake nuna falalarmu a kan sauran al’ummai, saboda sauran al’ummai ba a basu wannan damar ba. Mu kaɗai ne muke da irin wannan damar, don ya ce a hadisin, “Allah Ya yafe wa al’ummata…” wanan ya nuna sauran al’ummar da suka gabata, ba su sami wannan falalar ba.

Abin da ake nufi da an ɗauke muna zunubin abin da mukayi da mantuwa ko kuskure ko abin da aka tilasta mu akai, shi ne an yafe mana wannan zunubin. Misali an sayan wa sallah lokacinta, sai wani ya bari har lokacinta ya fita, ba tare da ya yi ba, ba tare da uzurin komai ba, wannan yana da zunubi. Wani kuma lokacinta ya fita, ba tare da ya yi ba, saboda barci ya ɗauke shi, ko saboda ya manta har lokacinta ya fita, sannan daga baya ya tuna, wannan bashi da zunubi. To haka al’amarin yake! duk abin da mutum ya yi da mantuwa ko da kuskure, an ɗauke masa zunubinsa. Ba cewa aka yi ba za ka rama ba, maganar ramuwa daban, zunubi kawai aka yafe maka, amma idan abu ya kama na biya ne, sai ka biya. Misali bisa kuskure ka yi min hasarar wani abu na dukiya, ba ka da laif wajen Allah, Allah Ya yafe maka wannan laifin, saboda kuskure, ka yi, amma wannan bashi yake nuna ba zaka biya ni ba, in nace sai ka biya ni. Amma idan da gangan ne ka lalata min dukiyata, kana da zunubi a wajen Allah, sai kai istigfari, sannan kuma sai ka biya ni kayana. Haka nan ka riga kayi rantsuwar ba zaka shiga gidan wane ba, sai ya sa ƙarti suka kama ka suka shigar da kai, Ko kana aiki, ka riga kayi rantsuwa, wallahi yau ba zaka fito ba, sai ka kwana a gidanka, sai aka sa karti suka fito da kai da ƙarfin tsiya. Ka ga dai anan rantsuwarka ta riga ta karye, amma ba zaka yi kaffara ba, saboda tilasta ka akayi, ba son kanka ba ne. Amma da wani zai zo ya tsare ka ya ce maka dole sai ka kashe wane, ko in ka kashe ka, ko sai ka fille hannun wane, ko kai in fille maka hannunka, to idan ka fille masa hannun kana da laifi, tunda kai ne ka yi da kanka, yanzu tilastaka ɗin da akayi, ka yi ne don tseratar da rayuwarka, sai ka je ka zubar da rayuwar wani. Iman Malik ya ce, da wanda ya sa aka yi kisan da wanda ya yi kisan, su biyu duk za mu kama, mu kashe, kamar sun yi tarayya ne sun kashe rai ɗaya, ba za a ce ai tilasta shi a ka yi ba, ai ba shi da laifi!.

(FASSARA DA SHARHI DA GA BAKIN GARIGAYI SHEIK JA’AFAR MAHAMUD ADAM {R} ).

No comments:

Post a Comment

KITABUT-TAUHID (Babi Na Goma Sha Biyar15)

  SHARHI Babukan da suka wuce sun yi magana a kan yana daga dangin shirka neman taimako wajen wanin Allah. Wannan babi kuma zai nuna maka ...