An karɓo
daga Abu Hurairata (R.A) ya ce, "Manzon Allah (ﷺ)
ya ce, "Dukkan gaɓɓai
na mutane akwai sadaƙa a ciki,
kowanne yini da rana ke hudowa cikinsa, da za ka sasanta tsakanin mutane biyu,
da ke rigima da juna sadaƙa ne, ka taimaki
mutum game da dabbarsa, ka ɗora
shi a kai, ko ka ɗauki
kayansa ka ɗora masa a kan
dabbar, sadaƙa ne; kalma daddaɗa sadaƙa
ce; dukkan taku da za ka yi tattaki zuwa sallah, sadaƙa
ne; ɗauke wani abu mai
cutarwa daga kan hanya sadaƙa
ne." Bukhari (#2989) da Muslim (#1009) suka rawaito shi!”
SHARHI
Wannan hadisi yana cewa, dukkan gaɓɓai, wato dukkan wata, mahaɗa ta ƙashi,
kamar gwiwa, wuyan hannu, ƙafa,
da dai sauransu, akwai sadaƙar
da mutum zai yi da ita. Haka kowanne yini, wanda a cikinsa da za ka sasanta
tsakanin mutane biyu, ka yi adalci tsakanin mutane biyu da ke rigima da juna,
sadaƙa
ne. Ka wayi gari wane da wane suna rigima, wance ta yi yaji, ka sasanta su ita
da mijinta, to wannan za a ba ka ladan ka yi sadaƙa.
Haka idan ka taimaki mutum game da dabbarsa; dattijo ne ba zai iya hawa kan
dabbarsa ba, sai ka ɗora
shi a kai; ko ka zo wata tasha, sai ka ga wani dattijo zai hau mota da nauyin
jiki, ka kama ka ɗora
shi kan motar nan, ko dukkan wani abin hawa; ko ka ɗauki kayansa ka ɗora
masa a kan dabbar don shi ba zai iya yi ba, ko ka kama masa, ka taimaka kuka ɗora tare, to duk dai wannan sadaƙa
ce. A wani hadisin sahabbai suke tambayar me za mu yi, ba mu da dukiyar da za
mu yi sadaƙa, sai Annabi (ﷺ)
ya ce, "Ku yi tasbihi, ku yi hailala, in ba ku samu damar wannan ba, ku yi
umami da kyakkyawan aiki, ku yi hani da mummuna, in ba ku sami damar wannan ba,
ku faɗi daddaɗar kalma ga 'yan uwanku musulmi sadaƙa
ne." Sai ya ce, in duk kun kasa yin wannan, "Ka kame bakinka kar ka
faɗi Sharri."
No comments:
Post a Comment