An karɓo
daga Abu Zarril Al Gifari (R.A) ya ce, "Waɗansu
mutane daga cikin sahabban Annabi (ﷺ)sun
ce da shi, "Ya Manzon Allah (ﷺ)!
Ma'abota dukiya sun tafi da lada, suna yin sallar (farilla) kamar yadda muke
yi, suna yin azumin (farilla) kamar yadda muke yi, amma kuma suna sadaƙa
da sauran dukiyarsu. Sai Annabi (ﷺ)
ya ce, "Shin Allah bai riga ya ba ku abin da za ku yi sadaƙa
da shi ba ne? Dukkan tasbihi sadaƙa
ne, dukkan wata kabbara sadaƙa
ce, dukkan wata hamdala sadaƙa
ce, dukkan wata hailala sadaƙa
ce, umarni da kyakkyawan aiki sadaƙa
ne, hana mummunan aiki sadaƙa
ne, a gaɓar kowanne daga cikinku
akwai sadaƙa"sai sahabbai
suka ce "Ya Manzon Allah! Yanzu mutum zai biya buƙatarsa
kuma ya zama yana da lada?" Sai (Annabi ﷺ)
ya ce, "Ku ba ni labari da a ce ya sanya (gaɓar)
tasa a cikin haram, shin yana da zunubi? To haka nan in ya sanya ta a halal zai
zama yana da lada. Muslim (#1006).
SHARI
Abin nufi, " ...amma kuma suna sadaƙa
da sauran dukiyarsu" wanda mu kuma ba mu da kuɗin da za mu yi sadaƙa,
saboda haka mu ma a ba mu abin da za mu yi mu sami lada. Ma'ana, shi yana ganin
an yi sallah tare, an yi azumi tare, to an zo sadaƙa
su kuma ba su da ko kobon da za su yi sadaƙa,
sai suke kishin don me wane zai yi sadaƙa,
mu ba mu samu damar yin hakan ba? Ina ma mu ma, mu samu halin da za mu yi sadaƙa?
Halin ya sha bamban, tsakanin masu kuɗinmu
da talakawanmu da kuma na sahabbai, masu kuɗin
sahabbai kullum so suke su yi alheri. Lokacin da ayar da Allah yake cewa,
(Ba za ku samu albirru ba ( wanda shi ne shiga
aljanna ) har sai kun ciyar daga mafi kyan abin da kuke so). [Ali-Imran: 92]
Sai Abu Dalha ya ce, "To ni dai ba abin da nake ƙauna
cikin dukiyata irin makekiyar gonata da ake kira Biruhai. Wata gona ce a
Madina, wadda saboda daɗin
ruwanta Annabi (ﷺ) yana shiga ciki ya
huta, ya ɗebi ruwanta ma
ya sha. Abu Ɗalha ya ce, "Ba ni
da abin da ya fi komai tsada irin wannan gonar, ga shi an ce ba a samun
aljannah sai an ciyar daga abin da ake ƙauna,
to ga ta nan wurinka, ka raba ta yadda Ubangiji ya umarce ka." [Bukhari
(#1461) da Muslim ne suka rawaito wanna ƙissar].
Wato dai sai da ya duba abin da ya fi komai tsada sannan ya bayar. Su kuma
talakawansu, sun nemi samun irin wannan ne, ba don su kece raini ba, ko su fi
su sa'a, a'a! sai don su ciyar saboda Allah. Don haka suka zo wajen Annabi (ﷺ)
suka ce masa "Ma'abota dukiya sun tafi da lada...." sallah mun yi
tare, azumi mun yi tare, amma sadaƙa
kuma sun fi mu, tunda mu ba mu da abin da za mu yi sadaƙa."Sai
Annabi (ﷺ)
ya ce da su, "Shin Allah bai riga ya ba ku abin da za ku yi sadaƙa
da shi ba ne?" Ai Allah ya riga ya ba ku, "Dukkan tasbihi...."
subahallahi da za ku faɗa,
kamar ku ɗauki sadaƙar
dukiya ne kun bayar da hannunku. Haka, "....dukkan wata kabbara...."
da za ku ce, Allahu Akbar; kamar kun ɗauki
sadaƙa
ne kun bayar.
Akwai riwayar hadisin da ta zo sama da haka, da ta
faɗi abin da aka faɗaa musu, tasbihi da hailala da kabbara, suka je suka
yi ta yi, su ma masu kuɗin
da suka ga haka, suka rinƙa yin tasbihin
da hailalar duk gaba ɗaya.
Sai suka dawo suka ce, abin da ka faɗa
mana, su ma sun ji sun ci gaba da yi, sai Annabi (ﷺ)
ya ce, "Ku haƙura, ai falalar
Allah ce yake ba da ita ga wanda ya ga dama, ku haƙura.“
To da aka faɗa musu haka,
suka ga ba yadda za su yi, kamar yadda hadisi na cikin Bukhari [#1416 da Muslim
#1018] ya nuna, sai waɗansu
daga cikinsu suke zuwa suna yin dako a kasuwa, ba don talauci ba, sai don su
tara abin da zai isa su fitar da zakka, ya zamanto su ma sun taɓa yin zakka kafin su mutu. Sai su yi dako, su yi
noma, su yi fatauci, so suke dai wai ya zamanto cikin rukunan musulunci,
kowanne sun taɓa yi. To su
sahabbai dako suka rikayi don sutara kudin da zasu fitar da zakka.
muna godiya, amma don Allah arinka yin rubutu dakyau, yadda zaibada ma'ana me kyau
ReplyDeleteMasha Allah mungode
ReplyDelete