An karɓo
daga Nawas ɗan Sam'an (R.A)
ya ce, Manzon Allah (ﷺ) ya ce, "Aikin ɗa'a shi ne kyawawan dabi'u, laifi shi ne abin da ya
yi kai kawo a zuciyarka, kuma ba ka so mutane su ga kana yin wannan abin."
Muslim (#2553) ya rawaito.
An karɓo
daga Wabisa (R.A) ya ce, "Na zo wurin Annabi (ﷺ),
sai ya ce, "Ka zo ne kana tambaya dangane da ɗa'a?" Sai na ce, "Na‘am!" Sai ya ce,
"Ka yi wa zuciyarka fatawa,
aikin ɗa'a
shi ne abin da zuciya ta nutsu da shi, amma aikin saɓo kuwa shi ne duk abin da ya yi kai kawo a cikin
zuciyarka, ko da mutane za su ba ka fatawa." Hadisi ne mai kyau, mun
rawaice shi daga littafin Musnad na Imamu Ahmad (J4/Sh 227) da Musnad na Imam
Addarimi (12/ sh 246) da sanadi mai”
SHARHI
Aikin
ɗa'a shi ne kyawawan ɗabi'u,
kamar hakuri, aikin laifi kuma, shi ne abin da ya yi kai-kawo a cikin
zuciyarka. Abin da kai kanka lokacin da kake yi, ba ka nutsu ba da aiwatar da
shi, kuma ka ƙi, ba ka so ma mutane su ga
kana yin wannan abun, wannan shi ne shubuha. Domin da a ce aikin laifi ne ƙarara
akwai nassi a kansa, ai ba ka jiran ka yi kokwanto, nassi kawai ya wadatar.
Amma abin da yake nassi bai zo ba ƙarara
a kai, to kai kawon da za ka yi a cikin zuciya na nuna wannan abin laifi ne. Da
aka ce, “....ba ka son mutane su ga kana yi....” ba wai ana nufin dukkan mutane
ba, ana nufin masu ilimi da addini. Duk wanda ka san mai addini ne, mai ilimi,
ba ka son ya ji wani abu a fili da kake yi, ba ka son ya gan ka, to wannan abun
laifi ne.
Shukran
ReplyDeleteALLAH Yasa ka da Al-kairai
ReplyDelete