GABATARWA.



WWW.TAFARKINSUNNAH.BLOGSPOT.COM

WANNAN SHAFI YANA DAUKE DA HADISAN ANNABI(SAW)ACIKIN HARSHEN HAUSA. IDAN ANGA MUNYI KUSKURE ASANAR DA MU.ALLAH YAYI MUNA JAGORA AMEEN!



DAMIN AIKO DA GYARA KO KARIN BAYANI;
{tafarkinsunnah@gmail.com]

Nov 24, 2011

ARBA'UNA HAADITH (46) HADISI NA ARBA'IN DA SHIDA


An karɓo daga ɗan Abu Burda, daga babansa, daga Abu Musal Ash’ariy (R.A) ya ce, Annabi (ﷺ),  ya tura shi ƙasar Yemen, sai ya tambaye shi dangane da wani abin sha da ake yi a can, sai ya ce, “Menene abin?” Sai ya ce,“Albit’u da Almizru.” sai aka ce da Abu Burda, “Menene Albit’u?” sai ya ce,
wani tsimi ne da ake yi da zuma, almizru kuwa wani tsimi ne da ake yi da alkama. Sai Annabi (ﷺ),  ya ce, “Duk abu mai sa maye haramun ne.” Bukhari ne rawaito shi (#4343).

SHARHI;


Da manzon Allah (ﷺ),  ya ce, “Duk abu mai sa maye haramun ne….” sai malamai suka ce abin da yake sa maye abu biyu ne: Awai abin da yake sa maye, ya kuma sa ka walwala da jin daɗi. Giya tana sa maye, tana sa walwala da jin daɗi, wani farin cikin na babu-gaira-babu-dalili. To wannan giya kenan, ittifaƙin haramun ne. Amma akwai abin da zai sa ka
maye ba walwala, suka ce wannan bai zama haramun ba. Idan za ayi wa mutum aiki a asibiti, likitoci ai suna ɗirka masa allura, ya ji bai san ida yake ba. A wannan lokacin ai ba shi da hankali! Duk dangi an yarda bai san inda yake ba, shi ma haka bai san yadda yake ciki ba, amma bambancinsa da ɗan giya, ɗan giya sha da gwangwajewa da yake yi, shi kuwa ba ya cikin jin daɗi, yana cikin wahala. Akwai mgabatan da suke cewa duk abin da yake sa maye, ko yasa walwala, ko bai sa walwala ba, shi ma haramun ne. Waɗansu suna da wannan fatawar cikin manyan malamai da suka gabata, cikin sahabbai da tabi’ai da tabi’ut tabi’in. A gaskiyar al’amari duk abin da zai sa maye ɗin nan, wato na tilas ba na jin daɗi ba, ya ɗauke maka hankali, to wannan ba giya ba ne, waɗanda suka haramta shi, galibi suna cewa ba ma so mu buɗe ƙofa, in muka buɗe ƙofa ɗin sai mutum ya sa a kawo masa barasa ya sha. To wannan shi ya sa suke haramtawa.

(FASSARA DA SHARHI DA GA BAKIN GARIGAYI SHEIK JA’AFAR MAHAMUD ADAM {R} ).

No comments:

Post a Comment

KITABUT-TAUHID (Babi Na Goma Sha Biyar15)

  SHARHI Babukan da suka wuce sun yi magana a kan yana daga dangin shirka neman taimako wajen wanin Allah. Wannan babi kuma zai nuna maka ...