An karɓo
daga Abu Hurairata (R.A) daga Annabi (ﷺ)
ya ce, "Wanda duk ya kautar wa da mumini wani baƙin
ciki, daga baƙin cikin duniya, to
Allah zai kautar masa da wani baƙin
ciki daga cikin irin baƙin cikin ƙiyama,
duk wanda ya kawo sauƙi ga wanda yake
cikin tsanani, Allah zai kawo masa sauƙi
a duniya da lahira, wanda ya suturce musulmi, to Allah zai yi masa sutura a
duniya da lahira. Lallai Allah yana cikin taimakon bawa matuƙar
bawan ya kasance mai taimakon ɗan
uwansa musulmi. Wanda duk ya kama wani tafarki yana neman ilimi a wannan
tafarkin, Allah zai sauƙaƙa
masa hanyar shiga aljanna. Babu wasu mutane da za su taru a cikin wani ɗaki cikin ɗakunan
Allah, suna karanta littafin Allah, suna darasinsa a tsakaninsu da juna, face
sai nutsuwa ta sauka a kansu, rahama ta lullube su, (Mala'iku sun kewaye su),
sai kuma Allah ya ambacesu a fadarsa. Wanda duk aikinsa ya yi sanɗa da shi, to dangantakarsa ba za ta yi gaggawa da
shi ba." Muslim ne ya rawaito shi (#2699) da Wannan lafazi.
SHARHI
Manzon Allah (ﷺ)
ya ce, "Wanda duk ya kautar wa mumini Wani baƙin
ciki...." daga dangin wani baƙin
ciki da ke iya samun mutum a nan duniya, "....to Allah zai kautar masa da
wani baƙin
ciki...." daga cikin irin baƙin
cikin da kan iya riskar bawa a gobe ƙiyama.
Misali wani mutum mumini yana fama da matsala ta rayuwa, sai ka taimaka masa,
ka yaye masa wannan baƙin cikin: An
rubuto masa magani a asibiti, ba shi da kuɗin
da zai saya, sai ka je ka sayo ka ba shi: An ba shi notis a gidan haya, sai ka
zo ka ba shi kuɗin
da ake bin sa, Ko aka sallame shi daga gidan haya, sai ka zo ka ba shi kuɗin da ake bin sa, ka ƙara
masa kuɗin hayar na wata huɗu a kai, masu zuwa. Duk wanda ya yi wannan, Allah
zai yaye masa wani baƙin ciki daga
cikin dangin baƙin ciki da ke
iya samun mutum a ranar tashin ƙiyama.
Sai a can lahira, ba a nan zai yaye masa ba, a can zai yaye masa, a inda ba mai
yayewa, sai shi (Allah). Sannan Manzon Allah (ﷺ)
ya sake cewa, "....duk wanda ya kawo sauƙi...."
ga duk mutumin da yake cikin tsanani, "....Allah zai kawo masa sauƙi
a duniya da lahira...." Misali, mutum ne yake cikin wani tsanani, sai ka
ba shi sauƙi: Kamar mutum ne ana
bin sa bashi, sai ka taimaka masa ya biya. Ka ga cikin tsanani kenan yake, kai
kuma sai ka taimaka masa. Ko kuma lokacin biya ya yi, babu abin biya, sai ka ƙara
masa lokaci, ka ce bari sai wata na gaba in ya yi, ka biya, ko wata biyu masu
zuwa, ko wata uku masu zuwa. Domin ba a cewa bari sai lokacin da ka samu ka
kawo, ba a yin wannan, dole sai an ƙayyade
lokaci. Sai dai in ya kasa, sai a ƙara
masa wani lokacin, ba a yin bashi da cewa in ka samu ka kawo, Allah yana cewa,
(Idan (mutum) yana cikin tsanani, to a yi masa
jinkiri zuwa lokacin da ya samu, wanda kuwa ya yafe, to wannan shi ya fi
alheri). [Al Baƙara: 280]. Faɗin Manzon Allah (ﷺ)
cewa, "....wanda duk ya kama wani tafarki yana neman ilimi a wannan
tafarkin, Allah zai sauƙaƙa
masa hanyar shiga aljanna...." wannan yana nuna falalar neman ilimi kenan.
Duk wanda ya kama hanyar neman ilimi, to sai Allah ya sauƙaƙa
masa shiga aljanna, ta cikin ruwan sanyi, ba wahala. Duk wanda ya tsaya a
jahilci kuwa, to sai an rufe masa ƙofar
gidan aljanna. A nan ba ya nufin sai ka zamanto tun da safe zuwa dare kana
neman ilimi, alal-aƙalli ka taso
daga ƙarfe
biyar, ka je ka koyi Alƙur'ani, ka je ka
koyi hadisan Annabi (ﷺ), ko ka ɗauki Ahalari, ka je ka koya, ba ƙaramin
alheri ba ne. Kada ka ce kai ka yi girma da koyon karatu, wannan ita ce
hanyarka ta shiga aljanna.
A ƙarshen
hadisin, Manzon Allah (ﷺ) ya ce,
"....Wanda duk aikinsa ya yi sanɗa
da shi, to dangantakarsa ba za ta yi gaggawa da shi ba." a ranar tashin Alƙiyama.
Abin nufi, a nan gidan duniya za a ce, wane ɗan
wane ne za a yi masa alfanna, a lahira babu alfarma, sai dai wa ya zo da imani
da aiki nagari! Ba mai tsira, sai wanda yake ya je wa Allah da imani da aiki
nagari. wannan shi ake buƙata! Don haka
duk dangantakar mutum, ba za ta ƙara
masa komai ba. Shi ya sa Annabi (ﷺ)
yake cewa, "Ku 'ya'yan Banu Abdulmuɗɗalib!
Ku tsamar da kanku daga wuta, domin ba zan amfana muku komai ba. Ku 'ya’yan
Banu Hashim! Ku tsamar da kanku daga wuta. Ya Faɗimatu
bintu Muhammad! Tambaye ni abin da kike so a cikin dukiyata, ba zan iya wadatar
miki da komai ba ranar alƙiyama. [Duba:
Sahih Al Bukhari (#2753) Sahih Muslim (#204)]. Don haka dangantaka ba ta amfani
a gidan lahira, sai in ka yi aiki na-gari. In ka ga dangantaka ta yi amfani, to
an shiga aljanna. Idan ɗa
da iyayensa sun shiga aljanna, wani yana benen sama, kamar uba yana sama, yaro
na benen ƙasa, sai a ce bari a daɗaɗa
wa ubannin, sai a tura ɗan
ya je wajen ubansa, duk da ɗan
bai yi aikin da zai je gurin da uban yake ba. Allah ya ce,
(Waɗanda
suka yi imani, kuma zuciyarsu ta bi su a kan (imanin) mun riskar da su tare da
su). [Aɗɗur: 21] Amma in uba
yana cikin aljanna, ɗa
ya yi aikin da za a kai shi wuta, to ba a fito da shi daga wuta don mahaifinsa,
matuƙar
ya
mutu yana kafurci, zai dawwama a wuta, mahaifinsa ba
zai iya tsamo shi ba.
No comments:
Post a Comment