An karɓo daga ɗan Abbas (R,A) ya ce,
Manzon Allah (ﷺ), ya ce, “Ku riskar da
kowanne rabon gado sananne ga ma’abotan wannan rabon, abin da ya ragu, to a ba
namiji wanda
ya fi kusanci.” Bukhari (#6732) da
Muslim (#1615) ne suka rawaito shi.
SHARHI;
Abin da wanna hadisi yake nufi shi
ne, rabon gado kashi biyu ne: Akawai waɗanda ake basu da farali, wato masu rabo
sananne, wanda shi kuma ya kasu kashi shida: ko a ce a baka rabin dukiya (1/2), ko ɗaya
bisa hudu (1/4) na dukiya, ko ɗaya bisa takwas(1/8) na dukiya,
ko ɗaya bisa uku (1/3) na dukiya, ko biyu bisa ukun (2/3) na
dukiya, ko ɗaya bisa
shida (1/6) na dukiya. Wannan shi ne farali guda shida! Duk wanda suke
da rabin dukiya sanannu ne, mutane ne kasha biyar, ban da su ba a ba kowa;
waɗanda ake ba kasha ɗaya bisa huɗu na dukiya, su ma waɗannan sanannu ne; kashi
ɗaya bisa takwas na dukiya, su ma sanannu ne; kashi biyu bisa uku; ko kashi
ɗaya bisa shida, duk waɗannan sanannu ne, ayoyin Alkur’ani sun yi bayaninsu. To
wannan shi ne farali! abin da ba wannan ba, sai a ce masa asibci, shi ne
mutumin da ba a ce ɗauki kaza bisa kaza ba. Lallai zai ci gado, amma ba a ce
ɗauki kaza bisa kaza ba, shi dai yana cikin masu cin gado. Idan waɗanda
aka ce su ɗauki kaza bisa kaza an ba su, abin da ya yi ragowa nasa ne gaba
ɗaya, ko shi da masu matsayi irin nasa, su raba, namiji yana da rabon mata
biyu.(FASSARA DA SHARHI DA GA BAKIN GARIGAYI SHEIK JA’AFAR MAHAMUD ADAM {R} ).
No comments:
Post a Comment