An karɓo daga Anas ɗan Malik (R.A)
ya ce, “Na ji Manzon Allah (ﷺ), yana
cewa, Allah Maɗaukakin Sarki yana cewa, “Ya kai ɗan Adam! Lallai ba za ka bauta
min ba, kuma ka sanya rai game da rahamata ba, face sai na gafarta maka ban
damu ba. Ya kai ɗan Adam! Da a ce zunubanka zasu cika sashen sama gaba ɗaya,
sannan ka nemi gafarata, sai in gafarta maka. Ya kai ɗan Adam!
Da a ce zaka zo min da cikin ƙasa
gaba ɗaya zunubai ne, sannan ka gamu dani, ba tare da ka haɗa ni da kowa ba, Ni
kuma zan kawo maka gafara, cikin ƙasa.” Tirmizi ne ya rawaito shi (#3540)
ya ce, hadisi ne mai kyau, ingantacce.
SHARHI;
Wannan hadisi yana nuna falalar
tauhidi ta yadda idan mutum ya mutu ba ya shirka Allah yana gafarta masa
zunubansa amma wanann ba ga kowa bane, sai wanda Allah ya ga damar ya
gafartawa.
(FASSARA DA SHARHI DA GA BAKIN GARIGAYI SHEIK
JA’AFAR MAHAMUD ADAM {R} ).
Jazakumullah
ReplyDelete