An karɓo
daga Abu Sa'alaba shi ne Jursumu ɗan
Nashib (R.A) ya ce, Manzon Allah (ﷺ)
ya ce, "Lallai Allah Ta'ala ya farlanta farillai, kar ku tozarta su, ya
sanya iyakoki, kar ku ƙetare su, ya
haramta wasu abubuwa, kada ku keta alfarmarsu, ya yi shiru game da waɗansu al’amura don jinƙan
ku, ba don mantuwa ba, kar ku bincike su. Daraƙuɗuni ne ya rawaito shi a cikin littafinsa Sunan (J 4
sh 184) da waninsa.
SHARHI
Faɗin
Manzon Allah (ﷺ) cewa, "....Allah
Ta'ala ya farlanta farillai, kar ku tozarta su...." yana nufin lallai ku
tsayar da wannan farillan yadda Allah ya ɗora
muku su. Cewar, "....ya sanya iyakoki, kar ku ƙetare..." waɗannan iyakokin, yana nufin dangogin haram, ko kuma abubuwan da suke na haddi; idan mutum ya yi su, za a yi masa haddi kaza, duk wanda ya yi, ku tsayar da haddin a kansa. Sai kuma Manzon Allah (ﷺ) ya ci gaba da cewa, "....ya haramta wasu abubuwa, kada ku keta alfarmar...." waɗannan al'amura da aka haramta su. Sannan sai ya ce, Ubangiji, " ..... ya yi shiru game da waɗansu al'amura don jin-kan ku...." ya yi shiru bai haramta su ba, ya ƙyale ku, ya yi shiru, ba don ya manta ba, don haka kar ku ce sai kun gano hukuncinsu, ku ƙyale, in kuna son ku yi amfani da su, ku yi, in ba kwa so, ku kyale, kar ku ce sai kun gano haram ne ko halal, an ƙyale muku su ne, don rahama, ba don Allah ya manta ba. Da dama daga cikin malaman hadisi sun raunana wannan hadisi, abinda zan iya tunawa daga ciki akwai Ibnu Rajah Alhambali a cikin littafinsa, Jami'ul Ulum Wal-hikam in ban manta ba ya raunana wannan hadisi.
No comments:
Post a Comment