SHARHI
Babukan da suka wuce sun yi magana a kan yana daga
dangin shirka neman taimako wajen wanin Allah. Wannan babi kuma zai nuna maka dalilan
da suke nuna cancantar Allah da bauta shi kaɗai,
Da kuma dalilan
da ke nuna kasawar wanin Allah wajen a bauta masa.
Zai kawo siffofi da suke nuna cancantar Allah a bauta masa shi kaɗai
da siffofi da suke nuna duk wanda ba Allah ba, yana da rauni bai dace a bauta
masa ba. Abin da wannan babi da mai bi masa za su nuna mana kenan.
************************
Da faɗin
Allah;
Shin suna haɗa Allah da wani, wanda ba ya halittar komai, alhalin su ne ake halittawa. Kuma ba sa iya taimaka musu, kuma ko da kawunansu ba sa iya taimakawa? (Al-Araaf 191-192)
_____________________
SHARHI
Wannan na nuna gajiyawa. Dukkan wanda za a sanya
shi kishiya ga Allah, dukkan matsayinsa, ko yana cikin salihan bayi, ko
waninsu, ko yana cikin mala' iku, ko Annabawa, ko aljanu, ko cikin bani Adam,
duk wannan sifar ta hada su, ba sa iya halitlar wani abu, su kansu halitta ne
na Allah (SWA). Ko da Annabi Isa (ASW) nau'in mu' ujizar da aka ba shi, ba ta yin
halitta ba ne mu'jiza ce, ba wai shi ya yi halittar ba. Waɗannan
dalilai
ne na nuna gajiyawar wanin Allah. Duk wani wanda
ba Allah ba, ba ya taimaka wa wani, haka ma ba ya iya taimaka wa kansa, Yanzu wannan
ayar ta nuna mana sittofin gajiyawa uku;
a. Rashin iya halittar wani abu.
b. Rashin taimaka wa kai.
C. Rashin iya taimaka wa wani duk Wani wanda ba
Allah ba, waɗannan sifofin sun tabbata a gare shi.
************************
Da faɗarsa
"Waɗanda
kuke kira ba Allah, ba sa iya mallakar ko da farar fatar kwallon dabino. Kuma
idan kun kira su, ba za Su ji kiranku ba ko da sun ji. ba zä su amsa muku ba,
kuma ranar kiyama za a katirce wa shirkarku, babu kuma mai ba ka labarl, Sama
da (Allah mai cikakken sani." (Faɗir:
13-14)
_____________
SHARHI
Ga wata siffa ta nuna gajiyawar duk wanda ba Allah
ba. Shi ne ba ya mallakar komai, ko da farar fata ta jikin kwallon dabino.
Sannan Ailah (SWA) ya ce duk wanda kuka kira ba zai ji kiram ba. Dalilan da
suke hana jin
kira sun hada da mutuwa, na biyu, idan ba kwa gari
ko waje ɗaya nan ma ba za ku ji ba. Ko gindin
kabari ka je ka kira mai kabari ka ji ya amsa, to wallahi shaiɗan
ne ya ke damfarar masu bauta. Idan an kai wani abinci kabari ko aka yi yanka,
aka kai wa mai kabari, ba shi yake cin abin ba.
Mai kabarin bai ma san an kawo ba. Masu gadin
kabarin, su suke cinyewa, don hakä ba sa so masu wannan aƙidar su gane. Wani
lokaci ma har ƙarya suke yi musu, su ce "Ai mai
kabari wane yana gaishe ka!"
Wallahi duk ƙarya suke! A ƙarshen ayar sai Allah
ya sanya wa abin suna shirka, alhali a farko kira' ya kirawo bautar. Ashe duk
wanda za ka kira ba Alah ba shirka ce!
Wannan aya ƙarara ta nuna kiran wanin Allah, ko
waye, in dai ba Allah ba, shirka ne kamar yadda Allah (SWA) yake cewa ko da
yaushe a Alkur'ani, “Wanin Allah” ka ga ba wai gumaka yake nufi kaɗai
ba. A’a duk wanda ka kira a inda ba wanda zai ji sai Allah, wanin nan Annabi
ne, mala’ika ne, aljani ne, shehi ne, waliyyi ne, ko ma menene, in dai ba Allah
ba ne, ya zama, "Wanin Allah' yin haka babbar shirka ce. Allah ya kiyashe
mu.
***********************
Ya zo a cikin hadisi sahihi, daga Anas ibn Malik,
ya ce, an yi wa Annabi (SAW) rotse ranar Uhud kuma aka balla masa haƙorinsa. Sai Annabi
yake cewa, "Ta yaya waɗansu mutane za
su rabauta, alhalin sun yi wa Annabinsu rotse a ka? Sai wannan aya ta sauka
Allah ya
ce, "Al'amarin (azaba) ba a hannunka yake ba;
dan Allah ya ga dama ya karɓi rubansu, ko
ya yi musu azaba, domin su azzanumai ne
(Ali -Imrana 128)
_______________________
SHARHI
To. Idan an kore wa Annabi mallakar azaba ko
rahama, Allan yà ce duk a hannunsa Suke, za a taboatarwa da wani waliyi ko
shehi? Kuma wannan hadisi shi ne sababin saukar wannan aya ta Cikin Suuraul
Aali-lmraan.
Wannan hadisi, Bükhari |Duba Fathul Bari J / 563
ya kawo shi ba da cikakken isnadi ba, amma Musiim [#1791) ya kawo shi da
cikakken isnadinsa. haka nan kuma Ahmad JS/99] da Tirmizi |#5002) da Nasaa’i
duk sun ruwaito shi.
**************************
A cikin Bukhari Kuma, an karɓo
hadisi daga Abdullahi bin Umar (RA) cewa yaji Manzon Allah (SAW) yayin da ya
dago Kansa daga ruku’u a raka’ar ƙarshe ta sallar asubahi, sai na ji
yana cewa, Allah ka la’anci Wane da wane Bayan ya ce, “Sami Allahu liman
hanidahu, Rabbana Walakal hamdu “ Yana
ambaton wasu kafirai da Sunayensu. Sal Allah ya saukar da wannan ayar,
"Al’amari ba a hannunka yuke Da. (Aali-Imraan: 128) Bukhari #4069]
____________________
SHARHI
Wannan hadisi na nuna sanadiyyar saukar ayar shi
ne alkunut ɗin da Manzon Allah (SAW) ya yi. Yanzu,
wancan sababin ya sha bamban da wannan sababin kuma duk ayar ɗaya
ce. Abin da malamai suke cewa, aya ɗaya
na iya sauka sau biyu, ko uku, ko kuma sama da haka da dalilai daban-daban.
Saboda haka, waɗannan abubuwa guda
biyu, dukkansu a Sanadiyar faruwarsu ayar ta sauka, don ta magance abin da ya
taru ko Suka faru. a wata fuskar daban, aya ta iya sauka sama da sau ɗaya.
Wani abu ya faru ta sauka don dangantakarta da abin, sannan wani lokaci ta Sake
sauka don a nuna cewa tana iya magance wannan matsalar, Kamar yadda take iya
magance waccan matsalar.
Abin da ayar take nunawa, cewar Annabi (SWA) ba
shi da mallakar wani abu a hannunsa na cutar da mutane ko amfanar da su, na yi
musu azaba ko rahama. Abin yana hannun Allah (SWA) ne shi kaɗai,
ba ya hannun
kowa, babu mai tarayya da Allah (SWA) a cikinsa.
Tunda aka ce Annabi ba Shi da shi, Kuma shi ne shugaban halitta, ya nuna kowa
ma ba Shi da shi Kenan. Wannan shi ne babban darasin da ke cikin ayar.
Idan muka koma hadisin Anas ibn Malik, me yake
nunawa? Ga shi Annabi ya fita yaƙin Uhud har an ji masa ciwo a ka. Abin
da wannan yake nunawa shi ne, dukkan wanda ba Allah ba, yakan iya zama ajizi;
ya nuna ba shi ne yake ba wa kansa kariya ba kenan. Allah ya kaddara abin ya
same shi, kuma lallai ne ya same shi. A wannan lokaci, ba shi da tsimi ko
dabara ta kare abin kada ya same shi. Sannan kuma, yana nuna shugabannin jama'a
suna ɗaya daga cikin wafanda ake son su fi
kowa shan wahala. Ga shi Annabi (SAW) ya fita yaƙi, bai zauna a gida ba, ga shi kuma
an fasa masa kai, wannan yana nuna ƙudwatun hasanah. Yadda mabiyansa suka
sha wahala, shi ma ga shi yana shan wahala tare da su, har ma ya ti su shan
wahala.
Hadisin Abduilahi ibn Umar, yana nuna ana iya yin
alƙunut
a kan kafirai. ldan kafirai sun muzguna wa musulmi, ya halatta a yi musu alƙunut don a la'ance
su. Wasu malamai sun fitar da hukuncin cewa ya halatta a ambaci wasu da
sunayensu a la'ance su ko bai halatta ba'? Wasu suna ganin ya halatta a ambaci
sunan wani a la ance shi, Ka fayyace Sunansa, ba wai ka ambace shi a cikin
kafirai ba. Ka ce, "Ya Allah! Ka la' anci wane. Wasu suka ce, in dai ya
halatta ka fayyace wani mutum ka la ance shi, to ya halatta ka fayyace wani
mutum ka ɗora masa Kalmar kafirci. Domin
la'antarsa na biye masa kalmar (kaulasan) wato kafirci.
Domin in dai ka yarda da nagartarsa, ka la a'ance
shi? Wasu suka ce, ba za a ambaci wani mutum da sunansa a la'ance shi ba. Domin
wanda Annabi ya yi a hadisin, ya yi ne kafin a hana shi. Faɗin
cewa, "Laisa laka minal amri shai'un... (Aali-Imraan:128) ya kunshi cewa
nan gaba Annabi (SAW) ya daina la'antar kafirai da sunayensu, sai dai a cikin
taro. Haka kuma, alkunut ana yin sa a cikin sallar farilla, ba sai a wutiri ba.
***************************
A cikin wata riwayar kuma, yana mummunar addu'a ga
Safwan ibn Umayya da Suhail ibn Amru da Haris ibn Hisham.
Sai wannan ayar ta sauka, "Al’amari ba a
hannunka yake ba...” (Aali Imraan: 128) Bukhari #4070]
__________________
SHARHI
Kuma a cikin ikon Allah (SWA), sai waɗannan
mutane suka musulunta, Suka zama cikin manyan sahabbai. Wannan sai ya nuna cewa
Annabawa ba su san gaibu ba. In da Annabi (SAW) ya san za su musulunta, ba zai la'ance
su ba. Bai daina la'antarsu ba, sai da Allah (SWA) ya ce ya daina. To shi ne
hikimar ta cewa ba a nuna wane, Ka la’ance shi, don ka iya la’antarsa yau, gode
kuma ya musulunta, sai dai ka la'anci kafirai a cikin taro, Ka ce, ya Allah: Ka
la’anci kafirai. Sai la’antar ta fada a kan wanda Allan ya san ba zai musulunta
ba. Ga Annabi ya yi adau’a, amma ba’a Karɓa
ba, saboda hikimar Allah cewa mutanen za su musulunta, da an karɓa,
to da ba su musulunta ba. Hikimar rashin karɓa
shi ne nuna cewa mulkin komai gabaɗaya
a hannun Allah (SWA) yake, ba ya hannun Annabi (SAW) ballantana waninsa. Kullum
ana buga misali da Annabi, ba sai an fadi sauran ba.
*******************
A cikin Bukhari, an karɓo
hadisi daga Abu Hurairah, ya ce Manzon Allaln (SAW) ya tashi yayin da aka
saukar masa da, "Ka yi gargaɗi
ga danginka mafiya kusanci (yaya, Iyaye mata da sauransu).. (Shu’ara:214) Sai
ya Kirayi Ƙuraishawa
ya ce, Ku fanshi kawunanku (Imani da aiki nagari) don ba zan iya amfanar da ku komai
ba a wurin AlIah. Ya Abbas ibn Abdul-Muɗɗalib!
Ba zan amtanar da kai komai ba a wurin Allah. Ya Safiyya bint Abdul Muɗɗalib!
Ba zan wadatar da ke komai ba a wurin Allah. Ya Fatima bintu Muhammad: Ki roke
ni Cikin dukiyata duk abin da kike so a nan gidan auniya), don ba zan amfanar
da ke komai ba a wurin Allah (a ranar ƙiyama)."[Bukhari #2753, Muslim
#206)
____________________
SHARHI
Bayan ya kira danginsa, sai aka ce ya kirawo kowa
da kowa. Wannan yana nuna cewa dangantakar mutum, ba za ta yi masa komai ba a
ranar ƙiyama,
mutukar bai yi imani da alki nagari ba. Ba fiddau za a yi maka ta tsirar da
mutum idan ya mutu ba. Sai dai aiyyuka su kwace shi wajen Allah kamar yadda
Allah ya ba da labari a Suuratul Asr. Matular mutum bai yi aiki nagarı ba, in
da zai ciyar da fam-taɓa-sama na dukiya, ba
za su kwace shi wajen Allah ba. Gwara tun farko ka tsaya ka yi wa kanka gata ka
yi imani da aiki nagari yadda addıni ya yi umarni bisa ga dalili ba bisa taƙlidanci ba.
To yanzu Annabi (SWA) kenan an ce ya gargadi
danginsa mafiya kusanci, don ba shi da ikon ya kwaci duk wanda bai bi Allah ba,
to waye ya isa ya ce zai ƙwaci
ɗansa ko babansa ko muridansa Ko
makwabtansa?
Amma saboda izgili da rashin sanin ƙimar Manzon Allah
(wanimalami yake cewa matsayin waliyyansu da shehunansu ya fi na Annabawa! Da
yanzu Annabawa za su dawo duniya, da sun buraci su zamanto muridan Shehi wane!
Sannan suke cewa su sun fi ƙarfin
aljanna!
Sannan zikirin Juma'a da suke yi ya fí Juma'ar
kanta! Irin waɗannan maganganu na hauka, haka suke
tara mutane suna faɗa musu. Da ba dan Annabi
(SAW) ya roka mana ba, da Allah ya yi fushi ya halakar da mu
gabaɗaya
saboda munin iin waɗannan maganganu!
Wannan hadisi Abu Huraira ne ya ruwaito, amma ba
shi ne ya halarci ƙissar
da kansa ba. Ya samu ƙissar
a wurin sahabbai. Ba ka buƙatar
ka san wannan sahabin, Domin a ƙa'idar
malaman hadisi, jahiltar wanene sahabi, ba ya cutar da kai, domin sahabbai
dukkansu adalai ne, Allan ya adalantar da su. Domin wani zai iya cewa wannan
hadisi na Makka ne, kuma Abu Hurairah a lokacin bai musulunta ba.
************************
A Cikin Wannan Babi Akwai Mas'auloli Kamar Haka.
1. Tafsirin ayoyi biyun larko.
2. Ƙissar yaƙin Uhud.
3. Mun ga alƙunutun da shugaban manzanni ya yi kuma
shugabannin waliyyan duniya (sahabbai) suna cewa
amin
4. Waɗanda
kuma aka yi wa addu'ar kafirai ne.
5. Cewa waɗanda
aka yi wa addu'ar sun yi tabargaza wanda mafi yawan kafirai ba su yi ba. Wato
shi ne Sun ji wa Annabi ciwo, da kuma buƙatarsu ta su kashe shi, sannan kuma
sun yayyanki wasu ɓangarori na
gawawwakin musulmi bayan yaƙi,
tare da cewa ya'yan baffanni suke.
6. Duk da haka, Ubangiji ya saukar da,
"Al'amari ba a
hannunka yake ba...
7. Faɗar
Allah, "..kuma ko ya gafarta musu ko ya yi musu azaba... sai ya karɓi
tubansu ɗin, suka kuma yi imani.
8. Halaccin yin alkunut a cikin matsatsi, “Ana yin
alkunuti lokacin da kafirai suka tsanantawa musulmai, ko kuma wata musifa da
nassin shari'a ya bada izini a yi. Kamar lokacin fari, sai a yi ko wata ya yi
khusufi. Amma cuta ta kamar kwalara, ko makamantansu, Annabi (SAW) ya hana a yi
musu kunuti. Haka ma wata buƙata
taka ta duniya, kamar cin jarrabawa ko neman makaranta, ko neman aure, duk waɗannan
ba a yi musu alkunuti.”
9. Halaccin anbaton sunayen waɗanda
ake yi wa munanan addu’a da sunan iyayensu.
10. Ana kuma iya la antar wani sananne a cikin
alkunut.
11. Ƙissar Manzon Allah (SAW) yayin da aka
saukar masa da, "Ka yi wa danginka na kusa gargaɗi.
12. Ƙoƙarinsa (SAW) wajen isar da musulunci
inda har akedanganta shi da hauka. Ko da musulmi ne ya yi a yanzu, Za a ce masa
haka.
13. Faɗin
Manzon Allah (SAW) ga na kusa da shi, da na nesa da shi, "Ba zan iya
wadata maka da komai ba a wurin Allah..
har zuwa inda yake cewa, "Ya Faɗimatu
yar Muhammad!
Ba zan wadata miki komai ba a wurin Allah. To har
idan
Manzon Allah (SAW) ya bayyana haka, kuma shi ne
shugaban dukkan manzanni, cewa ba zai iya wadatar da shugabar matan duniya da
komai a wurin Allah ba, to in dai mutum ya yi imani da hakan, sannan ya kalli abin
da yake cikin zukatan wasu mutane, da suke ganin kansu keɓantattu
ne, to zai bayyana a gare shi, yadda tauhidi yake, da kuma yadda addini ya zamo
baƙo.
Super article;)
ReplyDeleteAgree with this;)
ReplyDelete