An karɓo daga Abdullahi ɗan Amru
(R.A) daga Annabi (ﷺ), ya ce, “abubuwa
guda huɗu wanda suka kasance tare da shi ya kasance munafiki, wanda siffa ɗaya
ta kasance tare da shi daga huɗun nan, to lallai siffa ta munafinci na tare da
shi, har sai ya bar ta, idan yayi magana, ya zamanto ya yi ƙarya, Idan ya yi
alƙwari, sai ya
zamanto ya saɓa, Idan an yi rigima
dashi, sai ya ƙetare dokar Allah, idan kuma aka ƙulla alƙawari, to zai yaudare ka.
Bukhari (#34) da Muslim(#58) suka rawaito shi.
SHARHI;
Waɗannan siffofi guda huɗu in sun
taru ga mutum, to ya zama munafiki, in kuwa ɗaya ce, to wanan ya zama yana da
siffa ta munafunci.To amma abin da ake nufi da munafunci a nan gurin,
munafuncin aiki. Don munafunci iri biyu ne: akwai Annifaƙul Amali,
munafunci a
cikin aiki, da Kuma Annifaƙul I’itiƙadi, munafunci na zuci, wanda yake nufin
mutum ya bayyana musulunci a zahiri, amma a zuciyarsa yana nan kan addininsa na
kafirci. To duk mai wannan ba musulmi ba ne, ko da ya rantse. Don munafukai
masu irin wannan, sai da suka zo wajen Annabi (ﷺ), suka rantse suka ce sun yarda da shi amma
Allah ya ƙaryata su Allah yace,
اذا جاء ك المنفقون قالو انك لر سو ل
الله و الله يعلم انك لر سو له و
الله ان المنفقين لكذ بون ( المنا
فقون:
(Idan Munafukai suka zo wajenka,
suka ce, "Mun shaida kai Manzon Allah ne!” Allah ya san kai manzonsa ne,
Allah ya shaida haƙiƙa Munafukai ƙarya suke ) (Al-munafuƙun 1)
و من الناس من يقول ءامنا با الله
وباليوم الا وم هم ب مو منين: البقرة.
(A cikin mutane akwai waɗanda za su
ce, "Mun yi imani da Allah da ranar ƙarshe"alhali su ba Muminai ba
ne) [Al-Baƙara: 8]
To wannan shi ne munfuncin zuci,
ƙudure kafirci a zuciya, amma mutum yana bayyana musulunci a harshensa, wannan
ba musulmi ba ne, kuma irin waɗannan su ne Allah yace akansu,
ان المنفقون فى الدرك الاسفل من النار
ولن تجد لهم نص) النساء:
(Hakika munafukai suna ƙasan wuta,
kuma ba zaka sami wani mataimaki a tare da su ba.) [Annisa’i]
ان المنفقون بخد عو ن الله وهو خد عهم
و اذ قا مو الى الصوة قامو كسالى يراءون الناس ولا يذ كرو ن الله الا قليلا) النساء:
(Haƙiƙa munafukai suna yaudarar
Allah, Amma Allah yana mayar musu da yaudararsu akansu, idan suka tashi yin
sallah, sai su tashi suna kasala, suna yi (Sallar) don mutane su gani, ba sa
ambaton Allah, sai zan kaɗan) [Annisa’i:142]
Duk ayar da tazo ta nuna dawwama a
cikin wuta ga munafukai, to da irin waɗannan munafukai take.
Kashi na biyu shi ne, munafunci a
aikace, zuciyarka da imani, amma kana da wani aiki wanda bai kamata a ce kai
musulmi ne kake yi ba, aikin irin aikin munafukai ne. To irin wannan, idan
mutum ya yi, sai a ce ya yi aikin munafunci, amma ba ma cewa shi munafuki ne,
mu saukar da faɗin Allah a kansa, "Haƙiƙa munafukai suna ƙasan
wuta...." wannan ba ta shafe shi ba. Saboda kar mutum ya yi amfani da
wannan hadisin, ya kafirta ‘yan uwansa, ba tare da ya fahimta ba, dole sai ya
ware, Annifaƙul I’itiƙadi, wanda ya yi shi ya zama kafiri, amma Annifakul
Amali, duk wanda ya yi shi yana nan a matsayinsa na musulmi, amma fasiƙin
musulmi ne.
(FASSARA
DA SHARHI DA GA BAKIN GARIGAYI SHEIK JA’AFAR MAHAMUD ADAM {R} ).
No comments:
Post a Comment