An karɓo
daga Abu Hurairata (R.A) ya ce, Manzon Allah (ﷺ)
ya ce, Allah Ta'ala ya ce, "Duk wanda ya yi gaba da waliyina, to na ba shi
sanarwa ya zo ya yi yaƙi da ni. Bawana
ba zai kusance ni ba, da wani abu da na fi ƙauna,
sama da abin da na wajabta masa. Bawana ba zai gushe ba yana kusanta ta da
nafilfili, har sai na zamanto ina ƙaunarsa,
idan na ƙaunace
shi, sai na kasance jinsa, da yake ji da shi, da ganinsa, da yake gani da shi,
da hannunsa, da yake damƙa da shi, da ƙafarsa,
da yake tafiya da ita. Wallahi, idan ya roƙe
ni, zan ba shi abin da ya roƙa,
kuma wallahi, idan ya nemi tsarina, zan tsare shi." Bukhari ne ya rawaito
shi (#6502).
SHARHI
Abin da ake nufi da waliyin Allah a nan, shi ne duk
wanda yake ƙaunar Manzonsa (ﷺ),
mace ce ko namiji, a da ne, ko a yanzu, in dai mumini ne, mai ƙaunar
Allah, to ya zama
waliyyi.
Wannan hadisi da dama daga cikin 'yan bidi’a sun
ribace shi wajen fassara shi da cewa Ubangiji na iya shiga gangar jikin bawa,
ya zamanto Allah ya cakuɗa
da bawansa Wa’iyazu billahi! Wannan mummunar aƙida
wadda take daga 'yan mishan (kiristoci), sufaye sun ɗauko ta, musammam ma irinsu Hallaj da Ibnu Arabi duk
suna da irin waɗannan
munanan aƙidu a wake ke a rubuce.
In ka tambaye su meye hujjarku, sai su ce, ai Allah ya ce, matukar bawa ya
aikata farilla ya yi nafila, Allah zai zama ganinsa, sai ya zamanto mutum ya
zama shi da Allah sun zama ɗaya
kenan. Haka suka fassara wannan hadisin! Malaman sunna sun fassara wannan
hadisin da cewa, abin da hadisin ke nufi shi ne, Allah zai sa bawa a kan
daidai, zai kasance jinsa; ba zai rinƙa
sauraron komai ba, sai abin da Allah ya yarda da shi, in sun ji ashariya, sai
su toshe kunnensu, in sun ji mummunar magana, sai su toshe kunnansu. Wato Allah
ya tsare su, ta yadda babu yadda za a yi wata Barna, sai Allah ya kare su, ba
sa son ji. Allah ya kasance jinka kenan! Haka Allah zai kare ganinka; ba za ka
kalli komai ba, sai abin da yake na halal, wanda Allah ya yi izini a kalle shi.
Duk abin da yake haramun ne, sai ka ga Allah ya kare ka, ba ka iya kallonsa, da
ka gan shi kiciɓis,
ba tare da niyya ba, sai ka kauda idonka. Haka sai Allah ya zamanto hannunsa da
yake bayar wa ko amsa; zai zamanto ba za ka bayar ba da hannunka, sai abin da
yake halal ne, ba za ka karɓa
ba, sai abin da yake halal, ba ka zubar da jinin wani, ba ka ɗaukar dukiyar wani, ba ka cutar wani. Haka ƙafarsa;
sai ya kasance duk inda za ka taka ka je da ƙafarka,
wajen yi wa Allah da‘a ne, ba wajen saɓa
masa ba ne. Za ka samu wannan ne, idan ka tsayar da farillai daidai, kuma kana
yawan yin nafila. Azumin Ramadan, kana yin sa daidai bisa ga tsarin Annabi (ﷺ),
kana kiyaye ladubban da ke ciki, tun daga sahur har izuwa buɗa baki; kana kuma yin azumin Sitta Shawwal, kana ƙoƙarin
yin azumin Arfa, kana ƙoƙarin
yin azumi uku kowanne wata. Sannan kuma kana ƙoƙarin
yin sallah ta farilla da ta nafila, kana yin shafa'i da wutiri. To in kana
haka, sai ka ga Ubangiji ya azurta ka da irin wannan: Jinka da ganinka da
hannunka da ƙafarka, duk ba za ka
aiwatar da su ba, sai ta hanyar abin da yake da'a ne ga Allah. Wannan shi ne
abin da hadisin yake nufi, ba wai ana nufin Allah ya zama bawa ba. Wannan ba
zai yiwu ba!
Shi ya sa malaman sunnah suka ce, idan ka duba
hadisin, za ka ga ɓangare
biyu ne da shi, akwai wanda ake kusanta, da wanda yake kusanta ɗin; da mai roƙo
da wanda ake roƙo; mai neman
tsari da wanda ake neman tsarin a wurinsa. A cikln hadisin, cewar, "Bawana
ba zai gushe yana kusanta ta....", ka ga nan mai neman kusanci shi ne
bawa, wanda ake neman kusancinsa shi ne Allah; wanda yake bayarwa in an roƙe
shi, shi ne Allah, wanda yake roƙon
shi ne bawa; mai neman tsari shi ne bawa, wanda ake neman tsari a wajensa,
shine Allah. Ka ga wannan ya tabbatar da cewa abubuwa ne guda biyu. To ta yaya
kai ka dunƙule su, suka zama ƙwaya
ɗaya, tun daga farkonsu
har izuwa ƙarshensu, ka ce sun dunƙule
sun zama ɗaya? Wannan ita
ce fassarar da malamai
suke yi wa wannan hadisi.
No comments:
Post a Comment