An karɓo
daga Abu Sa'id Alƙhuduriy (R.A) ya
ce, “Na ji Manzon Allah (ﷺ) yana cewa, "Duk
wanda ya ga abin ƙi, to ya gusar
da shi da hannunsa, in ba shi da iko, ya gusar da shi da harshensa, in ba shi
da iko, to ya ƙi abin a zuci, wannan
shi ne mafi raunin imani" Muslim ne ya rawaito shi (#49).
SHARHI
Malamai suka ce, wannan hadisi yana cikin nassosin
da ke nuna wajabcin umami da kyakkyawan aiki, da hani ga mummuna. Wannan kuma
shi ne tabbatacce cikin ayoyin
Alƙur'ani
da dama. Don haka wannan hadisi yana bin ayoyin da suke nuna wajabcin cewa, duk
inda aka ga mummunan abu, to a ƙi
shi, duk kuma inda aka ga abu mai kyau, a ja hankalin mutane su bi shi.
Cewa ka gusar da shi .da hannunka ko ka gusar da shi
da harshenka, wannan ba wajibi ba ne a kan ɗaiɗaikun al'umma. A'a! Wajibi ne a kan waɗanda suke da ikon yin hakan a cikin al'umma. Za ka
iya ganin abin ƙi yana faruwa,
kana son ka hana su da harshenka, amma ba ka da dalilai na shari'a da za ka
gamsar da wanda yake aikata wannan Samar a kan ya bari. Ka ga, ba kai ne wanda
wajibin yake kanka ba, sai dai ka yi ƙoƙari
ka sanar da wanda kake ganin zai iya wa'azantar da shi, ya faɗakar da shi, ya ba shi dalili, don ya sanar da shi,
ba kai ba. Kai din idan ka fara, ba za ka iya kaiwa ko'ina ba, saboda ba ka da
dalili, ba ka da abin da za ka gamsar da shi ɗin.
Wajen ture abin ƙi ko ɓarna da hannu kuwa, da ma wannan, sai dai ko a ƙwaryar
gidanka ne, za ka iya hanawa da hannunka. Amma idan ya zo titi, waɗansu suka zo suna sayar da barasa a unguwarku, suka
buɗe shagon sayar da
barasa, ai bazaka taho da sanda ka ture suba, ko kace zaka fasa kwalbar
barasar, ka yi tafiyarka ne. In ka yi haka, sai ka gan ka a police station, ana
cewa sai ka biya kuɗin
giyar da duk ka zubar. Ka ga ai ta ɓaci!
Haka kuma ko da wani lokaci in za ka gusar da ɓarna,
sai ka ga menene abin da zai biyo baya? In ka san in ka ture ɓarna alheri ne zai biyo baya, to wajibi ne ture
wannan ɓarnar. In kuwa ka san
wannan ɓarnar ba za ka iya ture
ta gaba ɗaya ba, amma dai ka
rage mata ƙarfi, za ka iya ture
kashi ɗaya bisa uku ko
rabinta, wannan ma wajibi ne ka yi ƙoƙarin
ture wannan ɓarnar. Idan ka
san in ka ture ɓarna,
wata ɓarnar ce
makamanciyarta, za ta zo ta cike gurbin wannan, to sai malamai suka yi saɓani, Waɗansu
suka ce ka barta, ta ci gaba da faruwa, waɗansu
suka ce, a'a! kai dai ka ture wannan, waccan ai ba kai ka janyo ta ba. In kuma
ka san, in ka ture ɓarna
wata ɓarnar da ta fi ta girma
ita za ta maye gurbinta, to haramun ne ka ce za ka ture wannan ɓarnar, sai dai ka ƙyale
ta, ta ci gaba da faruwa, ita ƙarama
ce, a maimakon ka je ka ture wannan babbar ɓarna
ta zo. Wannan yana cikin fiƙihun
da malamai suka yi magana a kansa, musamman Ibnul ƙayyim
a cikin littafinsa I’iIamul Muwaƙi’in.
No comments:
Post a Comment