An karɓo daga Abdullahi ɗan
Busur, (R.A) yace wani mutum (mazaunin karkara ) yazo wurin Annabi (ﷺ), yace ya Manzon Allah shari’oi sun yi
mana yawa a bamu wani babu gamamme da zamu riƙe. Sai Annabi (ﷺ), yace "kada harshenka ya bushe wajen
ambaton Allah "Ahmad ne ya
rawaito shi (#188, 190).
SHARHI;
Wannan hadisin yana nuna cewa, wani
mutum mazaunin karkara yazo wurin manzon Allah (ﷺ), yace dashi ya manzon Allah shari’oi sun yi
mana yawa an ce kayi kaza, ka bar kaza, don haka a faɗi wani guda ɗaya wanda zamu riƙe wanda ba gudu baja da ya sai anyi
shi ko ana cikin me, Sai Annabi (ﷺ), yace, kada harshenka ya bushe wajen ambaton
Allah in dai kana son abin da zaka rike ba wahala kayi, komai kuɗinka komai talaucinka zaka iya yi ko
kana da muƙami
ko baka dashi kana kwance, a gadon asibiti ko a gida kake
matuƙar kana da rai zaka iya yi yace, to
ga zikirin Allah abin da ake nufi ka zamanto mai ambaton Allah a tsaye ko
ayaune, Allah yana cewa,
"الذين يذ كرو ن الله قيما
وقعودا و على جنو بهم و يتفكرو ن فى خلق السمولت ولارض ) ال عمران."
Ma'ana (Waɗanda suke ambaton Allah atsaye da
zaune, da in suna kwance kuma suna tunani akan halittar sammai da ƙassai) (Ali Imran 191)
Wannan shi ne cikon hadisi na hamsin
idan an ƙara
guda takwas waɗanda
Ibnu Rajab Alhambali ya ƙara kenan, kuma wannan shi ne ƙarshen wannan fassarar llittafi mai
albarka na Arba’una Hadis abin da duk muka faɗa na dai-dai Allah ya bamu lada a kai, wanɗa mukai kuskure, to Allah ya yafe
mana.
(FASSARA
DA SHARHI DA GA BAKIN GARIGAYI SHEIK JA’AFAR MAHAMUD ADAM {R} ).
Masha Allah
ReplyDelete