An karɓo daga Umar ɗan Khaɗɗab
(R.A) daga Annabi yace, da ace kuna dogara ga Allah haƙiƙanin dogaro da Shi da Allah ya azurta
ku kamar yadda yake azurta tsuntsaye. Suna sammako da yunwa amma suna dawowa
da
yamma suna ƙoshe.
Imam Ahmad (# 01,52) da Tirmizi (#2344) da Nasa’i a cikin Sunnan Alkubra (J 8/
sh 79) da Ibnu Majah (#4164) da Ibnu Hibban ya inganta shi (730) da Hakin (418)
Tirmizi yace, hadisi ne ingantacce.
SHARHI;
Tsuntsu ba ya ajiye abincin gobe. In
yaje yau. Yayi kiwo shi kenan gobe kuma ya bar ta ga hannun Allah. A nan ba wai
ana nufin kada mu ma mu ajiye abincin gobe ba, ba haka hadisin yake nufi ba.
Abi da hadisin yake nufi ,irin yadda tsuntsu ya ɗauka cewa in ya fita da safe, Allah
zai bashi to lallai ka ɗauka cewa in ka fita ka nema, lallai Ubangiji na iya baka
irin yaddayake wa tsuntsu Ma’ana ya zamanto zuciyarka ta rayayu da cewa Allah
zai baka, ban daShi ba mai baka, kuma gaɓɓanka suna aiki tuƙuru don neman abin gurin Allah. Wannan shine tawakkalin da
ake so.
(FASSARA
DA SHARHI DA GA BAKIN GARIGAYI SHEIK JA’AFAR MAHAMUD ADAM {R} ).
No comments:
Post a Comment