GABATARWA.



WWW.TAFARKINSUNNAH.BLOGSPOT.COM

WANNAN SHAFI YANA DAUKE DA HADISAN ANNABI(SAW)ACIKIN HARSHEN HAUSA. IDAN ANGA MUNYI KUSKURE ASANAR DA MU.ALLAH YAYI MUNA JAGORA AMEEN!



DAMIN AIKO DA GYARA KO KARIN BAYANI;
{tafarkinsunnah@gmail.com]

Sep 14, 2011

ARBA'UNA HADITH (17) HADISI NA SHA BAKWAI

An karɓo daga Abu Ya'ala Shaddadu bin Ausi (R.A) daga Annabi () ya ce, "Allah Ta'ala ya wajabta kyautatawa ga kowane irin abu (da mutum zai yi a duniya) idan kuka yi nufin kisa, ku kyautata kisan, idan kun yi nufin yanka (dabba) ku kyautata yankan, kowane dayanku (da zai yi yanka) ya wasa wukarsa, ya hutar da abin yankansa." Muslim (#1955) ya rawaito.
                               
SHARHI
Ma'ana, Ubangiji ya wajabta kyautatawa: Ga kowanne irin abu da mutum zai yi a duniya, ya zamanto ya kyautata shi. Kowanne irin abu, ɗan Adam ne, dabba ne; yana buƙatar

ARBA'UNA HADITH (16) HADISI NA SHA SHIDA

An karɓo daga Abu Hurairata (R.A) ya ce, wani mutum ya zo, ya ce da Annabi () "Ka yi min wasiyya." sai ya ce da shi, "Kada ka yi fushi!“ sai ya yi ta maimaita buƙatarsa, sai (annabi ()) ya ce, "Kada ka yi fushi!" Bukhari (#6116) ya rawaito.

SHSRHI
Dangane da lafazin 'wasiyya‘ da ya zo a cikin jumlar, "Ka yi min wasiyya." abin da ake nufi da 'wasiyya', shi ne wata kalma taƙaitacciya da zan daɗe ina amfani da ita a cikin

ARBA'UNA HADITH (15) HADISI NA SHA BIYAR

An karɓo daga Abu Hurairata (R.A) ya ce, "Lallai Annabi () ya ce, "Wanda ya kasance ya yi imani da Allah da kuma ranar ƙarshe, ya fadi alheri ko ya yi shiru, wanda ya kasance ya yi imani da Allah da ranar ƙarshe, to ya girmama maƙocinsa, wanda ya kasance ya yi imani da Allah da ranar ƙarshe, to ya girmama baƙonsa." Bukhari (#6018) da Muslim (#48) suka rawaito.

SHARHI

Saƙo uku wannan hadisin yake ɗauke da su: Kama harshe; kar mutum ya yarda ya furta magana, sai cikin abin da yake akwai maslaha ta addini ko ta duniya. Maslahar addini,

ARBA'UNA HADITH (14) HADISI NA SHA HUDU

An karɓo daga Abdullahi ɗan Mas'ud (R.A) ya ce, Manzon Allah () ya ce, "Jinin mutum musulmi ba ya halatta, sai da ɗaya daga cikin (laifuka) guda uku: Magidanci mai zina, da ran da ta kashe rai, da wanda ya bar addininsa, ya rabu da jama'a.‘' Bukhari (#6878) da Muslim (#1676).

SJARHI

Manzon Allah () ya ce, "Jinin mutum musulmi ba ya halatta, sai da ɗaya daga cikin laifuka guda uku...." Na farko, magidanci, Wanda ya taɓa yin aure ingantaccen aure, kuma ya zo ya aikata zina bayan aurensa, to wannan ya zama

ARBA'UNA HADITH (13) HADISI NA SHA UKU

An karɓo daga Abu Hamza, Anas ɗan Malik (R.A), yaron gidan Annabi () ya ce, Manzon Allah () ya ce, "ɗayanku ba ya zama mai cikakken imani, har sai ya so wa ɗan uwansa abin da yake so wa kansa." Bukhari (#13) da Muslim (#45) suka rawaito
                   
SHARHI

Faɗin Annabi () cewa, "....ba ya zama mai cikakken imani....”, wannan yana kore cikar imani ne, ba wai yana kore asalin imani ba. Irin waɗannan hadisai suna da yawa.

ARBA'UNA HADITH (12) HADISI NA SHA BIYU

An karɓo daga Abu Hurairata (R.A) ya ce, Manzon Allah () ya ce, "Yana daga kyawun musuluncin mutum, barin abin da ba ya da muhimmanci a gare shi."(” Tirmizi (#2318) da Ibnu Majah (#3976).
                   
SHARHI
Faɗin Manzon Allah () cewa, "Yana daga kyawun musuluncin mutum, barin abin da ba ya da muhimmanci a gare shi." yana nufin, duk abin da ba shi da muhimmanci, to a rabu da shi. Wannan shi ke nuna kyautatuwar

ARBA'UNA HADITH (11) HADISI NA SHA DAYA

An karɓo daga Abu Muhammad, (shi ne) Hasan ɗan Aliyyu ɗan Abu dalib, jikan Annabi () abin ƙaunarsa, ya ce, "Na haddato daga bakin Annabi () ya ce, "Ka ƙyale duk abin da ke sa maka kokwanto, zuwa ga abin da ba ya sa maka kokwanto." Tirmizi (#2520) da Nasa'i (#5711) suka rawaito shi, Tirmizi ya ce, "Hadisi ne mai kyau ingantacce."

SHARHI

Annabi () ya ce, "Ka Kyale duk abin da ke sa maka kokwanto, zuwa ga abin da ba ya sa maka kokwanto." Ma'ana, duk wani abu da yake da kokwanto, ko zai raba

ARBA'UNA HADITH (10) HADISI NA GOMA

An karɓo daga Abu Hurairata (R.A) ya ce, Manzon Allah () ya ce, "Lallai Allah tsarkakakke ne, kuma ba ya karɓar abu, sai tsarkakakke. Allah ya umarci muminai da irin abin da ya umarci Manzanni da shi. Ya ce, "Ya ku Manzanni! Ku ci daga daɗaɗan abubuwa, kuma ku yi aiki na-gari" kuma (Allah) ya faɗa (lokacin da yake umartar muminai) "Ya ku waɗanda suka yi imani! Ku ci daga daɗaɗan abubuwan da muka azurta ku da shi." Sannan (Annabi ) ya ambaci wani mutum, da yake tsawaita tafiya, gashin kansa ya yi gizo, ya yi ƙura, yana miƙa hannayensa zuwa ga sama, yana ccwa, "Ya Rabbi! Ya Rabbi!” amma kuma abincinsa haramun ne, abin shansa haramun ne, tufafmsa haramun ne, an ciyar da shi haram. Ta yaya za a amsa masa (addu'arsa)? (Muslim #1015)
                      
SHARH

Abin da ake nufi da, “....Allah Ta‘ala tsarkakakke ne...." shi ne kamili ne shi cikin siffofinsa, babu tawaya ko nakasa tare da shi (). Dukkan wani dangi na tawaya, Allah ya tsarkaka daga barinsa, dukkan dangi na kamala, Allah ya siffanta da wannan. Dukkan siffar da ke nuna kamala, to Allah shi ne da mafi cikar wannan siffar: Ilimi kamala ne, to Allah shi ya fi kowa ilimi; ƙarfi kamala ne, to Allah ya fi kowa ƙarfi, adalci kamala ne, to Allah shi ya fi kowa adalci a bayan ƙasa.

Dangane da faɗin Manzon Allah () cewa, "....kuma ba ya karɓar abu, sai tsarkakakke....", idan an ce aiki tsarkakakke, to ana nufin abin da ya cika sharuɗɗa waɗanda shari'a da gindaya a kansa, aikin da aka dogara da Alƙur'ani da hadisi dangane da tabbatuwarsa.
Dangane kuwa da faɗinsa cewa, "....Allah ya umarci muminai da irin abin da ya umarci Manzanni da shi....", a nan wurin, ka ga Allah ya ce wa Manzanni, "Ku ci daga daɗaɗan abubuwa...." ya ce kuma da muminai, "Ku ci daga daɗaɗan abubuwan da muka azurta ku da shi." Irin abin da Allah ya kallafa wa Manzanni, ya ce lallai su yi, haka ya ɗora wa bayinsa muminai. Wannan yana nuna mana, dukkan abin da mutum zai yi Allah ya karɓa, to ya zamanto wannan abin tsarkakakke, halatacce ne, ya cika sharuɗɗan da shari'a take buƙata. Kowace irin ibada, sai ta cika wannan! Idan ibada za a yi ta da dukiya, to ya zamanto dukiyar da aka yi wannan ibada da ita, dukiya ce ta halal, ba dukiya ce da aka same ta ta hanyar maguɗi ba. In za ka yi masallaci, in za ka yi makaranta, in za ka je hajji ko umara, ko za ka biya wa wani ya je, to ya zamanto dukiya ce ta halal, da guminka ka samu; ta hanyar .. fatauci, ko ta hanyar kasuwanci, ko mutuwa aka yi aka bar ta a gidanku, sai ka sarrafa ta wannan tasarrufin, to wannan ya halatta, kuma kana da lada a kai. Amma in dukiya ta kasance ta “maguɗi ko haram ce, ko ta ƙwace ce, ko ta sata ce, ko ta sama dafaɗi ka same ta, to ko ka bayar da kujera ɗari ko miliyan, ba ka da lada a wajen Allah. Ko ka ɗauki kuɗin sata ka je hajji, ko ka je umara, ba za a karɓa maka ba, domin "....Allah tsarkakakke ne, ba ya kuma karɓar abu, sai tsarkakakke...." Saboda haka wajibi ne mutum ya nemi halak cikin dukkan abin da zai yi, sannan ya bayar da dukiya ta halal. Haka kuma, ta iya yiwuwa abin naka na halal ne, sai dai ba ya da nagarta, sai ka ɗauka ka bayar sadaƙa, to Allah ba ya son irin wannan sadaƙar. Kamar abinci ya lalace, sai ka ɗauka ka bayar sadaƙa, ko ka taskance shinkafa ko masara ko gero a suto, har ya fara lalacewa, ta yadda ko ka kai shi kasuwa ba zai yi ƙima ba, ba zai yi daraja ba, wannan Allah ba zai saurare ka ba, saboda Allah Ta'ala mai tsarki ne, kuma ba ya karɓar aiki sai mai tsarki. Kuma Allah yana ccwa,

(Ya ku waɗanda kuka yi imani! Ku ciyar daga daɗaɗan abubuwan da kuka tsururuta, da abin da muka fitar muku daga cikin ƙasa, kada ku nufaci lalatacce ku ce daga shi za ku ciyar, alhali ku ba za ku kabe shi ba, sai kun runtse idanu. Ku sani haƙiƙa Allah mawadaci ne abin godiya). [Bakara: 267]

Sannan Annabi () ya ambaci wani mutum da yake tsawaita tafiya: Wasu malamai sun ce tafiyar aikin hajji ce, wasu kuma sun ce tafiyar umara ce, wasu suka ce a'a! yana cikin tafiyar datake ta ɗa‘a ce. Ma'ana dai, wannan mutum yana cikin tafiya, kuma tafiyar ɗa'a ga Allah Ta‘ala, ga gashin kansa duk ya cure da juna, bai ma samu ya taje gashin kansa ba, duk ya ƙuƙƙulle saboda halin tafiya, sannan kuma, duk ya yi datti, ya yi ƙura. Manzon Allah () ya ambaci wannan mutum ya ce, "....yana miƙa hannayensa biyu biyu zuwa sama, yana cewa "Ya Rabbi! Ya Rabbi!!"amma kuma abincinsa haramun ne, abin shansa haramun ne, tufafinsa haramun ne, an ciyar da shi haram (tun yana yaro).
Ta yaya za a amsa masa (addu'arsa)?" Ma'ana, ai ba za a amsa masa ba. Sharaɗin da ake buƙata ga addu'a a yi ta, a karɓa, ya cika: Ga shi dai matafiyi ne, ana amsa addu'ar mutumin da yake matafiyi. Saboda haka lokacin tafiya, hali ne na amsa addu'ar mutum. Ga shi kuma, "....gashin kansa ya cakuɗe, ya yi ƙura...." wanda yake nuna yana cikin wahala. Duk mutumin da yake cikin halin tsanani, ana sa ran a karɓa masa addu’arsa, don Allah ya ce,

(Lallai a tare da tsanani akwai sauƙi. Lallai a tare da tsanani akwai wani sauƙi) [Sharahz5-6].

A nan wurin sauƙi biyu ne, tsanani ɗaya, waye zai rinjayi wani? Mutumin da ke cikin tsanani, ana sa ran sauƙi zai zo masa da wuri. Sannan kuma shi wannan mutumin da Manzon Allah () yake magana a kansa, ya yi riƙo da wani ladabi cikin ladubban addu'a, shi ne mutum ya ɗaga hannayensa sama. Annabi () in yana addu'a, yana ɗaga hannayensa sama. Hadisai mutawaturai suka zo daga Annabi () cewa, idan Annabi ()  yana addu'a yana ɗaga hannu sama, in ya gama addu'a kuma saukewa yake, ba ya shafa wa a fuska. Ga shi kuma mutumin ya tabbatar wa Allah rububiyyarsa, bai haɗa Allah da kowa ba, don yana cewa, ”Ya Rabbi! Ya Rabbi?!" Wato yana tabbatar wa Allah rububiyyarsa, imani da cewa ba wanda zai cire shi daga wannan abun, sai Allah. Tsabar tauhidi duk ya kankama, amma me ya kawo cikas aka ƙi karɓar addu'arsa? Abin da ya biyo baya shi ne, cewa, "....abincinsa haramun ne, abin shansa haramun ne, tufafinsa haramun ne, an ciyar da shi haram, ta yaya za a amsa masa (addu'arsa)?" Ba wai don addu'ar ce bai karanta daidai ba, ya karanta daidai; ba wai don bai ɗaga hannu ba, ya ɗaga hannu; ba wai don bai cancanta ba, ya cancanta, tunda yana cikin tsanani, amma me ya kawo masa cikas? Sharuɗɗai sun cika, amma sai aka samu wani abu da ke hanawa. Kamar mutum ne ya cancanci cin gado ta kowacce fuska, sai wani abu ya zo ya hana shi cin gado: Misali akwai dangantaka tsakaninsa da mamaci, kuma lallai mamacin ya mutu wannan yana da rai, ka ga dukkan sharuɗɗai da ake buƙata sun cika, wannan musulmi ne, wannan musulmi ne, sai muka bincika sai muka ga wannan ɗan, shi ya kashe mahaifinsa, ka ga ba za mu ba shi gado ba, tunda shi ya kashe mahaifinsa. Wannan hadisin yana nuna mana yunƙurin neman halal a cikin dukkanin al’amura: In za mu yi tufafi, ya zamanto halal ne, haka in za mu ci, ya zamanto halal ne, domin duk inda haramun take, ba ta da albarka, halal ita ce mai albarka, halal za ka ci ka kwanta lafiya, haram kuwa idan ka ci, ko ba ta tashi a nan ba, to za ta tashi a can. Saboda haka ya kamata mutum ya kiyaye wannan. Allah yana cewa;
 (Ka ce, "Halal da haram ba su zama ɗaya ba, ko da yawan harmun ɗin nan ya burge ka."). [Al Ma‘ida: 100].

ARBA'UNA HADITH (9) HADISI NA TARA

An karɓo daga Abu Huraira Abdur-Rahman ɗan Sakhrin (R.A), ya ce, na ji Manzon Allah () yana cewa, "Duk abin da na hane ku (da bari), to ku nisance shi. Abin da na umarce ku da shi, to ku zo da shi (wannan abin) gwargwadon iko. Abin da ya hallakar da waɗanda suke kafin ku, yawan tambayoyinsu, da saBawarsu ga Annabawansu."Bukhari (#7288) da Muslim (#1337) suka rawaito shi.

SHARHI

Wannan hadisi, an karɓo shi daga Abu Huraira, Iimamin masu hadisi cikin sahabban Annabi (). Sunansa shi ne Abdur-Rahman bin Sakhrin Addausiy. Malamai sun yi

Sep 12, 2011

ARBA'UNA HADITH (8) HADISI NA TAKWAS

An karɓo daga Abdullahi ɗan Umar (R.A) ya ce, "Lallai Annabi () ya ce, "An umarce ni in yaƙi mutane, har sai sun shaida babu abin bauta wa bisa cancanta sai Allah, (sun yarda Annabi) Muhammad Manzon Allah ne, su tsayar da sallah, kuma su bayar da zakka. Idan sun aikata haka, sun kare jininsu da dukiyoyinsu daga gare ni, sai da haƙƙin musulunci, hisabinsu yana wajen Allah Maɗaukaki." Bukhari (#25) da Muslim (#22) ne Suka ruwaitoshi.
                       
SHARHI
Da Annabi () ya ce, "An umarce ni in yaƙi mutane....", a nan kafuai ake nufi, ba dukkan mutane ba. Wannan wani salone na larabci, salo ne na Alƙur'ani, salo ne na hadisi, a

ARBA'UNA HADITH (7) HADISI NA BAKWAI

An Karɓo daga Abu Ruƙayya, (shi ne) Tamim ɗan Ausid Dari (R.A) ya ce, Annabi () ya ce, "Addini nasiha ne!" Sai muka ce, "Ga wa?" sai ya ce, " (Nasiha ne) ga Allah, da Littafinsa, da Manzonsa, da shugabannin musulmi, da dukkan mutane" Muslim ne ya rawaito (#55)

SHARHI

A larabce abin da kalmar annasiha take nunawa, shi ne tace zuciyarka, wanke zuciyarka dangane da wanda aka ce ka yi masa nasiha ɗin. Don haka shi tace zuciya ya sha bamban: Idan ya zamanto tace zuciya ga Allah ne, to kenan kar ka

ARBA'UNA HADITH (6) HADISI NA SHIDA

An karɓo daga Abu Abdullahi, Nu'uman ɗan Bashir, (R.A) ya ce, "Na ji Manzon Allah () yana cewa, "Lallai halal a bayyane take, kuma lallai haramun a bayyane take, amma a tsakaninsu akwai al'amura masu rikitarwa, da yawa daga cikin mutane ba su san su ba. Duk wanda ya nisanci abubuwa masu rikitarwa, haƙiƙa ya nemi kuɓutar da addininsa da mutuncinsa. Wanda ya auka cikin abubuwa masu rikitarwa, to ya auka cikih haram. Kamar makiyayi ne da yake kiwo a gefen shinge, ya kusanta ya shiga (ya yi kiwo) a cikinsa. Ku saurara! Kowane sarki yana da iyaka. Ku saurara! Iyakar Ubangiji ita ce abubuwan da ya haramta. Ku saurara! Lallai a cikin jiki akwai wata tsoka, idan ta gyaru, dukkan jiki ya gyaru, idan ta lalace, dukkan jiki ya lalace. Ku saurara! (Wannan tsokar ɗaya) ita ce zuciya."
Bukhari #59 da Muslim (#1599).

SHARHI
Ma'ana, halal a bayyane yake a cikin Alƙur'ani da hadisai tabbatattu daga Annabi (), haka kuma haramun a bayyane yake a cikin Alkur’ani da hadisai tabbatattu daga Annabi (), amma a tsakanin halal da haram, akwai

KITABUT-TAUHID (Babi Na Goma Sha Biyar15)

  SHARHI Babukan da suka wuce sun yi magana a kan yana daga dangin shirka neman taimako wajen wanin Allah. Wannan babi kuma zai nuna maka ...