GABATARWA.



WWW.TAFARKINSUNNAH.BLOGSPOT.COM

WANNAN SHAFI YANA DAUKE DA HADISAN ANNABI(SAW)ACIKIN HARSHEN HAUSA. IDAN ANGA MUNYI KUSKURE ASANAR DA MU.ALLAH YAYI MUNA JAGORA AMEEN!



DAMIN AIKO DA GYARA KO KARIN BAYANI;
{tafarkinsunnah@gmail.com]

Sep 9, 2013

KITABUT-TAUHID (BABI NA ƊAYA 1)


                                       KITABUT-TAUHID
_____________  
SHARHI
Abin da tauhidi yake nufi shi ne kaɗaitawa, Wato daga Kalmar wahhada, Malam a nan ya na nufin Kitabut-tauhidillahi wato llttafin kaɗaita Allah. Kaɗaita Allah, kuma
ta ɓangarori ne guda uku.
  1) Rubuubiyya: Daga kalmar Rabb, wadda ma’anarta shl ne mai halitta da kuma kulawa da halitta ɗin. Tabbatarwa da Allah (SWA) ne kadai ya yi halittu gabaɗaya kuma yake kula da su, shi ne kaɗaita Allah da rububiyya.
  2) Uluuhiyya ko Al-Ilahiya: Daga kalmar A I-ilaallu wato alma ’abuudu wato abin bauta. Amma a shari’a ldan an ce alma’abuudu abin da ake nufi shi ne abin bautawa bautar ta gaske,
Don haka duk wanda aka bautawa ba Allah ba, to ba bautar gaske ba ce. Allah (SWA) kaɗai ake wa ta gaskiya. Shi ya sa kalmar shahada ta ƙunshi ɓangarori guda biyu: Bangare na farko, kwaɓe rigar ilahantaka ga kowa wato Iaa ilaaha. Sal kuma Bangare na biyu illallahu, wato sal Allah (ﷺ)  kaɗai.
 3) Kaɗaita Allah wajen sunayensa da siffofinsa. Dukkan suna ko siffa na Allah, nasa ne, wani ba ya tarayya da shi wajen sunan ko siffar.

********************
Da faɗin Allah Ta’ala;
"Kuma ban halicci aljanu da mutane ba, sai domin su bauta mini."  (Zaariyaa; 56)
__________________________
SHARHI
Malam da ya ce Kitabut-tauhid, sai ya fara da kawo ayoyi da hadisai. Wato ba ra’ayinsa ya kawo ba, zallar gaskiya ce.
        Kalmar ‘aljanu’ a ayar ta haɗa
dukkan jinsin aljanu gabaɗaya, haka ma kalmar ‘mutane’ ta haɗa dukkan bil adama a ban ƙasa, maza da mata, yara da ƙanana, kowa da kowa. Don haka kowa an halicce shi ne don ya yi bauta ga Allah (SWA). Don haka za mu ga a cikin jinsin mutane, Annabawa sun fl kowa falala, amma duk da haka bayi suke ga Allah (SWA), su kansu an halicce su ne don su bautawa Allah. Shi ya sa a wajaje da yawa a Alƙur’ani Allah (SWA) yana siffantasu da bayi. Kamar yadda ya siffanta Annabi Dawud (AS) da Annabi Sulaiman (AS) da Annabi Ayyub (AS) da sauransu.
"Ka ambaci bawan mu Dawud ma’abocin ƙarfi, haƙiƙa shi mai yawan komawa ga Allah ne."(saad;17)
"Kuma mun bai wa Dawud kyautar (ɗa) Sulaiman, madalla da bawanmu, lallai shi mai yawan komawa ne ga Allah." (Saad:30)
Haka kuma Annabi Muhammad (ﷺ)  cikin farkon Suuratul Israa ’ da Suuratul Kahfi da .Suuratul Furƙaan.
"Godiya ta tabbata ga Allah Wanda ya saukarwa da bawansa Alƙur’ani, bai sanya shi karkatacce ba." (Kahfi: 1)
"Tsarki ya tabbata ga (Allah) Wanda ya tafiyar da bawansa da daddare...”(Israa’i:1)
"Albarka (ta Allah) ta yawaita Wanda ya saukar da Alfurkan ga bawansa don ya zama mai gargadi ga talikai."(Furƙaan:1)
Duk Allah (SWA) ya siffanta su da bayi masu bauta ga Allah. Ashe Annabawa ma ba a bauta musu, su ma bautar suke yi. Annabawa, matsayin su a wajen mutane shi ne matsayin tsani Wanda ba za mu san me Allah (SWA) yake so da kuma abin da ba ya so ba, sai ta hanyar su Annabawan. Duk wata kafa a toshe take ta hanyar bayi da Allah sai ta hanyar Annabawa kadai. Ba wani Wanda zai samu wata hanyar sanin, ko fada mana abin da Allah  ke so, ko ba ya so, sai ya zamanto Annabi. Idan ba Annabi ba ne ba, to sai mu ce daga ina ka samo Shi? Kuma Annabi idan ya zo, sai ya yi. nasa kuma ya umarci mutane su yi. Hikimar shi ya yi, shi ne ya nunawa mutane ba ni za ku yi wa ba, Allah za kuyi wa. Amma matsayina, ku so ni sama da kowa, ku girmama ni sama da kowa, sannan kada ku karɓi wani saƙo da zai sada ku da rahamar Allah sai Wanda ni na ba ku. Wannan shi ne matsayin Annabawa a wajen mutane, amma ba a bauta musu. Dukkan su bayi ne an kallafa musu yin aiki. Don haka suka fita jihadi suka wahala har aka fasawa Annabi (ﷺ)  hakori a yaƙin Uhud, aka kore shi daga Makka, yana jin yunwa. Idan ya zamanto Annabawa bayi ne gabadayansu, to ina ga Wanda ba Annabi ba? Dole shi ma ya zamto bawa ga Allah.
   Imam Mujahid, wajen tantance menene Al-Ibaadah, yake cewa, ma’anar ayar  shi ne sai don na sa su, kuma na hana su. Don haka sai ibada gabaɗaya ta zama umarni da hani. Shi ne samfurin abin da aka bai wa Annabi Adam (AS) da matarsa a cikin aljanna, wato umami da hani.
Aka Ce;
"Kuma muka ce, "Ya Adamu! Ka zauna kai da matarka cikin gidan aljanna, kuma ku ci daga abin da kuka so, kuna masu jin dadi, kada kumaku kusanci wannan bishiyar, sai ku kasance cikin azzalumai.” (AI-Baƙara:35)
             Don haka, ibada umami ne da hani gabaɗaya. Ka san me Allah ya umarce ka, ka yi, kuma ka san me ya hane ka, domin ka hanu. Yin wannan shi ne bauta. Ka ga kenan sai an ce ka yi sannan za ka yi. Idan ka fara yi ba a ce ka yi ba, ya zama kuskure. Haka kuma ba za ka haramta wa kanka wani abu ba, sai idan Allah ne ya ce ka bari.

********************

Da faɗar Allah;
"Kuma haƙiƙa mun aiko a cikin kowace .al’urnma manzo, cewa ku bauta wa Allah kuma ku nisanci ɗagutu." (Nahl;36)
­_______________
SHARHI
 A nan wurin akwai abubuwa guda uku
          a. Rahamar Allah wajen turo Annabi ga kowace al’umma. Wannan yatabbata cikin wata ayar;
"Babu wata al’umma, face sai da aka turo mai gargadi a cikinta." (Faɗir:24)
Rahama ce daga Ubangiji turo manzo ga al’umma, don kada a kama su da abin da ba a hana su ba.
           b. Aiko Annabi a kan ya ce, "Ku bautawa Allah" Don nuna abin bautar guda ɗaya ne, a dukkan zamani.
           c. Ɗagutu shi ne duk abin da zai sa ka ƙetare iyakar Allah. Wannan abin mutum ne, aljan ne, kana tare da shi a zamaninka, ko ya wuce zamaninka, kana sani, wannan abin ya zama ɗagutunka. Ba wai sai ka taskace shi ka ajiye ba.
          Abin da wannan yake nunawa shi ne, musulunci bai yarda da haɗe- haɗe ba. Menene haɗe-haɗe? Ka haɗa musulunci da kiristanci, yahudanci, ko maguzanci, ka ɗan taɓa wannan, gobe wancan. Shi ya sa Allah (SWA) ya ce;
"To Wanda ya kafirce wa ɗagutu, kuma ya yi imani da Allah, to haƙiƙa ya yi riƙo da igiya mai ƙarfi, wacce ba ta tsinkewa." (Al-Baƙara:256)
Don haka, kalmar shahada ta ginu a kan ɓangare guda biyu:
    a. Kore bauta ga dukkan wani dangin abin bauta, ba Allah ba.
    b. Tabbatar da bauta ga Allah shi kaɗai.
Ka ga ya zama, Laa ilaaha illallaahu kenan.
********************
Da faɗinsa;
"Ubangijinka ya yi umarni (ya zartar) kada ku kuskura ku bauta wa kowa sai shi, iyaye guda biyu kuma, ku kyautata musu.” (Al-lsraa‘:23)
********************
Da faɗinsa;
"Ku bauta wa Allah (shi kadai), kada ku yarda ku haɗa shi da wani"
(An-Nisaa’:36)
********************
 Da faɗinsa;
“Ka ce, Ku zo (mutane) na karanta muku abin da Allah ya haramta muku. Kada ku yarda ku haɗa shi da wani !” (Al-An'aam: 151-153)
  Abdullahi ibn Mas’ud ya ce, “Duk Wanda yake so ya ga wasiyyar Annabi Muhammad (ﷺ)  Wadda ya sa hatiminsa a kai, to ya karanta fadin Allah Ta’ala, “Ka ce, “Ku zo (mutane) na karanta muku abin da Allah ya haramta muku. Kada ku yarda ku haɗa shi da wani!” har zuwa faɗinsa,“...haƙiƙa  wannan shi he hanyata daidaitacciya.”
”Cikin Suuratul An’aam, wasiyyar nan guda goma”
********************
   An karɓo daga Mu’az bin Jabal ya cc, “Na kasance a bayan Annabi (ﷺ)  a kan jaki,” sai Annabi  ya ce da ni,“Ya Mu’az:! Shin ka san haƙƙin da Allah yake da shi a kan bayi, kuma ka san haƙƙin da bayi suke da shi a wurin Allah?” Sai na ce, “Allah da Manzonsa su ne mafiya sani.” Sai Annabi ya ce, “Haƙƙin da Allah yake da shi bisa ga bayinsa, su bauta masa shi kaɗai, kada su haɗa shi da wani.
Amma haƙƙin da bayi suke da shi wurin Allah, Ubangiji ba zai azabtar da duk Wanda bai yi shirka ba.” Mu’az ya ce, “Ba na je na yi wa mutane bushara ba?” Sai Annabi  ya ce, “Kada ka ba su bushara, sai su dogara (da aikinsu).” [Bukhari #2856 da Muslim #30]
_________________
SHARHI
Wannan yana nuna ƙanƙan da kan Annabi (SWA), a matsayinsa na shugaban halitta, amma ga shi yana hawa jaki, kuma har ya goya wani a baya. Waɗanda suke samun irin wannan matsayin, ana ƙirga su a cikin waɗanda suka samu katafaren matsayi. Adadin waɗanda Annabi ya goya su a bayan jaki ko doki, a ƙirge suke a wurin sahabbai. Mu’az ibn Jabal na cikinsu.
 Abin da wannan hadisi yake nunawa shi ne, duk mutumin da ya mutu da tauhidi yana da matsayi guda biyu: -
      a. ko dai ba za a yi masa azaba gabadaya ba.
      b. Ko kuma a kama shi da azaba gwargwadon laifinsa, yadda sauran waɗansu hadisai suka nuna.
A nan malamai na yin bayani; akwai bambanci tsakanin haƙƙin Allah da haƙƙin bayi. Haƙƙin Allah dole ne sai sun yi shi, amma haƙƙin bayi da suke da shi Wurin Allah, hakki ne Wanda babu Wanda ya wajabta masa, shi ya wajabta Wa kansa don ganin damarsa, su kuwa bayi dora musu aka yi. Idan ka haɗa ayoyi da hadisai da suka zo a wannan babi, za ka fito da sakamakon cewa, mutane kashi uku ne, bayan an yi sakamako gobe ƙiyama: -
      a. ‘Yan aljanna tsantsa; za su shiga aljanna babu fita.
      b. ‘Yan Wuta tsantsa; wadanda idan sun shiga babu fita.
      c. Muminai, wadanda suka yi aiki nagari da aikin Barna. Waɗansu za a yi musu afuwa, wasu za a yi musu azaba a fito da su, ko kurna a yi musu azaba a duniya.
********************
A CIKIN WANNAN BABI AKWAI MAS’ALOLI KAMAR HAKA
1.   Hikimar halittar mutum da aljan.
___________
SHARHI
An halicce su ne don su bauta wa Allah, mun fahimci wannan ƙarƙashin ayar cikin Suurauz Zaariyat. Ashe kenan duk abin da Allah (SWA) ya yi, akwai hikima a cikinsa.
2.   Abin da ake nufi da ibada, shi ne tauhidi, don haka jayayya ma acikinta take.
­­­___________
SHARHI
Saboda duk ibada ba ta karɓuwa sai idan tauhidi ya cika. Sannan duk jayayyar da Annabawa suka yi su da mutanansu, sun yi ta ne a kan tauhidi. Ba Wanda ya sami rigima da mutanensa a kan sallah kozakka ko a kan wani abu face tauhidi. Da zarar mutane sun sallamawa tauhidi, to sauran abubuwan ma sai su bi. Idan an sami gardama a sauran abubuwa, to ba a sallamawa'tauhidi_ ba.
3.   Dukkan Wanda bai yi tauhidi ba, to bai bauta wa Allah ba. Kuma a ciki akwai ma’anar faɗIn Allah;
 “Kuma ku ma ba za ku zama masu bauta wa abin da nake bautawa ba.” [Al-Kafirun:3)
____________
SHARHI
Abin nufi, duk wanda ba shi da tauhidi, to duk ibadar da ya yi a banza. Mutum ya yi ta azumi, sallah, zikiri, salati, matuƙar babu tauhidi, to bai yi komai ba. Shi ya sa Allah a cikin ayar ya nuna cewa kafirai ba za su yarda su bautawa Allah ba, ko su yi masa yanka, ko wata ibada. Amma ga shi suna yanka a Makka suna ibada, to tun da ba tauhidi, sai ya zama kamar ba su bautawa Allah ba ne.                                           
4.   Hikimar turo manzanni”
”Shi ne don su tabbatar da tauhidi.”
5.   Manzanci ya shafi kowace al’umma (wato Allah ya turo wa kowace al’umma Manzo).
6.   Lallai addinin Annabawa iri ɗaya ne”
__________
SHARHI
Shi ne tauhidi. Don kowanne Annabi  ya ce da mutanensa  kar su bautawa kowa sai Allah. Duk waɗannan mas’aloli mun fahimce su a ayar Suuratun Nahl.
7.   Gagarumar mas’ala ita ce cewa, ibada ba ta yiwuwa, sai an kafirce wa ɗagutu. A ciki akwai ma’anar fadinsa;
“Duk Wanda ya kafirce wa ɗagutu ya yi imani da Allah.” (Al-Baƙara:256)
______________
SHARHI

Wato imani da Allah ba ya yiwuwa sai ka kafircewa ɗagutu. Kafircewa ɗagutu shi ne rashin ganin cancantar kowacce doka wadda ba ta Allah ba, a zuciyarka ka yarda wannan dokar ba ta cancanci ta shugabanci duniya ba. Ko da wannan dokar ita take jagorantar ka a ƙasarka, ka san a bias lalura ne, gobe ka sami dama za ka hankaɗar da ita. Amma idan ka sakankance cewa eh! 'Wannan dokar ta dace babu laifi, kamar yadda ta Allah ta dace, to duk ibadarka wallahi ta zama shirme! Dole sai zuciyarka ta yarda cewa duk abin da ba Allah ne ya ce ba, ko Manzon Allah ya ce ba, to shirme ne, bai cancanta ba ya mulki duniya kuma zalunci ne. Dukkan dokar da ba ta Allah ba, to azzalumar doka ce, domin zalunci shi ne sab abu a inda bai dace ba. Dukkan dokar da ba ta Allah ba, babban abin da ya fara kawo mata tangarɗa, shi ne jahilci. Allah shi ne cikakken mai ilmi kamar yadda ya faɗa:

 “Allah masani ne ga dukkan komai.” (Taghabun 11)
Amma ɗan Adam ba zai zamanto ya san komai ba, jahiltar wani ɓangare na rayuwa shi zai sa mai sanya doka ya sa dokar a wani waje inda ba ta dace ba. Sai ya yi zalunci maimakon adalci.
8.   Dagutu shi ne dukkan abin da aka bautawa, ba Allah ba.”
___________
SHARHI
Wannan sai ya nuna dukkan Wanda aka bautawa a da ko a yanzu matuƙar ba Allah ba ne, to ya zama dagutu. Malamai sake cawa idan har Wanda aka bautawa ya yarda da bautar. Don Annabi lsa (AS) da Annabi Uzairu (AS) da Mala‘iku duk ana bauta musu, amma "ba su yarda da bautarba, don haka su ba dagutai ba ne. ldan kuma aka bautawa abin da ba shi da hankali, kamar gunki, to a nan gurin dagutun shi shaiɗan. Don shi ya ƙawata maka gunki ka mai da shi abin bauta.
9.   Girman sha’anin ayoyi uku tabbatattu (muhkamat) na cikin Suurarul An’aam, a wurin magabata ba a shafe ba. A cikinta akwai mas’aloli guda goma Na farkonsu, hani game da shirka!
10.                     Ayoyi  tabbatattu (Waɗanda ba a shafe hukuncinsu ba) a cikin Suuratui  Israa  A cikinsu akwai mas’aloli guda goma sha takwas. Allah ya buɗe su da fadinsa, “Kada ka sanya wani abin bauta tare da Allah, sai ka zama abin zargi, taɓaaɓɓe....” Ya kuma cika ta da faɗinsa, “Kada ka sanya wani abin bauta tare da Allah, sai a‘ jefa ka cikin jahannama kana abin nisantarwa.” Kuma Allah, tsarki ya tabbata gare shi, ya faɗakar a kan girman sha’anin waɗannan mas’aloli da faɗarsa, “Wannan shi ma abin da Ubangijinka ya yi wahayi zuwa gara ka na hikima.”
11.                     Ayar da ke cikin Suuratul Nisaa’i. wadda ake ce mata ayar hakkoki guda goma, wadda Allah ya fara ta da cewa, “Ku bautwa Allah, kada ku yi tarayya da shi….“
12.                     Nuna mana wasiyyar Manzon Allah  yayin mutuwarsa.

13.                     Mun gane haƙƙin Allah a kanmu”
“Mu bauta masa shi kadai, ba tare da sanya masa kishiya ba.”
14.                     Mun gane haƙƙin bayi a wurin Allah, idan sun bayar da haƙƙinsa.
15.                     Cewa wannan mas’alar da yawa daga cikin sahabbai ba su santanba.
______________
SHARHI
Mu’az bin Jabal bai faɗi wannan hadisi ba sai da ya zo ƙarshen rayuwarsa da cutar ajali ta kama shi, sai ya ji tsoron kar ya mutu ya shiga cikin masu Boye ilimi, narkon azaba ta kama shi. Ashe kenan mas’alar tauhidi sahabbai ba su gane ta ba sai da aka karantar da su, tun da Annabi ya tambayi Mu’az ya ce bai sani ba, sai da Manzon Allah (ﷺ)  ya ilimantar da shi. Don haka ba a gane tauhidi da Zaƙin baki, dole sai da wahayi. Amma sauran abubuwa na ibada da mu’amalat za a iya yin ijtihadi amma banda tauhidi, shi dole sai da nassi ƙarara.
16.                     Ya halatta boye wani Bangare na ilimi domin maslaha.
17.                     Mustahabbi ne yin bushara ga musulmi da abin da zai faranta masa.
18.                     Jin tsoron dogaro bisa yalwar rahamar Allah (ba tare da yin aikiba.)
19.                     Faɗin Wanda aka tambaya idan bai sani ba da cewa ya ce, “Allah da Manzonsa su ne mafi sani.”
20.                     Halaccin kebance wani sashe na mutane da Wani ilimi ban da wanmsu.
21.                     Tawali’un Manzon Allah (ﷺ)  wajen hawan jaki, da yin goyo a kansa.
22.                     Halaccin yin goyo a kan abin hawa, Wato hawan mutum biyu.
23.                     Falalar Mu’az bin Jabal”
“Duk waɗannan mas‘aloli mun fahimce su a hadisin Mu’az bin Jabal (RA).”
24.                     Girman sha’anin Wannan mas’ala [ta tauhidi].


(FASSARA DA SHARHI DA GA BAKIN GARIGAYI SHEIK JA’AFAR MAHAMUD ADAM {R} ).  (zamuci gaba Insha Allah)


3 comments:

KITABUT-TAUHID (Babi Na Goma Sha Biyar15)

  SHARHI Babukan da suka wuce sun yi magana a kan yana daga dangin shirka neman taimako wajen wanin Allah. Wannan babi kuma zai nuna maka ...