An karɓo daga ɗan Abu Burda, daga
babansa, daga Abu Musal Ash’ariy (R.A) ya ce, Annabi (ﷺ), ya tura shi ƙasar Yemen, sai ya tambaye shi
dangane da wani abin sha da ake yi a can, sai ya ce, “Menene abin?” Sai ya ce,“Albit’u
da Almizru.” sai aka ce da Abu Burda, “Menene Albit’u?” sai ya ce,
wani tsimi ne da ake yi da
zuma, almizru kuwa wani tsimi ne da ake yi da alkama. Sai
Annabi (ﷺ), ya ce, “Duk abu mai sa maye
haramun ne.” Bukhari ne rawaito shi (#4343).
SHARHI;
Da manzon Allah (ﷺ), ya ce, “Duk abu mai sa maye haramun ne….” sai
malamai suka ce abin da yake sa maye abu biyu ne: Awai abin da yake sa maye, ya
kuma sa ka walwala da jin daɗi. Giya tana sa maye, tana sa walwala da jin daɗi,
wani farin cikin na babu-gaira-babu-dalili. To wannan giya kenan, ittifaƙin
haramun ne. Amma akwai abin da zai sa ka
maye ba walwala, suka ce wannan bai
zama haramun ba. Idan za ayi wa mutum aiki a asibiti, likitoci ai suna ɗirka
masa allura, ya ji bai san ida yake ba. A wannan lokacin ai ba shi da hankali!
Duk dangi an yarda bai san inda yake ba, shi ma haka bai san yadda yake ciki
ba, amma bambancinsa da ɗan giya, ɗan giya sha da gwangwajewa da yake yi, shi
kuwa ba ya cikin jin daɗi, yana cikin wahala. Akwai mgabatan da suke cewa duk
abin da yake sa maye, ko yasa walwala, ko bai sa walwala ba, shi ma haramun ne.
Waɗansu suna da wannan fatawar cikin manyan malamai da suka gabata, cikin
sahabbai da tabi’ai da tabi’ut tabi’in. A gaskiyar al’amari duk abin da zai sa
maye ɗin nan, wato na tilas ba na jin daɗi ba, ya ɗauke maka hankali, to wannan
ba giya ba ne, waɗanda suka haramta shi, galibi suna cewa ba ma so mu buɗe
ƙofa, in muka buɗe ƙofa ɗin sai mutum ya sa a kawo masa barasa ya sha. To
wannan shi ya sa suke haramtawa.
(FASSARA
DA SHARHI DA GA BAKIN GARIGAYI SHEIK JA’AFAR MAHAMUD ADAM {R} ).
No comments:
Post a Comment