An karɓo daga Miƙdamu ɗan Ma'adi
Yakrib (R.A) ya ce "Naji Manzon Allah (ﷺ), yana cewa, "Dan Adam bai taɓa cika wani
boki ba, ko wani ƙoƙo mafi sharri, sama da cikinsa ba. Ya ishi ɗan Adam waɗansu
'yan lomomi, wanda za su tsaida masa gadon bayansa (Yunwa ba zata galabaita shi
ba). Idan dole (sai ya ci abinci da yawa), sai
ya kasa cikinsa kasha uku, kashi
ɗaya abinci, kashi na biyu ruwan sha, kashi ɗayan ya bar wa numfashi."
Ahmad (J4/ sh 132) da Tirmizi
(#2380) da Ibnu Majah (3349) Tirmizi ya ce, Hadisi ne mai kyau.
SHARHI;
Wannan shi ne ladabin cin abinci
kenan da Annabi (ﷺ), ya koyar da mutane.
Annabi (ﷺ), ya ce, ka kasa cikin ka uku.
Don haka sai malamai suke cewa, wannan abin da Annabi (ﷺ), ya bayar shin umarni ne na wajibi idan an ƙi
bin sa an yi saɓo, ko kuma shiryarwa ce? idan ka kama wannan abu, ka kasa
cikinka uku, zai fi dacewa, kuma ya tabbatar da lafiya, kuma kana da ladan
biyayya ga Annabi (ﷺ), dangane da abin
da ya yi na shiryarwa, amma in ka cika cikinka, ka tashi ba ka son komai,ba ka
yi wani zunubi ba. Akwai malaman da suke da wannan ra’ayi na ƙarshe cewa, ka
ɗauki abin da aka fi so, amma in ka cika cikinka ba komai. Suka ce ai Abu
Hurairata (RA) ya cika cikisa a gaban Annabi (ﷺ), kuma Annabi (ﷺ), bai ce masa komai ba. Abu Hurairata (RA) yana
jin yunwa sai aka kawo sadakar nono kofi ɗaya. Abu Hurairata (RA) ya ce,
so nake Manzon Allah (ﷺ), ya ce,
"Shanye!" ko ya ɗan kurɓa ya ba ni kawai sai Annabi (ﷺ), ya ce, "Jeka ka kirawo wane da wane, suna
nan a zaune." Ya ce, ya nono kofi ɗaya a ce in kirawo wane da wane. Sai ya
yi haƙuri ya je ya ce "Annabi (ﷺ), ya ce, ku zo!" Sannan aka ce masa, ba wa
wane ya sha, miƙa wa wane shi ma. Duk sai da kowa yasha ya ƙoshi, sai Annabi (ﷺ),
ya ba Abu hurairata (RA) ya ce,
"Sha!" Ya ce, "Na sha, na sha." Annabi (ﷺ), ya ce, "Ƙara dai!" Har yace wallahi
ya ma’aikin Allah, babu wani wuri da ya rage, babu, ya cika, ya gama. Ka ga a
nan a gaban Annabi (ﷺ), Abu Hurairata
(RA) ya cika cikinsa, ba bin da ya rage a ciki. To shi ne suka ce, in da
haramun ne Annabi (ﷺ), ba zai bashi dama
ya yi wanan ba (Duba Bukhari #6452).
(FASSARA
DA SHARHI DA GA BAKIN GARIGAYI SHEIK JA’AFAR MAHAMUD ADAM {R} ).
No comments:
Post a Comment