An karɓo
daga Abu Sa'id, Sa'ad ɗan
Malik ɗan Sinan Al-Khudriy
(R.A) ya ce, Manzon Allah (ﷺ) ya ce, "Ba cuta,
babu cutarwa." Ibnu Majah ne ya rawaito shi (#2341) da Daraƙuzuni
(#228) da waninsu Musnadan. Haka Imamu Malik ya rawaito shi a cikin Muwaɗɗa (J2/sh 746) daga Amru ɗan Yahya daga babansa daga Annabi (ﷺ)
Mursalan, bai ambaci Abu Sa'id ba. Amma hadisin yana da hanyoyin da sashinsu
yana ƙarfafa
sashi.
SHARHI
Waɗansu
malamai suka ce, abin da ake nufi da gaɓar,
"Ba cuta...." shi ne kada ka cuci wani, don ka amfana da wannan cutar
tasa, "....babu cutarwa." kuma tana nufin kada ka cuce shi, ko da ba
za ka amfana da wannan abin ba. Misali mutum yana da kuɗi, sai ka je ka sace masa, ka zo ka yi amfani da su.
Wannan shi ne darar, ka cutar da wani don ka amfana. Dirar kuma, mutum ne yana
da dukiya ko kadara, sai ka je ka ƙona
ta, ka raba shi da ita, ba don ka amfana da ita ba. Wannan shi ne dirar. Wannan
hadisi ne da yake an kafa ƙa'idojin
fiƙihu
da shi da dama. A ƙarƙashin
wannan hadisi, dukkan dangin cutarwa, shari'a ta haramta shi, duk abin da za ka
yi ya zamanto ka musguna wa ɗan
Adam ɗan uwanka musulmi, to
shari'a ba ta yarda ba.
No comments:
Post a Comment