An karɓo
daga Mu'azu ɗan Jabal (R.A)
ya ce, "Na ce, Ya Manzon Allah! Ba ni labarin wani aiki da zai shigar da
ni aljanna, ya kuma nisantar da ni daga wuta.“ Sai ya ce, "Haƙiƙa
ka yi tambaya game da abin da yake mai girma, sai dai abu ne mai sauƙi
ga wanda Allah ya sauƙaƙe
shi gare shi. Ka bauta wa Allah, ba tare da ka haɗa
shi da wani ba, kuma ka tsayar da sallah, kuma ka ba da zakka, kuma ka azumci
Ramadan, sannan ka ziyarci ɗakin
Allah." Sannan sai (Annabi ﷺ)
ya ce, "Shin ba zan shiryar da kai ƙofofin
alheri ba? Azumi garkuwa ne, sadaƙa
kuma tana shafe kurakurai, kamar yadda ruwa yake kashe wuta, haka sallar mutum
a cikin yankin dare. Sannan ya karanta (faɗin
Allah), "...gefen jikinsu yana nisantar gurin kwanciyarsu. . . " har
ya kai inda (Allah yake cewa ’Ya'amaluun' sannan sai Annabi ﷺ)
ya ce, "Ba zan ba ka labarin kan al'amarin ba, da ginshikinsa da ƙololuwar
Samansa?" Sai na ce "Eh!" sai ya ce, "Kan al'amarin (shi
ne) musulunci, ginshiƙinsa kuwa salla,
ƙololuwar
samansa kuwa jihadi." (Sai Annabi ﷺ)
ya ce, "Ba zan ba ka labarin abin da yake mallakar kusan gaba ɗaya ba?" sai na ce "Ba ni labari."
sai ya kama harshensa ya ce, "Ka riƙe
wannan." Sai na ce, "Shin yanzu za a kama mu da maganar da muka
yi?" sai (Annabi ﷺ) ya ce, "Da ma
mahaifiyarka ta rasa ka! Akwai abin da yake jefa mutane wuta a kan fuskokinsu
(ko ya ce) kan hancinsu, sai sakamakon abin da harshensu ya faɗa." Tirmizi (#2616) ya ce, hadisi ne mai kyau,
ingantacce.
SHARHI
Wannan hadisi daga Mu'azu ɗan Jabal (R.A) ya ce, "....Ba ni labarin wani
aiki da zai shigar da ni aljanna, ya kuma nisantar da ni daga wuta...."
Wannan ne ya sa ake cewa fatawar sahabbai ta sha bamban da tamu, saboda su
kullum nema suke ina inda za a shiga aljanna, ina inda za a sami tsira da tsari
daga wuta. Haka za ka ji kullum suna tambayar Annabi (ﷺ),
sai Annabi (ﷺ) ya zana musu dangogi
masu yawa, don idan ka kasa yin wancan, ka yi wannan.
Dangane da faɗin
Annabi (ﷺ)
cewa, "Haƙiƙa
ka yi tambaya game da abin da yake mai girma, sai dai abu ne mai sauƙi
ga wanda Allah ya sauƙaƙe
shi gare shi....." wannan shi ya sa ake son kullum ka roƙi
Allah tabbatuwar shiriya a kan tafarki madaidaici. Duk yadda ka kai da son
gaskiya da begenta, in ba Allah ne ya yi ma gam-da katar ba, ba za ka dace da
ita ba. Faɗin Annabi (ﷺ)
kuwa cewa, "....Azumi garkuwa ne...." yana nufin azumi na nafila. Don
azumin wajibi ya riga ya gabata a can, a wani hadisin ya ce, "....azumi
garkuwa ne zai kare mutum daga wuta...." [Duba Tirmizi (#764)] saboda haka
Annabi ke kwaɗaitar da mu da
yawaita azumin nafila, bayan mun sauke na farilla. Azumin nafila kuwa yana da
yawa: Litinin da alhamis ana yi; shida cikin Shawwal bayan ƙaramar
sallah kenan, wanda yake kankare zunubin shekara ɗaya
gaba ɗaya; azumin Tasu'a da
Ashura, tara da kuma goma ga watan Muharram, shi ne farkon azumin da aka
wajabta a musulunci, daga baya aka wajabtar da Ramadan, shi wancan aka mai da
shi ya zama mustahabbi; azumi uku a kowane wata, musamman ma sha uku da sha
hudu da sha biyar ga wata. A taƙaice
duk wannan dangogin azumi, azumi ne na nafila da zai taimaka wa mutum. Azumin
nafila idan za ka yi sama da haka, ka ga kana da ƙarfin
da za ka yi sama da abin da muka ambata, to sai ka yi azumi yau, gobe ka ƙi
yi, jibi ka yi, gata ka huta, citta ka yi. Wannan shi ne Siyamu Dawud da Annabi
(ﷺ)
ya ce, "Azumin da Allah ya fi so, shi ne azumin Annabi Dawud, ya yi yau,
ya huta gobe, jibi ya yi, gata ya huta." [Duba: Sahih Al Bukhari (#1131)
da Sahih Muslim (#1159)]. Saboda haka ba sunna ba ne ka je ka jeranta azumi
kwanakj masu yawa na nafila! Sai dai ka yi yau gobe ka huta, jibi ka yi, gata
ka huta, haka Annabi (ﷺ) ya koya wa sahabbai.
Ba jarumta ba ne don ka yi wata biyu a jere ko wata uku a jere, ka saɓa wa sunnar Annabi (ﷺ)
ba ka sani ba. Shi addinin musulunci ba wai jarumta ko gwaninta yake so ba,
a'a! abin da ake so ka yi, sai ka yi, shi kenan magana ta ƙare,
komai ƙankantarsa,
kada ka raina shi. Sadaƙa ma a nan, ana
nufin ta nafila, domin maganar zakka, ta riga ta gabata a baya.
Sallar mutum a cikin wani yanki na dare, wato ƙiyamullaili
kenan, za ka yi cikin jam'i, za ka yi kai kaɗai,
za ka yi kai da matarka, duk wanda ka sami dama ka yi. Sai dai ƙiyamullaili
a cikin jam'i ya fi falala, sama da ka yi kai kaɗai.
Wannan ita ce fatawar da muka tafi a kai, don akwai haidisi a kai, inda Annabi
(ﷺ)
ya ce, "Duk wanda ya tsaya da liman, suka yi sallar dare, har liman ya yi
sallama, sannan kai ma ka yi sallama, za a rubuta maka kamar ka sallaci daren
gaba ɗaya." [Tirmizi
(#806) da Nasa'i (#1605) da Ibnu Majah (#1327) suka rawaito shi]. Amma idan kai
kad‘ai ne, to sai ka yi adadin da ake buƙata,
sannan za a ce ka yi ƙiyamullaili,
amma matuƙar a bayan liman ne, ko
raka'a huɗu ya yi, ya tafi
gida, ko shafa’i da wutiri kaɗai
kuka yi da liman ya tafi gida, za a rubuta maka ka sallaci dare gaba-ɗaya, ka ga ba za ka haɗa
da wanda ya yi shi kaɗai
ba.
Faɗin
Manzon Allah (ﷺ) ga Mu‘azu cewa,
sakilatka ummuka jumloli ne da ba a nufin zahirin ma'anarsu. Larabawa sun saba
suna amfani da su, shi ya sa ba a yin fassara ta kai-tsaye a kan irin wannan,
sai ya kasance ka fassara su da abin da bai dace ba. Fassara ta kai-tsaye,
sakilatka ummuka yana nufin da ma dai mahaifiyarka ba ta haife ka ba. Ka ga ba
zai yiwu Annabi (ﷺ) ya faɗa masa haka ba! Amma su Larabawa sukan faɗi haka ga mutumin da bai fahimci wani abin da ya
kamata ya fahimta ba, su ce, "Wane! Wane irin tunani ne gare ka? Ina hankalinka
ya tafi har ka kasa fahimtar abin da muke nufi?“ Kamar haka ne Annabi yake
nufi.
Asalamu alaykum, Allah ya kara mana imani ya kuma sa mudace Ameen,sadai kuma dan yi gera a rubutun angode
ReplyDeleteAllah ma
ReplyDeleteWanna hadisin Aziz ne
ReplyDelete