An karɓo daga Abdullahi ɗan Umar
(R.A) ya ce, Manzon Allah (ﷺ), ya dafa
kafaɗata ya ce, “Ka kasance a duniya tamkar kai baƙo ne, ko kuma wanda yake kan
hanya.” Ɗan Umar (R.A) yana cewa, “Idan ka kai yamma, kar ka yi jiran safiya,
idan kuma ka wayi gari, to kar ka jira yamma. Ka riƙi aiki alheri lokacin
lafiyarka, saboda lokain rashin lafiyarka. Ka riƙi aiki alheri lokacin
rayuwarka, saboda ka
SHRHI;
Manzon Allah (ﷺ), ya ce, “Ka kasance a gidan duniya tamkar baƙo
ne…”
wanda yazo balaguro, yana sa ran komawa, kar ka baje kayanka na koli, ko
kuma ka kasance tamkar, “….wanda yake kan hanya….” ba ka riga ka sauka ba. Ibnu
Umar (RA) yana cewa, “Idan ka kai yamma, kar kayi jiran safiya….” Ma’ana in ka
kai yini da ranka, aka zo aka maka tallar aikin alheri, kana ikon yi, kar ka
jinkirta shi, ka ce bari in bari sai gobe, ba ka da tabbacin kaiwa goben. “Haka
nan, “….Idan kuma ka wayi gari, to kar ka jira yamma….” Abin nufi, sai ga wani
aikin alheri ya bijiro, kada shaiɗan ya zo ya ce, “A’a! Bari sai da yamma na
yi.” ka aiwatar dashi a wannan lokacin, don ba kai kake da yammar ba. Don
lokacin ɗan Adam guda uku ne: wanda ya wuce, wanda kake ciki yanzu, da wanda zai
zo nan gaba. Wanda ya wuce, ya wuce, ba zai taɓa dawowa ba; wanda kake ciki
yanzu, shine naka; wanda zaizo nan gaba, gaibu ne, ba ka san me zai zo da shi
ba, zai zo kana lafiya ko baka da lafiya, zai zo kana da rai, kana da hali, ko
baka da hali, ba san me zaka samu kanka ciki ba.Wannan lokacin da kake ciki,
shi ne tabbas.
Cewar, “…Ka riƙi aikin alheri
lokacin lafiyarka…” yana nufin don ka amfana da shi, in rashin lafiya ya kama
ka. Saboda idan mutum ya saba yana yin aikin alheri lokacin lafiyarsa, idan rashin
lafiya ta zo, ba zai yi asarar niyyar nan tasa ba, za a riƙa bashi lada, tunda
dai bai sami damar yi ba. Wannan duk ana nuna wa mutum lokacin ribatar
al’amari, ƙoƙarin ribatar lokaci. Malamai suna cewa idan Annabi(ﷺ), ya fuskantar da magana zuwa ga wani daga cikin
al’ummarsa, wannan mutum bashi kaɗai abin ya shafa ba, ya shafi kowanne
musulmi, mace ko namiji, har zuwa alkiyama ta tashi. Don haka kar ka ce ai
wannan ya nuna cewa ana iya yi wa mutum daya magana, amma ana nufin kowa da
Abdullahi ɗan Umar (RA) kaɗai ake, mu nan gurin ba da mu ake ba. Wannan ya nuna
cewa ana iya yi wa mutum Magana, amma ana nufin kowa da kowa. Sannan hadisin
yana nuna mutum ya yi tanadi, saboda zuwam mutuwa, don gidan duniya ba gida ne
na wanzuwa ba, in ma ka yi nufin ka wanzu ko ka daɗe a ciki, ba yadda za a yi
ka dawwama.
(FASSARA
DA SHARHI DA GA BAKIN GARIGAYI SHEIK JA’AFAR MAHAMUD ADAM {R} ).
No comments:
Post a Comment