An karɓo
daga ɗan Abbas (R.A) daga
Manzon Allah (ﷺ) cikin irin abin da ya
rawaito daga Ubangijinsa, ya ce, "Allah ya riga ya rubuta ayyukan alheri
da munanan
ayyuka, wanda duk ya hinmatu zai aikata wani
kyakkyawan aiki, sai bai samu aikatawa ba, Allah zai rubuta masa kyakkyawan
aiki guda ɗaya cikakke.
Idan ya himmatu zai aikata wani kyakkyawan aiki, kuma ya aikata shi, to
Ubangiji zai rubuta masa lada goma, izuwa ninki ɗari
bakwai, zuwa ninkininki da yawa. In ya himmatu zai aikata mummunan aiki, kuma
bai aikata ba, Allah zai rubuta masa kyakkyawan aiki cikakke a wurinsa. Idan ya
himmatu da mummunan aiki, kuma ya aikata shi, Allah zai rubuta masa mummunan
aiki guda ɗaya” Bukhari
(#6491) da Muslim (#131) a cikin sahihan littattafansu.
SHARHI
A cikin wannan hadisi za mu fahimci yalwar rahamar
Allah Ta'ala, ta yadda rahamarsa ta fi azabarsa yalwa, yardarsa ta fi fushinsa.
Kuma wannan hadisi, hadisi ne ƙudusi,
cikin irin abin da Annabi (ﷺ) yake rawaitowa daga
Allah kai-tsaye. Allah Maɗaukakin
Sarki ya ce, "Allah ya riga ya rubuta (dangogin) ayyukan alheri .....
" da kuma dangogin ayyuka na ɓarna
wanda mutune za su yi. Allah ya rubuta da Alƙalaminsa
na ƙudura
cewa, ranar kaza, wane zai yi kaza, rana kaza, wane zai aiwatar da kyakkyawan
aiki. Don haka "....wanda duk ya himmatu ya aikata wani kyakkyawan aiki,
sai bai samu aikatawa ba...." a zuciyarsa ga niyya, niyyar ya riga ya
yanke lallai sai ya yi kaza, sai wani abu ya zo ya hana shi aikatawa, to duk da
bai aikata ba, "....Allah zai rubuta masa kyakkyawan aiki guda ɗaya cikakke...." duk da bai samu damar yi ba,
saboda wannan niyyar tasa."....Idan ya himmatu zai aikata wani kyakkyawan
aiki...." kuma ya sami dama ya aikata aikin,"....to Ubangiji zai
rubuta masa lada...." ɗaiɗai guda goma. Za kuma a iya ninkawa har zuwa ninki ɗari bakwai, har zuwa ninki mai yawa sama da ɗari bakwai. Sannan "....Idan ya himmatu zai
aikata mummunan aiki....” kuma bai sami damar aikatawa ba, "....Allah zai
rubuta masa kyakkyawan aiki cikakke a wurinsa...." Ma'ana mummunan aiki ne
ka zo za ka yi, sai ka tuna wani nassi na hadisin Annabi (ﷺ)
wanda ya haramta wannan abin, ko wani ya faɗakar
da kai, sai ka fasa, wannan fasawar da ka yi, za ta sa a rubuta maka kyakkyawa,
saboda ba ka yi wancan mummunan ba. Amma "....Idan ya himmatu da mummunan
aiki, kuma ya aikata shi, Allah zai rubuta masa mummunan aiki guda ɗaya." Ma'ana, ba za a ninka masa yadda aka
ninka lada ba. Wannan yana nuna yalwar rahamar Ubangiji, saboda Allah ba zai
amfanu da komai ba wajen azabtar da mu.
Wannan hadisi ya kasa mutane kashi huɗu: Na ɗaya,
wanda ya yi niyyar alheri, amma bai samu damar aikatawa ba, za a rubuta masa
lada ɗaya cikakke. Na biyu,
wanda ya yi niyyar yin alheri, ya kuma aikata, za a ninninka masa lada sau
goma, har zuwa sau ɗari
bakwai ko ma sama da haka. Na uku, wanda ya yi niyyar yin mummunan aiki, amma
bai aikata ba, za a rubuta masa lada ɗaya.
Na huɗu, wanda ya yi niyyar
yin mummunan aiki, kuma ya je ya aikata, za a rubuta masa mummuna guda ɗaya. Babu matsala cikin kashi na ɗaya da na biyu da na huɗu, amma wanda ya yi niyyar zai aikata mummuna, kuma
bai aikata ba, sai aka ce za a ba shi lada, to wannan in muka ɗauki wannan a haka, za mu ga wani nassin kuma wanda
yake karantar da wani abu daban dangane da mutanen da suka yi nufin za su
aikata ɓarna a garin Makka.
Annabi (ﷺ)
ya haramta yaƙi a Makka, haka Allah
ma ya haramta wannan a hurumin Makka. Ko ciyawa da ke garin, ba a yarda mutum
ya ƙetare
mata iyaka ba, haka ko tsuntsu ya shiga garin, ba a yarda ka farauce shi ba, ko
dabba ta shiga wurin, ba a yarda ka farauce ta ba, to ballantana ka ce za ka
aikata Wani mummunan aiki na zina ko na caca ko wani abu a wajen, Allah ya ce,
(Wanda duk ya yi nufin ɓarna a cikinsa ( wato garin Makka) za mu ɗanɗana
masa azaba mai tsanani) [Al-Hajj: 25] Nufata kawai mutum ya yi, niyya a zuci
zai aikata mummunan aiki a garin, Allah ya ce, "....za mu ɗanɗana
masa azaba mai tsanani." ’ko da bai aikata ba. To amma wannan, ya keɓanta da Makka, hukunci ne ga wanda yake cikin Makka
kaɗai, amma in a wani
garin ne ka yi nufin aikata wani mummunan aiki, ba ka kuma aikata ba, to za a
ba ka lada, amma a can Makka ka yi niyya, ko ba ka aikata ba, akwai zunubi,
saboda alfarmar wajen.
Ibnu Kasir ya ce, wanda ya zo zai yi mummunan aiki
kashi uku ne: Imma dai ya zamanto ka zo za ka aikata mumunan aikin, amma ba ka
aikata ba, saboda wa'azi, ko ka tuna wata aya, ko wani hadisi, sai ba ka aikata
ba. To wannan shi ne za a ba ka kyakkyawa guda ɗaya.
Ko kuma ya zamanto ka himmatu, ka tafi wani wuri za ka yi ɓarna, da ka tafi a hanya, sai wani abu ya bijiro
maka, ko wani ya tsare ka da hira, sai ka manta abin da ya fito da kai daga
gida, sai ka dawo gida, wannan ba ka da lada, ba ka da zunubi. Ko kuma ka
himmatu lallai sai ka aikata mummunan aiki, amma sai aka fi ƙarfinka,
ka tarar da wani ɗan
ta'adda ya fi ka ta‘addanci, abin da za ka yi na wannan saɓon ya hana ka, to wannan duk da ba ka sami damar yi
ba, amma da niyya: nan, sai an ba ka zunubi, saboda ba tsoron Allah ne ya sa ka
janye ba, abubuwa ne suka fi ƙarfinka.
Guda uku aka kasa su, kuma haka suke.
Dangane da wannan nufi na zuci, Ibnul ƙayyim
ya ce matakai ne guda huɗu,
kamar yadda ya kawo a littafinsa Ɗariƙul
Hijrataini. Imma abu ya zo ta fuskar umani, Shaiɗan
ya jefo maka tunanin yaya zan yi kaza, ya kawo maka tunanin aikin, ba tare da
ka yi niyyar aikatawa ba, in ba ka yi abin ba, ba za a ba ka lada ko zunubi ba
a kan wannan. So ake ka yi ƙoƙari
ka ture wannan aikin kafin a je mataki na biyu. Wannan matakin na farko shi ake
cewa alkhawaɗir; abu ne kawai
ya ɗarsu a zuciya, ba tare
da ka ɗauki wani mataki a kai
ba. Mataki na biyu, shi ne ka sami Irada, ka ji kana sha'awar abin, to wannan
sai ka yi ƙoƙari
ka ture wannan abin, kar ya kai mataki na uku, shi-ne sai a sami alƙasdu,
wato ka nufaci abin za ka yi. Mataki na huɗu
shi ne, attasmim, wato ya zamanto zuciyarka ta makance dole sai ka yi, To a
matakin farko in ka fasa, ba lada, ba zunubi a kansa; a mataki na biyu, ka
sanya irada za ka yi, sai ka tuna Allah ka fasa, to wannan akwai lada, idan ya
kai wancan mataki na makancewar zuciya, dole sai ka yi, sai ba ka sami yi ba,
to wannan shine sai an sa wa mutum zunubi. Waɗansu
malamai suka ce, matakan guda hudu ne; akwai khaɗir;
sai hadisun nafsi sai hammu, sai azmu, suka ce duk waɗannan guda huɗun,
na farko ba a kama mutum da laifi a kansu, a azmu ne ake kama mutum da laifi.
No comments:
Post a Comment