GABATARWA.



WWW.TAFARKINSUNNAH.BLOGSPOT.COM

WANNAN SHAFI YANA DAUKE DA HADISAN ANNABI(SAW)ACIKIN HARSHEN HAUSA. IDAN ANGA MUNYI KUSKURE ASANAR DA MU.ALLAH YAYI MUNA JAGORA AMEEN!



DAMIN AIKO DA GYARA KO KARIN BAYANI;
{tafarkinsunnah@gmail.com]

Nov 24, 2011

ARBA'UNA HAADITH (50) HADISI NA HAMSIN


An karɓo daga Abdullahi ɗan Busur, (R.A) yace wani mutum (mazaunin karkara ) yazo wurin Annabi (ﷺ),   yace ya Manzon Allah shari’oi sun yi mana yawa a bamu wani babu gamamme da zamu riƙe. Sai Annabi (ﷺ),  yace "kada harshenka ya bushe wajen
ambaton Allah "Ahmad ne ya rawaito shi (#188, 190).

SHARHI;

Wannan hadisin yana nuna cewa, wani mutum mazaunin karkara yazo wurin manzon Allah (ﷺ),  yace dashi ya manzon Allah shari’oi sun yi mana yawa an ce kayi kaza, ka bar kaza, don haka a faɗi wani guda ɗaya wanda zamu riƙe wanda ba gudu baja da ya sai anyi shi ko ana cikin me, Sai Annabi (ﷺ),  yace, kada harshenka ya bushe wajen ambaton Allah in dai kana son abin da zaka rike ba wahala kayi, komai kuɗinka komai talaucinka zaka iya yi ko kana da muƙami ko baka dashi kana kwance, a gadon asibiti ko a gida kake

ARBA'UNA HAADITH (49) HADISI NA ARBA'IN DA TARA


An karɓo daga Umar ɗan Khaɗɗab (R.A) daga Annabi yace, da ace kuna dogara ga Allah haƙiƙanin dogaro da Shi da Allah ya azurta ku kamar yadda yake azurta tsuntsaye. Suna sammako da yunwa amma suna dawowa
 da yamma suna ƙoshe. Imam Ahmad (# 01,52) da Tirmizi (#2344) da Nasa’i a cikin Sunnan Alkubra (J 8/ sh 79) da Ibnu Majah (#4164) da Ibnu Hibban ya inganta shi (730) da Hakin (418) Tirmizi yace, hadisi ne ingantacce.

ARBA'UNA HAADITH (48) HADISI NA DA TAKWAS


An karɓo daga Abdullahi ɗan Amru (R.A) daga Annabi (ﷺ),  ya ce, “abubuwa guda huɗu wanda suka kasance tare da shi ya kasance munafiki, wanda siffa ɗaya ta kasance tare da shi daga huɗun nan, to lallai siffa ta munafinci na tare da shi, har sai ya bar ta, idan yayi magana, ya zamanto ya yi ƙarya, Idan ya yi alƙwari, sai ya
zamanto ya saɓa, Idan an yi rigima dashi, sai ya ƙetare dokar Allah, idan kuma aka ƙulla alƙawari, to zai yaudare ka. Bukhari (#34) da Muslim(#58) suka rawaito shi.

SHARHI;


Waɗannan siffofi guda huɗu in sun taru ga mutum, to ya zama munafiki, in kuwa ɗaya ce, to wanan ya zama yana da siffa ta munafunci.To amma abin da ake nufi da munafunci a nan gurin, munafuncin aiki. Don munafunci iri biyu ne: akwai Annifaƙul Amali,

ARBA'UNA HAADITH (47) HADISI NA ARBA'IN DA BAKWAI


An karɓo daga Miƙdamu ɗan Ma'adi Yakrib (R.A) ya ce "Naji Manzon Allah (ﷺ),  yana cewa, "Dan Adam bai taɓa cika wani boki ba, ko wani ƙoƙo mafi sharri, sama da cikinsa ba. Ya ishi ɗan Adam waɗansu 'yan lomomi, wanda za su tsaida masa gadon bayansa (Yunwa ba zata galabaita shi ba). Idan dole (sai ya ci abinci da yawa), sai
ya kasa cikinsa kasha uku, kashi ɗaya abinci, kashi na biyu ruwan sha, kashi ɗayan ya bar wa numfashi."
Ahmad (J4/ sh 132) da Tirmizi (#2380) da Ibnu Majah (3349) Tirmizi ya ce, Hadisi ne mai kyau.

SHARHI;

ARBA'UNA HAADITH (46) HADISI NA ARBA'IN DA SHIDA


An karɓo daga ɗan Abu Burda, daga babansa, daga Abu Musal Ash’ariy (R.A) ya ce, Annabi (ﷺ),  ya tura shi ƙasar Yemen, sai ya tambaye shi dangane da wani abin sha da ake yi a can, sai ya ce, “Menene abin?” Sai ya ce,“Albit’u da Almizru.” sai aka ce da Abu Burda, “Menene Albit’u?” sai ya ce,
wani tsimi ne da ake yi da zuma, almizru kuwa wani tsimi ne da ake yi da alkama. Sai Annabi (ﷺ),  ya ce, “Duk abu mai sa maye haramun ne.” Bukhari ne rawaito shi (#4343).

SHARHI;


Da manzon Allah (ﷺ),  ya ce, “Duk abu mai sa maye haramun ne….” sai malamai suka ce abin da yake sa maye abu biyu ne: Awai abin da yake sa maye, ya kuma sa ka walwala da jin daɗi. Giya tana sa maye, tana sa walwala da jin daɗi, wani farin cikin na babu-gaira-babu-dalili. To wannan giya kenan, ittifaƙin haramun ne. Amma akwai abin da zai sa ka

Nov 18, 2011

ARBA'UNA HAADITH (45) HADISI NA ARBA'IN DA BIYAR

An karɓo daga Jabir ɗan Abdullahi (R.A) ya ce, “Naji Manzon Allah(ﷺ),  a shekarar buɗe Makka, a lokacin (Manzon Allah(ﷺ),  ) yana Makka, yana cewa “Lallai Allah da Manzonsa sun haramta sayar da giya da mushe da alade da gunki.” Sai aka ce, Ya Manzon Allah(ﷺ), ! Ba mu labari game da kitsen mushe, ana shafawa a jikin jirgin ruwa, ana shafawa a fata, ana kunna fitilu da shi, (shin ya halatta ko bai halatta ba?).”

ARBA'UNA HAADITH (44) HADISI NA ARBA'IN DA HUDU

An karɓo daga A’isha (R.A) ta ce, Manzon Allah (ﷺ),  ya ce, “Shayarwa tana haramta abin da haihuwa take haramtawa.” Bukhari (#2646) da Muslim (#1444) suka rawaito shi.

SHARHI;


Ma’ana, idan mace ta haife ka

tana da matsayin mahaifiyarka, ba ka aure ta a shari’ance; ba ka auren duk ‘yayan da ta haifa; ba ka da aurenƙannenta, domin sun zama ƙannen mahaifiyarka, ‘ya’yan da ta haifa sun zama yayayenka ko ƙannenka, ba ka auren mahaifiyata, ta zamanto kakarka. To haka matar da ta shayar da kai, ba ka aurenta  a shari’ance; ba ka auren ‘ya’yanta a shari’ance, domin sun zama yayyenka ko ƙannenka; ba ka auren

ARBA'UNA HAADITH (43) HADISI NA ARBA'IN DA UKU

An karɓo daga ɗan Abbas (R,A) ya ce, Manzon Allah (ﷺ),  ya ce, “Ku riskar da kowanne rabon gado sananne ga ma’abotan wannan rabon, abin da ya ragu, to a ba namiji wanda

ya fi kusanci.” Bukhari (#6732) da Muslim (#1615) ne suka rawaito shi.
SHARHI;


Abin da wanna hadisi yake nufi shi ne, rabon gado kashi biyu ne: Akawai waɗanda ake basu da farali, wato masu rabo sananne, wanda shi kuma ya kasu kashi shida: ko a ce a baka rabin dukiya (1/2), ko ɗaya bisa hudu (1/4) na dukiya, ko ɗaya bisa takwas(1/8) na dukiya, ko ɗaya bisa uku (1/3) na dukiya, ko biyu bisa ukun (2/3) na dukiya, ko ɗaya bisa

ARBA'UNA HAADITH (42) HADISI NA ARBA'IN DA BIYU

An karɓo daga Anas ɗan Malik (R.A) ya ce, “Na ji Manzon Allah (ﷺ),  yana cewa, Allah Maɗaukakin Sarki yana cewa, “Ya kai ɗan Adam! Lallai ba za ka bauta min ba, kuma ka sanya rai game da rahamata ba, face sai na gafarta maka ban damu ba. Ya kai ɗan Adam! Da a ce zunubanka zasu cika sashen sama gaba ɗaya, sannan ka nemi gafarata, sai in gafarta maka. Ya kai ɗan Adam!

Da a ce zaka zo min da cikin ƙasa gaba ɗaya zunubai ne, sannan ka gamu dani, ba tare da ka haɗa ni da kowa ba, Ni kuma zan kawo maka gafara, cikin ƙasa.” Tirmizi ne ya  rawaito shi (#3540) ya ce, hadisi ne mai kyau, ingantacce.

ARBA'UNA HAADITH (41) HADISI NA ARBA'IN DA DAYA

An karɓo daga Abu Muhammad Abudullahi ɗan Amru ɗan As (R.A) ya ce, Manzon Allah (ﷺ),  ya ce, “Ɗayanku ba ya zama mumini, har sai son zuciyarsa yana biyayya ga abin da na zo da shi.” Hadisin ne ingatacce, mai kyau, mun rawaito shi a cikin littafin Hujja da sanadi ingantacce.

SHARHI;

Wanna hadisi an karɓo shi daga Abu Muhamad, shi ne Abdullahi ɗan Amru ɗan As, ɗaya daga cikin ‘Abadila’ (wato waɗanda ake kira Abdullahi ) a cikin sahabbai,
waɗanda su huɗu ne, duk sunansu ya fara Abdullahi: su ne, Abdullahi bn Umar, Abdullahi bn Abbas, Abdullahi bn Mas’ud da Abdullahi bn Amru bn As. Waɗannan

Nov 15, 2011

ARBA'UNA HAADITH (40) HADISI NA ARBA'IN


An karɓo daga Abdullahi ɗan Umar (R.A) ya ce, Manzon Allah (ﷺ),  ya dafa kafaɗata ya ce, “Ka kasance a duniya tamkar kai baƙo ne, ko kuma wanda yake kan hanya.” Ɗan Umar (R.A) yana cewa, “Idan ka kai yamma, kar ka yi jiran safiya, idan kuma ka wayi gari, to kar ka jira yamma. Ka riƙi aiki alheri lokacin lafiyarka, saboda lokain rashin lafiyarka. Ka riƙi aiki alheri lokacin rayuwarka, saboda ka
amfana lokacin mutuwarka.” Bukhari ne ya rawaitoshi. (#6416).

SHRHI;

Manzon Allah (ﷺ),  ya ce, “Ka kasance a gidan duniya tamkar baƙo ne…”

ARBA'UNA HAADITH (39) HADISI NA TALATIN DA TARA


An karɓo daga ɗan Abbas (R.A) ya ce Manzon Allah (ﷺ),  ya ce, “Allah Ya yafe wa al’ummata, abin da ta yi dakuskure, da mantuwa, da abin da aka tilasta ta.” Hadisi ne mai kyau Ibnu Majah ne ya rawaito shi (#2045) da Baihaƙi a cikin Sunan.

SHARHI;

Waɗannan abubuwa guda uku an yafe wa Al’ummar Annabi (ﷺ), . Kuma wannan ɗaya ne daga cikin abin da yake nuna falalarmu a kan sauran al’ummai, saboda sauran al’ummai ba a basu wannan damar ba. Mu kaɗai ne muke da irin wannan damar, don ya ce a hadisin, “Allah Ya yafe wa al’ummata…” wanan ya nuna sauran al’ummar da suka gabata, ba su sami wannan falalar ba.

ARBA'UNA HAADITH (38) HADISI NA TALATIN DA TAKWAS


An karɓo daga Abu Hurairata (R.A) ya ce, Manzon Allah () ya ce, Allah Ta'ala ya ce, "Duk wanda ya yi gaba da waliyina, to na ba shi sanarwa ya zo ya yi yaƙi da ni. Bawana ba zai kusance ni ba, da wani abu da na fi ƙauna, sama da abin da na wajabta masa. Bawana ba zai gushe ba yana kusanta ta da nafilfili, har sai na zamanto ina ƙaunarsa, idan na ƙaunace shi, sai na kasance jinsa, da yake ji da shi, da ganinsa, da yake gani da shi, da hannunsa, da yake damƙa da shi, da ƙafarsa, da yake tafiya da ita. Wallahi, idan ya roƙe ni, zan ba shi abin da ya roƙa, kuma wallahi, idan ya nemi tsarina, zan tsare shi." Bukhari ne ya rawaito shi (#6502).

SHARHI
Abin da ake nufi da waliyin Allah a nan, shi ne duk wanda yake ƙaunar Manzonsa (), mace ce ko namiji, a da ne, ko a yanzu, in dai mumini ne, mai ƙaunar Allah, to ya zama

ARBA'UNA HAADITH (37) HADISI NA TALATIN DA BAKWAI


An karɓo daga ɗan Abbas (R.A) daga Manzon Allah () cikin irin abin da ya rawaito daga Ubangijinsa, ya ce, "Allah ya riga ya rubuta ayyukan alheri da munanan
ayyuka, wanda duk ya hinmatu zai aikata wani kyakkyawan aiki, sai bai samu aikatawa ba, Allah zai rubuta masa kyakkyawan aiki guda ɗaya cikakke. Idan ya himmatu zai aikata wani kyakkyawan aiki, kuma ya aikata shi, to Ubangiji zai rubuta masa lada goma, izuwa ninki ɗari bakwai, zuwa ninkininki da yawa. In ya himmatu zai aikata mummunan aiki, kuma bai aikata ba, Allah zai rubuta masa kyakkyawan aiki cikakke a wurinsa. Idan ya himmatu da mummunan aiki, kuma ya aikata shi, Allah zai rubuta masa mummunan aiki guda ɗaya” Bukhari (#6491) da Muslim (#131) a cikin sahihan littattafansu.

ARBA'UNA HAADITH (36) HADISI NA TALATIN DA SHIDA


An karɓo daga Abu Hurairata (R.A) daga Annabi () ya ce, "Wanda duk ya kautar wa da mumini wani baƙin ciki, daga baƙin cikin duniya, to Allah zai kautar masa da wani baƙin ciki daga cikin irin baƙin cikin ƙiyama, duk wanda ya kawo sauƙi ga wanda yake cikin tsanani, Allah zai kawo masa sauƙi a duniya da lahira, wanda ya suturce musulmi, to Allah zai yi masa sutura a duniya da lahira. Lallai Allah yana cikin taimakon bawa matuƙar bawan ya kasance mai taimakon ɗan uwansa musulmi. Wanda duk ya kama wani tafarki yana neman ilimi a wannan tafarkin, Allah zai sauƙaƙa masa hanyar shiga aljanna. Babu wasu mutane da za su taru a cikin wani ɗaki cikin ɗakunan Allah, suna karanta littafin Allah, suna darasinsa a tsakaninsu da juna, face sai nutsuwa ta sauka a kansu, rahama ta lullube su, (Mala'iku sun kewaye su), sai kuma Allah ya ambacesu a fadarsa. Wanda duk aikinsa ya yi sanɗa da shi, to dangantakarsa ba za ta yi gaggawa da shi ba." Muslim ne ya rawaito shi (#2699) da Wannan lafazi.

ARBA'UNA HAADITH (35) HADISI NA TALATIN DA BIYAR


An karvo daga Abu Hurairata (R.A) ya ce, Manzon Allah (ﷺ) ya ce, "Kada ku riqa yi wa juna hassada, kada ku yi kore, kada ku yi qiyayya da juna, kada ku juya wa juna bayanku, kada sashenku ya yi ciniki a, cikin cinikin xan uwansa. Ku kasance bayin Allah, 'yan uwan juna. Musulmi xan uwan musulmi ne, kada ya zalunce shi, kada ya kunyatar da shi, kada ka yi masa qarya, kada ya wulaqantar da shi. Tsoron Allah yana nan (har sau uku)." Yana nuna kirjinsa, "Ya ishi mutum sharri, ya rinqa tozartar da xan uwansa musulmi. Jinin kowanne musulmi da dukiyarsa da mutuncinsa, haramun ne a kan musulmi“ Muslim ne ya rawaito shi (#2564).

ARBA'UNA HAADITH (34) HADISI NA TALATIN DA HUDU


An karɓo daga Abu Sa'id Alƙhuduriy (R.A) ya ce, “Na ji Manzon Allah () yana cewa, "Duk wanda ya ga abin ƙi, to ya gusar da shi da hannunsa, in ba shi da iko, ya gusar da shi da harshensa, in ba shi da iko, to ya ƙi abin a zuci, wannan shi ne mafi raunin imani" Muslim ne ya rawaito shi (#49).

SHARHI
Malamai suka ce, wannan hadisi yana cikin nassosin da ke nuna wajabcin umami da kyakkyawan aiki, da hani ga mummuna. Wannan kuma shi ne tabbatacce cikin ayoyin

ARBA'UNA HAADITH (33) HADISI NA TALATIN DA UKU


An karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas (R.A) ya ce, Manzon Allah () ya ce, "Da za a bai wa mutane dukkan da'awarsu, da waɗansu sun yi da'awar dukiyar waɗansu da jininsu, sai dai hujja tana kan mai da'awa, rantsuwa kuma a kan wanda ya yi musu." Baihaƙi ne ya rawaito shi a cikin littafinsa Sunan (J 10/ sh 252). Wani sashi na hadisin yana cikin Bukhari da Muslim.

SHARHI
Ma‘ana, da duk da'awar da mutane za su yi, za a ɗauka a ba su wannan abin da suka yi da'awa, misali in sun ce kaza namu ne, a ba su, ba tare da shaida ba, ba tare da an bincika

ARBA'UNA HAADITH (32) HADISI NA TALATIN DA BIYU


An karɓo daga Abu Sa'id, Sa'ad ɗan Malik ɗan Sinan Al-Khudriy (R.A) ya ce, Manzon Allah () ya ce, "Ba cuta, babu cutarwa." Ibnu Majah ne ya rawaito shi (#2341) da Daraƙuzuni (#228) da waninsu Musnadan. Haka Imamu Malik ya rawaito shi a cikin Muwaɗɗa (J2/sh 746) daga Amru ɗan Yahya daga babansa daga Annabi () Mursalan, bai ambaci Abu Sa'id ba. Amma hadisin yana da hanyoyin da sashinsu yana ƙarfafa sashi.

ARBA'UNA HAADITH (31) HADISI NA TALATIN DA DAYA


An karɓo daga Abu Abbas, Sahlu ɗan Sa'ad Assa'idi (R.A) ya ce, "Wani mutum ya zo wajen Annabi () ya ce da shi "Ya Manzon Allah! Nuna min aikin da idan na aikata shi, Allah zai ƙaunace ni, mutane ma za su ƙaunace ni." Sai (Annabi ) ya ce, "Ka yi zuhudu cikin lamarin duniya, sai Allah ya ƙaunace ka, kuma ka nisanci abin da ke hannun mutane, sai mutane su ƙaunace ka." Ibnu Majah ne ya rawaito shi (#4102) da waninsa ta hanyoyi masu kyau.

Nov 8, 2011

ARBA'UNA HAADITH (30) HADISI NA TALATIN

An karɓo daga Abu Sa'alaba shi ne Jursumu ɗan Nashib (R.A) ya ce, Manzon Allah () ya ce, "Lallai Allah Ta'ala ya farlanta farillai, kar ku tozarta su, ya sanya iyakoki, kar ku ƙetare su, ya haramta wasu abubuwa, kada ku keta alfarmarsu, ya yi shiru game da waɗansu al’amura don jinƙan ku, ba don mantuwa ba, kar ku bincike su. Daraƙuɗuni ne ya rawaito shi a cikin littafinsa Sunan (J 4 sh 184) da waninsa.

SHARHI
Faɗin Manzon Allah () cewa, "....Allah Ta'ala ya farlanta farillai, kar ku tozarta su...." yana nufin lallai ku tsayar da wannan farillan yadda Allah ya ɗora muku su

ARBA'UNA HAADITH (29) HADISI NA ASHIRIN DA TARA

An karɓo daga Mu'azu ɗan Jabal (R.A) ya ce, "Na ce, Ya Manzon Allah! Ba ni labarin wani aiki da zai shigar da ni aljanna, ya kuma nisantar da ni daga wuta.“ Sai ya ce, "Haƙiƙa ka yi tambaya game da abin da yake mai girma, sai dai abu ne mai sauƙi ga wanda Allah ya sauƙaƙe shi gare shi. Ka bauta wa Allah, ba tare da ka haɗa shi da wani ba, kuma ka tsayar da sallah, kuma ka ba da zakka, kuma ka azumci Ramadan, sannan ka ziyarci ɗakin Allah." Sannan sai (Annabi ) ya ce, "Shin ba zan shiryar da kai ƙofofin alheri ba? Azumi garkuwa ne, sadaƙa kuma tana shafe kurakurai, kamar yadda ruwa yake kashe wuta, haka sallar mutum a cikin yankin dare. Sannan ya karanta (faɗin Allah), "...gefen jikinsu yana nisantar gurin kwanciyarsu. . . " har ya kai inda (Allah yake cewa ’Ya'amaluun' sannan sai Annabi ) ya ce, "Ba zan ba ka labarin kan al'amarin ba, da ginshikinsa da ƙololuwar Samansa?" Sai na ce "Eh!" sai ya ce, "Kan al'amarin (shi ne) musulunci, ginshiƙinsa kuwa salla, ƙololuwar samansa kuwa jihadi." (Sai Annabi  ) ya ce, "Ba zan ba ka labarin abin da yake mallakar kusan gaba ɗaya ba?" sai na ce "Ba ni labari." sai ya kama harshensa ya ce, "Ka riƙe wannan." Sai na ce, "Shin yanzu za a kama mu da maganar da muka yi?" sai (Annabi ) ya ce, "Da ma mahaifiyarka ta rasa ka! Akwai abin da yake jefa mutane wuta a kan fuskokinsu (ko ya ce) kan hancinsu, sai sakamakon abin da harshensu ya faɗa." Tirmizi (#2616) ya ce, hadisi ne mai kyau, ingantacce.

ARBA'UNA HAADITH (28) HADISI NA ASHIRIN DA TAKWAS

An karɓo daga Abu Najih, shi ne Irbadu ɗan Sariya (RA) ya ce, "Manzon Allah () ya yi mana wa'azi, wa'azi mai isarwa, zukata suka tsorata, ldanu suka zubar da hawaye. Sai muka ce da shi, "Ya Manzon Allah ()! Kamar wa'azin mai ban kwana? To ka yi mana wasici." Sai ya ce, "Ina muku wasici da jin tsoron Allah, da kuma ji da bi, ko da bawa ne ya zama shugaba a gare ku. Lallai wanda ya rayu a cikinku, da sannu zai ga saɓani mai yawa. Na umarce ku, ku riƙe sunnata, da sunnonin halifofi shiryayyu, ku riƙe ta da hakoranku (fiƙa), ku kiyayi fararrun al'amura, domin kowace bidi'a ɓata ce. Abu Dawud (#4607) da Tirmizi (#2676) suka rawaito shi, Tirmizi ya ce, wannan hadisi ne mai kyau, ingantacce."

ARBA'UNA HAADITH (27) HADISI NA ASHIRIN DA BAKWAI

An karɓo daga Nawas ɗan Sam'an (R.A) ya ce, Manzon Allah () ya ce, "Aikin ɗa'a shi ne kyawawan dabi'u, laifi shi ne abin da ya yi kai kawo a zuciyarka, kuma ba ka so mutane su ga kana yin wannan abin." Muslim (#2553) ya rawaito.

An karɓo daga Wabisa (R.A) ya ce, "Na zo wurin Annabi (), sai ya ce, "Ka zo ne kana tambaya dangane da ɗa'a?" Sai na ce, "Na‘am!" Sai ya ce, "Ka yi wa zuciyarka fatawa,

ARBA'UNA HAADITH (26) HADISI NA ASHIRIN DA SHIDA


An karɓo daga Abu Hurairata (R.A) ya ce, "Manzon Allah () ya ce, "Dukkan gaɓɓai na mutane akwai sadaƙa a ciki, kowanne yini da rana ke hudowa cikinsa, da za ka sasanta tsakanin mutane biyu, da ke rigima da juna sadaƙa ne, ka taimaki mutum game da dabbarsa, ka ɗora shi a kai, ko ka ɗauki kayansa ka ɗora masa a kan dabbar, sadaƙa ne; kalma daddaɗa sadaƙa ce; dukkan taku da za ka yi tattaki zuwa sallah, sadaƙa ne; ɗauke wani abu mai cutarwa daga kan hanya sadaƙa ne." Bukhari (#2989) da Muslim (#1009) suka rawaito shi!”

Oct 26, 2011

ARBA'UNA HADITH (25) HADISI NA ASHIRIN DA BIYAR


An karɓo daga Abu Zarril Al Gifari (R.A) ya ce, "Waɗansu mutane daga cikin sahabban Annabi ()sun ce da shi, "Ya Manzon Allah ()! Ma'abota dukiya sun tafi da lada, suna yin sallar (farilla) kamar yadda muke yi, suna yin azumin (farilla) kamar yadda muke yi, amma kuma suna sadaƙa da sauran dukiyarsu. Sai Annabi () ya ce, "Shin Allah bai riga ya ba ku abin da za ku yi sadaƙa da shi ba ne? Dukkan tasbihi sadaƙa ne, dukkan wata kabbara sadaƙa ce, dukkan wata hamdala sadaƙa ce, dukkan wata hailala sadaƙa ce, umarni da kyakkyawan aiki sadaƙa ne, hana mummunan aiki sadaƙa ne, a gaɓar kowanne daga cikinku akwai sadaƙa"sai sahabbai suka ce "Ya Manzon Allah! Yanzu mutum zai biya buƙatarsa kuma ya zama yana da lada?" Sai (Annabi ) ya ce, "Ku ba ni labari da a ce ya sanya (gaɓar) tasa a cikin haram, shin yana da zunubi? To haka nan in ya sanya ta a halal zai zama yana da lada. Muslim (#1006).

ARBA'UNA HADITH (24) HADISI NA ASHIRIN DA HUDU

An karɓo daga Abu Zarri Algifari (R.A) daga Annabi (), cikin abin da (Annabi) ke rawaitowa daga wurin Ubangijinsa. Lallai Allah Maɗaukakin sarki ya ce, "Ya ku bayina! Na haramta wa kaina zalunci, kuma na sanya zalunci ya zama abin haramtawa a tsakaninku. Ya ku bayina! Dukkaninku ɓatattu ne, sai fa wanda na shiryar da shi, ku nemi shiryarwata, ni kuma in shiryar da ku. Ya ku bayina! Dukkaninku mayunwata ne, sai wanda na ciyar da shi, don haka ku nemi ciyarwata, ni kuma zan ciyar da ku. Ya ku bayina! Kowannenku tsirara yake ba tufafi, sai wanda na suturta, ku nemi suturata, zan suturtar da ku. Ya ku bayina! Kuna yin laifi dare da rana, ni kuma ina gafarta zunubai gaba ɗayansu, ku nemi gafarata, ni kuma zan yi muku gafara ɗin nan. Ya ku bayina! Ba ku i'sa ku cutar da ni ba, ballantana ku ce za ku cutar da ni, ba ku isa ku amfanar da ni ba, ballantana ku ce za ku amfanar da ni. Ya ku bayina! Da a ce na farkonku da na ƙarshenku, da mutanenku da aljanunku, ku kasance a bisa ga zuciyar wani mutum ɗaya cikinku mafi jin tsoron Allah, hakan ba zai kara komai a cikin mulkina ba. Ya ku bayina! Da a ce na farkonku da na ƙarshenku, da mutanenku da aljanunku, ku kasance a bisa ga zuciyar mutum ɗaya mafi fajirci, hakan ba zai rage komai dangane da mulkina ba. Ya ku bayina! Da a ce na farkonku da na

ARBA'UNA HADITH (23) HADISI NA ASHIRIN DA UKU

An karɓo daga Abu Malik, Haris bin Asim Al ash’ariy ya ce, Manzon Allah () ya ce, "Tsarki rabin imani ne, faɗin Subhanallahi Walhamdulillahi; tana cika mizani, faɗin Subhanallahi da Alhamdulillahi; suna cika, ko (kowace ɗaya daga cikinsu) tana cika abin da ke tsakanin sama da ƙasa; sallah haske ce; sadaƙa huija ce; haƙuri kuma haske ne; Alƙur'ani hujja ne gare ka, ko a kanka. Dukkan mutane suna jijjifi da safe, daga cikinsu akwai mai zuwa sayar da kansa, ko dai ya 'yantar da kansa ko kuma ya halakar da kansa." Muslim (#223) ya rawaito.“

SHARHI

Da Manzon Allah () ya ce, "Tsarki rabin imani ne...." magana mafi inganci dangane da 'tsarki', shi ne abin da

ARBA'UNA HADITH (22) HADISI NA ASHIRIN DA BIYU

An karɓ0 daga Abu Abdullahi, Jabir ɗan Abdullahi Al ansariy (R.A) ya ce, "Wani mutum ya tambayi Annabi () ya ce da shi, "Ba ni labari idan na sallaci salloli na wajibi, na azumci watan Ramadan, na halatta halal, na kuma haramta haram, ban ƙara komai a kan haka ba, shin kuwa zan shiga Aljanna?" Sai Annabi () ya ce, "Eh! (za ka shiga aljanna).") Muslim (#15).

SHARHI

Abin da wannan hadisi yake nunawa, shi ne, idan mutum zai tsaya a kanwajibi kaɗai, ba tare da ya yi mustahabbi ko ɗaya a rayuwarsa ba, in dai ya sauke dukkan wajiban da ake

KITABUT-TAUHID (Babi Na Goma Sha Biyar15)

  SHARHI Babukan da suka wuce sun yi magana a kan yana daga dangin shirka neman taimako wajen wanin Allah. Wannan babi kuma zai nuna maka ...