An karɓo daga Abu Muhammad
Abudullahi ɗan Amru ɗan As (R.A) ya ce, Manzon Allah (ﷺ), ya ce, “Ɗayanku ba ya zama mumini, har sai son
zuciyarsa yana biyayya ga abin da na zo da shi.” Hadisin ne ingatacce, mai
kyau, mun rawaito shi a cikin littafin Hujja da sanadi ingantacce.
SHARHI;
Wanna hadisi an karɓo shi daga Abu
Muhamad, shi ne Abdullahi ɗan Amru ɗan As, ɗaya daga cikin ‘Abadila’
(wato waɗanda ake kira Abdullahi ) a cikin sahabbai,
waɗanda su huɗu ne, duk sunansu ya
fara Abdullahi: su ne, Abdullahi bn Umar, Abdullahi bn Abbas, Abdullahi bn
Mas’ud da Abdullahi bn Amru bn As. Waɗannan
waɗanda suka shahara kenan, ban da
zu za a iya samun Abdullahi da dama. Idan kana karanta litattafan Hadisi
Musamman Sahihul Bukhari sai ka ji ya ce, maka, “Daga
Abdullahi, daga Annabi (ﷺ), ….” bai faɗi Abdulllahi ɗan Abbas ba ko ɗan waye
ba, kawai yace daga Abdullahi, kuma daga Annabi (ﷺ), , to Abdllahi bn mas’ud
yake nufi. Ida wani yake nufi ba shi ba, zai faɗe shi. Haka idan cikin sunan,
tabi’ai suka ce Hasan, suka yi shiru, to suna nufin Alhasnul Basari.
Imamun Nawawi ya ce, wannan “Hadisi
ne ingatacce, mai kyau, mun rawaitoshi a cikin littafin Hujja da
sanadi ingatacce.” amma hadisi ne mai rauni da’ifi. Da ma hadisai uku ne,
waɗanda malamai suka raunana su cikinArba’una hadis. Hadisi na 30,
sai kuma wannan, na uku shi ne hadisi na 31, sai dai wannan (na 31) sahihi ne,
yana da waɗansu hanyoyyi da inganta da su. Sannan kamar yadda muka faɗa a baya
cewa, tayiwu ta fuskar riwayar hadisi da’ifi ne amma ta fuskar ma’anar da yake
ɗauke da ita, ta iya shiga ƙarƙashin wata aya ko ingantaccen hadisin daban,
amma ka jingina wa Annabi (ﷺ), ka ce,
Annabi ya ce, “Ɗayanku ba zai zama mumini ba, har sai son zuciyarsa yana
biyayya ga abin da nazo da shi” wannan jumla Annabi (ﷺ), bai faɗe ta ba, bat a tabbata daga gare shi
ba, amma ayoyin Alƙur’ani da dama sun nuna duk abin da zamu so, to ya dace da
abin da Allah ya ce, Annabi(ﷺ), ya ce,
kar mu bi son zuciyarmu kawai.
No comments:
Post a Comment