An karɓo
daga Abu Abbas, Sahlu ɗan
Sa'ad Assa'idi (R.A) ya ce, "Wani mutum ya zo wajen Annabi (ﷺ)
ya ce da shi "Ya Manzon Allah! Nuna min aikin da idan na aikata shi, Allah
zai ƙaunace
ni, mutane ma za su ƙaunace ni."
Sai (Annabi ﷺ) ya ce, "Ka yi
zuhudu cikin lamarin duniya, sai Allah ya ƙaunace
ka, kuma ka nisanci abin da ke hannun mutane, sai mutane su ƙaunace
ka." Ibnu Majah ne ya rawaito shi (#4102) da waninsa ta hanyoyi masu kyau.
SHARHI
Su mutane, idan za ka miƙa
hannu, sai su tsane ka; yau ka tambaya, gobe ka tambaya, jibi ka tambaya. Amma
in ka kame hannunka shi kenan, sai ka tsira lafiya a gurinsu. To abin da ake
nufi da, "Ka yi zuhudu cikin lamarin duniya...." shi ne ya kasance
mutum ya ɗauki duniya ba
komai ba, abin da kawai zai bukata a cikin duniya, shi ne duk abin da yake
wajibi, larurar rayuwa, abin da rayuwa take buƙata
kafin ta gudana a gidan duniya, wanda zai zamar maka dole a rayuwa shi ne ake
bukata. Larurar rayuwa ne ya kasance mutum ya samu halin da zai yi aure, don Ya
sami matar da za ta katange shi daga afkawa cikin laifi; larura ce ta rayuwa ka
sami ci da sha; larura ce ta rayuwa samun gida, mahallin da za ka zauna, ba sai
ka zauna a gidan haya ba. Idan gari yana da girma, ba zai yiwu ba dole sai kana
da abin hawa. Saboda haka abin da ake nufi da zuhudu, shine abin da yake dole
ne a rayuwa ya kasance ka same shi, kar ka ce ka damu da nafilar rayuwa. To
idan ka yi haka, sai Allah ya so ka. In ka fifita duniyarka a kan lahira, to
wannan ƙarshenta
zargi ya zo. Duk inda aka zargi duniya, to ana zargin ne a kan masu fifita ta a
kan abin da ya shafi harkar lahirarsu. Amma mutanen da suka flfita lahira a kan
duniya, in sun samu duniya suna amfani da ita, amma da wani abu ya zo na
lahira, suna fifita shi sama da komai. To wannan shi ne ƙarshen
zuhudu. Ba kamar yadda muke ɗaukar
yadda sufaye suka kawo zuhudu ba, cewa shi ne idan ka sami abinci mai kyau, kar
ka ci, sai kwananne ya fara wari, wai saboda gudun duniya. Wannan ba ya cikin
abin da yake zuhudu wanda shari‘a ta amince ka yi zuhudu a cikinsa.
No comments:
Post a Comment