An karɓo
daga Abu Najih, shi ne Irbadu ɗan
Sariya (RA) ya ce, "Manzon Allah (ﷺ)
ya yi mana wa'azi, wa'azi mai isarwa, zukata suka tsorata, ldanu suka zubar da
hawaye. Sai muka ce da shi, "Ya Manzon Allah (ﷺ)!
Kamar wa'azin mai ban kwana? To ka yi mana wasici." Sai ya ce, "Ina
muku wasici da jin tsoron Allah, da kuma ji da bi, ko da bawa ne ya zama
shugaba a gare ku. Lallai wanda ya rayu a cikinku, da sannu zai ga saɓani mai yawa. Na umarce ku, ku riƙe
sunnata, da sunnonin halifofi shiryayyu, ku riƙe
ta da hakoranku (fiƙa), ku kiyayi
fararrun al'amura, domin kowace bidi'a ɓata
ce. Abu Dawud (#4607) da Tirmizi (#2676) suka rawaito shi, Tirmizi ya ce,
wannan hadisi ne mai kyau, ingantacce."
SHARHI
Annabi (ﷺ)
ya kasance yakan yi wa sahabbai wa'azi daga lokaci zuwa lokaci, idan hakan ta
kama. A wata ruwayar ta hadisin, aka nuna wannan wa'azi Annabi (ﷺ)
ya yi musu shi ne bayan sallar Asuba. An kammala sallar sai ya yi wa'azi. Wani
lokacin idan ya so ya yi musu wannan wa'azin, yakan hau kan mimbarin juma'a ya
faɗakar da su, don a nuna
maka ba wai sai juma‘a ne kawai ake hawa mumbarin juma'a ba. Duk lokacin da buƙata
ta kama, za ka faɗakar
da al'umma, ka hau mumbari, ka yi Innal Hamda Lillahi ɗinka ya yi. lradu ɗan
Sariya ya ce, "Manzon Allah (ﷺ)
ya yi mana wa'azi mai isarwa, zukata suka tsorata, idanu suka zubar da
hawaye...." a sakamakon wannan wa'azin. Wato wa‘azi mai tasiri kenan,
wanda yake ratsa zuciya, ya sa suna kukan zuci, suna kukan idanu. Sai sahabbai
suka ce, "Ya Manzon Allah (ﷺ)!...."
wannan wa'azin da kake mana, "....Kamar wa'azin mai ban kwana?" ba mu
labari idan Allah zai karbi rayuwarka ne. Wato sun ji wa'azin ya ratsa su, sun
ji kamar kalma ce ta mai bankwana, don haka sai suka ce, "....To ka yi
mana wasici....“ sai ya ce, "Ina muku wasici da jin tsoron Allah..."
tsoron Allah kuwa, shi ne kiyaye dokokin Allah Ta'ala, kuma ina yi muku umarni
da ji da bi, ku ji, ku bi, "....ko da bawa ne ya zama shugaba a gare
ku...." lallai ku ji abin da ya faɗa,
ku yi biyayya dangane da umaminsa, matuƙar
bai saɓa wa Allah da Manzon
Allah (ﷺ)
ba. Wannan tsari kenan na shugabantar al'umma, lokacin da duk ƙasa
aka ce ga wani mutum an sa shi ya zama shugaba ga al'umma a musulunci, wajibi
ne al'umma su yi masa ɗa'a,
sai fa idan ya yi umarni da sabon Allah ne, to sai su ƙyale
shi, ba za su bi shi ba a cikin abin da ya yi umami da shi na saɓon Allah. Haka ma idan ya yi umami da sabon Manzon
Allah(ﷺ)
, sai a kyale shi.
Halifofin
Annabi su ne, Abubakar Assiddiƙ da
Umar bin Khaddab da Usman bin Affan da kuma Aliyu bin Abi-Ɗalib.
Waɗannan su ne halifofin
Annabi (ﷺ)!
Duk mulkin da ya biyo bayan wannan, sunansa mulki, ba a kiransa halifanci, don
su halifofi, halifantar Annabi (ﷺ)
suke yi. Idan ka lissafa shekarun da suka yi gaba ɗayansu,
za ka ga shekaru talatin suka yi, to waɗannan
shekaru talatin ɗin
Annabi (ﷺ)
ya ce, shi ne lokacin halinfantar Annabta. Daga baya kuma sai Allah ya mayar da
abin da ya zama mulki ga wanda ya ga dama. A tarihance sai aka samu waɗannan
halifofmin guda huɗu,
su suka mamaye shekaun. Wadansu malamai suka ce a'a! waɗannan
sahabbai guda huɗu
sun mamaye shekaru ashirin da tara ne da wata shida k wata takwas, Alhasan bin
Aliyu, bayan Aliyu ya yi shahada, shi ya zama halifa, shi kuma ya yi wata shida
ne ki wata huɗu
cikon waɗannan shekaru talatin ɗin,
da ya ga rigima ta yi yawa, sai ya sauka daga kan shugabancin ya bar wa
Mu‘awiya, ya ce masa ya je ya riƙe
don a zauna lafiya. Saboda haka idan aka haɗa
waɗannan watanni da Hasan bin
Aliyu ya yi, wata shida ko huɗu
ne, za ka samu shekaru talatin kenan shi ma ya zamanto cikin halifofin Annabi (ﷺ),
amma wannan wata magana ce cikin maganganun malamai. Wannan hadisin yana daga
cikin hadisan da suke nuna wajabcin bin sunnar Annabi (ﷺ).
Sai dai mai tambaya zai iya cewa shin akwai bambanci tsakanin sunnar Annabi (ﷺ)
da kuma sunnar halifofi masu shiryarwa, ko duk ɗaya
ne? Abin da ake nufi, waɗannan
sahabbai guda huɗu,
idan kansu ya haɗu a
kan mas'ala ta addini, to ba za ka ga sun saɓa
wa abin da Alƙur'ani ko hadisin Annabi (ﷺ)
suka zo da shi ba, shi ya sa aka ce a bi sunnarsu bayan ta Annabi (ﷺ).
To amma idan Abubukar ne (R.A) ya ba da fatawa, ko Usman (R.A) ko Aliyu (R.A)
kaɗai ya ba da fatawa, wannan
dole ne sai an gwada, idan ta dace da Alƙur'ani
da hadisi to shi kenan, amma idan kansu ya haɗu a
kan wata mas'ala, to da wuya ka ga sun saɓa
wa nassin Annabi (ﷺ).
No comments:
Post a Comment