An karvo daga Abu Hurairata (R.A) ya ce, Manzon
Allah (ﷺ) ya ce, "Kada ku riqa yi wa juna hassada, kada ku yi kore, kada
ku yi qiyayya da juna, kada ku juya wa juna bayanku, kada sashenku ya yi ciniki
a, cikin cinikin xan uwansa. Ku kasance bayin Allah, 'yan uwan juna. Musulmi
xan uwan musulmi ne, kada ya zalunce shi, kada ya kunyatar da shi, kada ka yi
masa qarya, kada ya wulaqantar da shi. Tsoron Allah yana nan (har sau
uku)." Yana nuna kirjinsa, "Ya ishi mutum sharri, ya rinqa tozartar
da xan uwansa musulmi. Jinin kowanne musulmi da dukiyarsa da mutuncinsa, haramun
ne a kan musulmi“ Muslim ne ya rawaito shi (#2564).
SHARHI
Abin da ake nufi da 'hassada', shi ne ka riqa burin
ina ma ni'imar da wane yake ciki, ta taho, ta bar shi; ina ma dukiyar wane ta
ragu, jarinsa ya lalace; ka rinqa jin ina ma muqamin da aka bai wa wane ya zo
ya rasa, to wannan ita ce hassada. Kuma siffa ce ta yahudu, sun fi kowa sanin
Annabi (ﷺ) da siffofinsa, amma hassada ta hana su yin imani da shi. Don haka,
ka yi qoqarin ka wanke zuciyarka daga yi wa xan uwanka musulmi hassada. Ko da
mutum yana qoqarin yin takara da kai kan wasu al'amura na duniya, kai kar ka yi
takara da shi. Lallai mutum ya kasance ya tarbiyatar da kansa a kan haka.
Lafazin ‘kore' da ya zo a wannan hadisi, shi ne kana da rumfa a kasuwa, kana
sayar da jakunkuna, sai na zo zan sayi jaka, muna cikin ciniki, ka ce naira
dari biyu, ni kuma ina cewa naira tamanin, kawai sai wani xan kore ya zo ya
xauki irin wannan jakar ya ce, "Don Allah ka sayar min da wannan jakar
xari da hamsin." Shi wanda ya zo ya yi hakan xin, ya yi ne fa don saboda
ni. Ya ce, "Xari da hamsin, ka sayar?" Ya ce, a'a! ya ce, "To
xari da sittin da biyar.", wai dole sai ya zurma ni na shiga, a yi da kyar
a sayar masa xari da saba'in. Bayan kuwa ciniki ne na bogi, na qarya, ba
gaskiya ba ne, don kawai ni in kai xari da saba'in, farashinta kuwa naira
tamanin. To wannan shi ne 'kore', kuma duk malamai sun yi ittifaqin haramcinsa.
Dangane da yiwuwar cinikin kuwa, waxansu suka ce ya yiwu, waxansu kuma suka ce
bai yiwu ba. Sai dai mafi ingancin magana, cinikin ya yiwu, don shi wanda ya zo
wannan tayi, ai ba da shi muka yi ciniki ba. wannan shi ne abin da Imamu Malik
bin Anas ya ce. Amma idan daga baya ka gane cewa wancan xan kore ne, to kana da
dama ka fito, ka mayar ka ce ba ka so a ba ka kuxinka, kuma dole ne a ba ka. In
kuma ka ce shi kenan kai ka haqura, kana son abin haka, ba komai, ya halatta.
Abu na uku: Annabi (ﷺ) ya ce, kar ku zamanto masu
qiyayya da juna. Ka je kana fushi da wani, shi ma yana fushi da kai, wannan ma
ba a so. Abin fushi idan ya faru, to a yi qoqari a rarrashi zuciya ta haqura.
Da Manzon Allah (ﷺ) ya ce, ...kada ku juya wa juna bayanku "yana nufin kar
ku qaurace wa junanku, ku yanke mu'amala da Juna. In dai an fara mu'amala kar a
yanke ta, a ci gaba, sai in an riga an cuce ka ne, to idan aka zo za a sake
zaunawa, sai ka ce "A'a! Ai rannan ka cuce ni, ba zan yarda ba."
sallah dai mu yi tare, da azumi komai ma mu yi tare. Sai kuma Manzon Allah (ﷺ)
ya ce, "....kada sashenku ya yi ciniki a cikin cinikin xan
uwansa...." Abin nufi, idan mu biyu muna da haja ta kasuwanci da muke
sayarwa, idan kwastoma ya shigo rumfata muna tsaye muna cinikayya, na sa masa
suna yana tayi, to bai halatta ba ka zo ka juye kwastoman nan ka ce, "Zo
mana in sayar maka qasa da yadda ya ba ka." Vangare na biyu, idan ni saye
nake a wani wuri, na zo ina sayen kaya, an sa min suna ina yin tayi, bai
halatta ba wani shi ma ya shigo, ya ce shi ma zai sayi wannan kayan, sai har ni
na bari, ba a daidaita da ni ba.
Daga qarshe sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce, "....Ku
kasance bayin Allah 'yan uwan juna, musulmi xan uwan musulmi ne, kada ya
zalunce shi, kada ya yi masa qaya, kada ya kunyatar da shi." ko ka qi
taimakonsa. In ya nemi taimakonka, ka taimaka masa, "....kada ya wulaqatar
da shi...." wai don talaka ne. Ka ba shi matsayinsa da ya dace da shi. Aisha
(R.A) tana cewa, "An umarce mu, mu sauke kowane mutum a matsayinsa."
Manzon Allah (ﷺ) ya qarasa da cewa, "....Ya ishi mutum sharri, ya rinqa
tozartar da xan uwansa musulmi...." Sharri ne babba tozartar da xan uwanka
musulmi, don talaucinsa ko don qaramin ma'aikaci ne, ko don xan makaranta ne,
ka xauka ba komai ba ne.
Jakallahu khairan
ReplyDeletenogode
ReplyDelete