GABATARWA.



WWW.TAFARKINSUNNAH.BLOGSPOT.COM

WANNAN SHAFI YANA DAUKE DA HADISAN ANNABI(SAW)ACIKIN HARSHEN HAUSA. IDAN ANGA MUNYI KUSKURE ASANAR DA MU.ALLAH YAYI MUNA JAGORA AMEEN!



DAMIN AIKO DA GYARA KO KARIN BAYANI;
{tafarkinsunnah@gmail.com]

Nov 15, 2011

ARBA'UNA HAADITH (38) HADISI NA TALATIN DA TAKWAS


An karɓo daga Abu Hurairata (R.A) ya ce, Manzon Allah () ya ce, Allah Ta'ala ya ce, "Duk wanda ya yi gaba da waliyina, to na ba shi sanarwa ya zo ya yi yaƙi da ni. Bawana ba zai kusance ni ba, da wani abu da na fi ƙauna, sama da abin da na wajabta masa. Bawana ba zai gushe ba yana kusanta ta da nafilfili, har sai na zamanto ina ƙaunarsa, idan na ƙaunace shi, sai na kasance jinsa, da yake ji da shi, da ganinsa, da yake gani da shi, da hannunsa, da yake damƙa da shi, da ƙafarsa, da yake tafiya da ita. Wallahi, idan ya roƙe ni, zan ba shi abin da ya roƙa, kuma wallahi, idan ya nemi tsarina, zan tsare shi." Bukhari ne ya rawaito shi (#6502).

SHARHI
Abin da ake nufi da waliyin Allah a nan, shi ne duk wanda yake ƙaunar Manzonsa (), mace ce ko namiji, a da ne, ko a yanzu, in dai mumini ne, mai ƙaunar Allah, to ya zama
waliyyi.

Wannan hadisi da dama daga cikin 'yan bidi’a sun ribace shi wajen fassara shi da cewa Ubangiji na iya shiga gangar jikin bawa, ya zamanto Allah ya cakuɗa da bawansa Wa’iyazu billahi! Wannan mummunar aƙida wadda take daga 'yan mishan (kiristoci), sufaye sun ɗauko ta, musammam ma irinsu Hallaj da Ibnu Arabi duk suna da irin waɗannan munanan aƙidu a wake ke a rubuce. In ka tambaye su meye hujjarku, sai su ce, ai Allah ya ce, matukar bawa ya aikata farilla ya yi nafila, Allah zai zama ganinsa, sai ya zamanto mutum ya zama shi da Allah sun zama ɗaya kenan. Haka suka fassara wannan hadisin! Malaman sunna sun fassara wannan hadisin da cewa, abin da hadisin ke nufi shi ne, Allah zai sa bawa a kan daidai, zai kasance jinsa; ba zai rinƙa sauraron komai ba, sai abin da Allah ya yarda da shi, in sun ji ashariya, sai su toshe kunnensu, in sun ji mummunar magana, sai su toshe kunnansu. Wato Allah ya tsare su, ta yadda babu yadda za a yi wata Barna, sai Allah ya kare su, ba sa son ji. Allah ya kasance jinka kenan! Haka Allah zai kare ganinka; ba za ka kalli komai ba, sai abin da yake na halal, wanda Allah ya yi izini a kalle shi. Duk abin da yake haramun ne, sai ka ga Allah ya kare ka, ba ka iya kallonsa, da ka gan shi kiciɓis, ba tare da niyya ba, sai ka kauda idonka. Haka sai Allah ya zamanto hannunsa da yake bayar wa ko amsa; zai zamanto ba za ka bayar ba da hannunka, sai abin da yake halal ne, ba za ka karɓa ba, sai abin da yake halal, ba ka zubar da jinin wani, ba ka ɗaukar dukiyar wani, ba ka cutar wani. Haka ƙafarsa; sai ya kasance duk inda za ka taka ka je da ƙafarka, wajen yi wa Allah da‘a ne, ba wajen saɓa masa ba ne. Za ka samu wannan ne, idan ka tsayar da farillai daidai, kuma kana yawan yin nafila. Azumin Ramadan, kana yin sa daidai bisa ga tsarin Annabi (), kana kiyaye ladubban da ke ciki, tun daga sahur har izuwa buɗa baki; kana kuma yin azumin Sitta Shawwal, kana ƙoƙarin yin azumin Arfa, kana ƙoƙarin yin azumi uku kowanne wata. Sannan kuma kana ƙoƙarin yin sallah ta farilla da ta nafila, kana yin shafa'i da wutiri. To in kana haka, sai ka ga Ubangiji ya azurta ka da irin wannan: Jinka da ganinka da hannunka da ƙafarka, duk ba za ka aiwatar da su ba, sai ta hanyar abin da yake da'a ne ga Allah. Wannan shi ne abin da hadisin yake nufi, ba wai ana nufin Allah ya zama bawa ba. Wannan ba zai yiwu ba!

Shi ya sa malaman sunnah suka ce, idan ka duba hadisin, za ka ga ɓangare biyu ne da shi, akwai wanda ake kusanta, da wanda yake kusanta ɗin; da mai roƙo da wanda ake roƙo; mai neman tsari da wanda ake neman tsarin a wurinsa. A cikln hadisin, cewar, "Bawana ba zai gushe yana kusanta ta....", ka ga nan mai neman kusanci shi ne bawa, wanda ake neman kusancinsa shi ne Allah; wanda yake bayarwa in an roƙe shi, shi ne Allah, wanda yake roƙon shi ne bawa; mai neman tsari shi ne bawa, wanda ake neman tsari a wajensa, shine Allah. Ka ga wannan ya tabbatar da cewa abubuwa ne guda biyu. To ta yaya kai ka dunƙule su, suka zama ƙwaya ɗaya, tun daga farkonsu har izuwa ƙarshensu, ka ce sun dunƙule sun zama ɗaya? Wannan ita ce fassarar da malamai
suke yi wa wannan hadisi.

No comments:

Post a Comment

KITABUT-TAUHID (Babi Na Goma Sha Biyar15)

  SHARHI Babukan da suka wuce sun yi magana a kan yana daga dangin shirka neman taimako wajen wanin Allah. Wannan babi kuma zai nuna maka ...