Tauhidi, shi ne
ginshikin al’amari gabaɗaya. Domin tabbatar datauhidi ne Allah ya saukar da Iittattafai, kuma ya turo da
manzanni. Sallah, azumi, zakka, hajji, kyautatawa iyaye, kyautatawa makwabta da
duk Waɗansu
ayyuka na ibada, ba sa ingantuwa sai idan an gina su a kan tauhidi. Inda mutum zai ciyar da dukiya fan taɓa sama, Ubangiji ba zai karɓa ba idan ba shi da tauhidi.
ayyuka na ibada, ba sa ingantuwa sai idan an gina su a kan tauhidi. Inda mutum zai ciyar da dukiya fan taɓa sama, Ubangiji ba zai karɓa ba idan ba shi da tauhidi.
Abdullahi ibn
Jud’an, wani mutum ne mai karamci da ciyar da maƙwabta, a lokacin jahiliyya har
ya mutu bai karfii musulunci ba. Aisha (RA) take tambayar Annabi (SAW) cewa abin
da Abdullahi ibn Jud’an ya ciyar, ranar tashin ƙiyama zai tashi ya samu tsira?
Annabi (SAW) ya nuna cewa, duk abin da ya ciyar ba zai amfane shi ba ranar
tashin ƙiyama. [Duba Muslim #214]. Don haka a tauhidi ne ake gina kowane irin
aiki. Duk ibadar da mutum zai yi, ya yi ta zikin' da salatin Annabi, ya yi ta
hailala da istigfari, ya ciyar da miskinai, matuƙar ba shi da tauhidi wallahi,
Ubangiji (SWA) ba zai karƙa ba!
Abin da yake
nuna muhimmancin tauhidi shi ne, tauhidi ne kaɗai abin da duniya ta haɗu a kai,
tun daga Annabi Adam (AS) har i zuwa kan 'Annabi Muhammad (SAW). Daga Annabi
zuwa Wani Annabin akan sha bamban a yanayin ibada, tsakanin hukunce- hukuncen
tsarki, alwala da na ganima. Duk annabawa babu Wanda aka halattawa ganima da
taimama sai Annabi (SAW). Tsakanin Annabi Musa (AS) da Annabi Isa (AS) akan
samu an haramta wani abu a can kuma wannan ya zo da halacci. Kamar yadda Annabi
Isa (AS) ya fada:
{ ولأحل لكم بعض الذي حرم عليكم}
"Kuma zan
rika halatta muku wani sashi da ya zama haram a kanku (a cikin Attaura, yanzu
Injila ta zo da halacci).” (Aali-!mraan:50) Annabi Muhammad (SAW) da ya zo, sai
aka ce don ya sauƙaƙe dukkan tsananin da ke cikin waɗancan biyun.
Amma tauhidi
tun daga farkon Annabi, zuwa Karshe (ɗaya ne. Sallah, azumi, zakka suna iya
bambanta amma tauhidi iri ɗaya ne.
{ولقد بعثنا في كل أمة رسولا أن اعبدوا الله واجتنبوا الطاغوت}
"Kuma
hakika mun aiko a cikin kowace al’umma, manzo, cewa ku bauta wa Allah kuma ku
nisanci ɗagutu."(An-Nal;36)
Kuma ya ce:
{وما أرسلنا من قبلك من رسول إلا نوحي إليه أنه لا إله إلا أنا
فاعبدون}
"Ba mu taɓa
turo wa ba kafinka, wani manzo face mun yi wahayi zuwa gare shi, cewa lallai
babu abin bauta bisa cancanta sai ni, don haka ku bauta mini.” (AI-Anbiyaa:25)
Kowa da ya zo abin da ya sanarwa al’ummarsa kenan. Wannan a jumlace kenan. A
rarrabe kuwa dalla-dalla ga shi nan;
{ ولقد أرسلنا نوحا إلى قومه إني لكم نذير مبين{25 }أن لا تعبدوا
إلا الله }
"Hakika
mun turo Nuhu zuwa ga mutanensa, “Lallai ni a gare ku, mai gargadi ne, Wanda
yake mabayyani, Kada ku kuskura, ku bauta wa kowa, sai Allah shi kaɗai.”"(Huud:
25-26) Kowane Annabi haka ya tabbatar da Wannan da’awar. Abin da zai ja
hankalinka, shi ne, a cikin Suuratul Anbiyaa inda aka zana sunayen annabawa,
aka fara da Annabi Musa (AS) da Harun (AS):
{ولقد آتينا موسى وهارون الفرقان وضياء وذكرا للمتقين}
"Hakika
mun bai wa Musa da Haruna Alfurƙan sannan haské da kuma tunatarwa ga masu
takawa." (Al-Anbiyaa:48)
Da aka yi gaba kadan cikin kissar Annabi Ibrahim (AS) sai aka ce;
{قال أفتعبدون من دون الله ما لا ينفعكم شيئا ولا يضركم}
"Sai ya ce
shin yanzu kwa rika bautawa koma-bayan Allah, irin abin da ba zai amfane ku da
komai ba, kuma ba zai cutar da ku ba?" (Al-Anbiyaa:66)
Da aka gama
ƙissarsa, a can karshe sai aka kawo Luɗ (AS) aka. raɓa shi:
{ونجيناه ولوطا إلى الأرض التي باركنا فيها للعالمين}
"Kuma muka
tsamar da shi da Lud i zuwa ga kasa wadda muka yi rnata albarka a cikinta
saboda talikai."(A1-Anbiyaa:7l)
Sai aka haɗa
da:
{ووهبنا له إسحاق ويعقوب نافلة وكلا جعلنا صالحين}
"Kuma muka
ba shi Is'haƙ da Yakub a rnatsayin nafila, kowane ɗaya mun sa shi ya zarno
salihi." (Al-Anbiyaa72)
Da aka gama da
wannan, sai aka kawo Annabi Nuh (AS):
{ونوحا إذ نادى من قبل فاستجبنا له فنجيناه وأهله من الكرب
العظيم}
"Tuna wa
mutanenka ƙissar Nuhu, lokacin da ya yi kira, tun da, saimuka amsa masa, sai
muka tserar da shi da iyalansa daga bakin ciki mai girma." (Al-Anbiyaa:76)
'
Da aka gama da
wannan, sai Dawud (AS) da Sulaiman (AS):
{وداوود وسليمان إذ يحكمان في الحرث إذ نفشت فيه غنم القوم وكنا
لحكمهم شاهدين}
"Tuna wa
mutanenka ƙiissar Dawud da Sulaiman, yayin da suka yi hukunci su biyu dangane
da amfanin gona, lokacin da dabbobin suka kiwace shi da daddare, kuma mun
kasance masu shaida dangane da
hukuncinsu.” (Al-Anbiyaa:78)
Da aka gama da
su sai aka kawo Annabi Ayyub (AS):
{وأيوب إذ نادى ربه أني مسني الضر وأنت أرحم الراحمين}
"Tuna wa
mutanenka ƙissar Ayyub, lokacin da ya kirayi Ubangijinsa, "Cuta kam ta
shafe ni, kai kuma kai ne mafi jin Kan duk masgjin kai."(AI-Anbiyaa:83)
Sannan aka kawo
Isma’il (AS), Idris (AS), da Zhulkifl (AS):
{وإسماعيل وإدريس وذا الكفل كل من الصابرين }
“Kuma Isma’il
da Idris, da Zhulkifl, kowane ɗaya yana daga cikin masu hakuri.” (Al-Anbiyaa:85)
An gama da
Wannan, sai Zannun (ma’abocin kifi), shi ne Annabi Yunus (AS):
{وذا النون إذ ذهب مغاضبا}
"Da kuma
ma’abocin kifi lokacin da ya tafi yana mai fushi." (Al-Anbiyaa:87)
Daga nan sai
Zakariyya (AS) da Yahya (AS):
{وزكريا إذ نادى ربه
رب لا تذرني فردا وأنت خير الوارثين}
"Da kuma
Zakariyy, Iokacin da ya kira Ubangijinsa, "Ya Ubangiji! Kada ka bar ni
tilo, kai ne fiyayyen masu gadarwa, "(A1-Anbiyaa:89) Sai aka kawo Annabi
Isa (AS) ta hanyar izina.
Duk da aka gama
sai aka cc:
{إن هذه أمتكم أمة واحدة وأنا ربكم فاعبدون}
"Lallai
wannan, al’ummarku ce, al’umma guda ɗaya, kuma ni ne Ubangijinku, don haka ku
bauta mini (Al-Anbiyaa:92)
Manufarsu duk
guda ɗaya ce. Don haka da’awar annabawa duka a kan tauhidi take. Shi ne abin da
idan ya gyaru sauran ayyuka sun gyaru. Idan ya rushe sauran ayyuka sun rushe.
Shi ya sa koyar da tauhidi ya zama wajibi.
A Kur’ani an
fara kira da tauhidi, aka saukar da wasu surorin da babu komai a cikinsu sai
tauhidi. Aka yi shekara goma sha uku (13) a Makka babu abin da ake kira sai abu
guda biyu, tauhidi da akhlaƙ. Sai sallah da aka shar’anta a daren Isra'I, amma
sauran hukunce- hukunce sai da aka zo Madina. Abu na ƙarshe da ya sauka, Wajen
tabbatar da tauhidi ne:
{واتقوا يوما ترجعون فيه إلى الله ثم توفى كل نفس ما كسبت وهم
لا يظلمون}
"Kuma ku
tsoraci wani yini da za a mayar da ku zuwa ga Allah a cikinsa, sannan kowace
rai, a cika mata abin da ta aiwatar na aiki, su ba za a zalunce su kornai
ba."(Al-Baƙara:281)
Karshen ayar da
ta sauka kenan cikin AIkur’ani. An fara da tauhidi an rufe da tauhidi!
Haka kuma,
tauhidi shi ne abin da yake haɗa al'umma. Wallahi, duk yadda ka yi ka haɗa kan
al'umma a kan wani abu daban, Wata ƙa’ida daban saɓanin tauhidi, ba za ka iya
ba. Jam’iyyar siyasa ba za ta iya ba, Wani tsarin mulki (constitution) ba zai
iya hada su ba. Wata dabara da za a yi wa aya, duk ba zai fitar da rnutane ba.
Sai ka sa a zuciyar kowa ya ji ba ya jin girma ko kimar Wani abu sama da Allah
(SWA) da Manzon Allah (SAW). Ba Wanda ya isa ya talauta Wani, ko ya cutar da
shi, sai Allah (SWA). Sannan idan ni'ima ce, ba Wanda ya isa ya kawo ta, sai
shi. Sai duk duniya ta yarda da haka, to sai kai ya haɗu. Idan kuwa duniya ba
ta yarda da Wannan Ka’idar ba, kowa ya zaɓi Wanda yake ganin zai fisshe shi, to
ba za a taɓa haɗuwa ba.
Misali, lokacln
da aka turo Annabi (SAW) ya samu Larabawa, Kasa ta hada su, launin fata da yare
ya haɗa su, suna magana da harshe ɗaya, amma ko da a cikin garin Makka, kowane
dangi babu ruwansa da ɗayan. Aws da Khazraj a Madina, shekara arba’in suna yaki
da juna, asalinsu guda daya ne, daga Yemen suka taso suka dawo Madina, a
sakamakon rushewar farko ta Dam a tarihi, Wato Ma’arib. A cikin Suuratus Saba
’Allah ya ba da labarin. Babu Wanda ya sasanta su sai Annabi Muhammad (SAW) da
ya kawo tauhidi.
Idan ka duba
tarihin Larabawa babu abin da suka yi Wake a kai sai rigima. Babu Wanda bai yi
Waka a kan faɗa ko rigima ba. Waƙoƙin, idan an tara gabadaya, a kan rigima ne.
Idan ka ɗauki Waƙar Amru ibn Kulthum, shi ma rigima ne da faɗa, yana hakaito
yaƙe-yaƙen da suka yi da sauran mutane. Ba su da Wani addini sai faɗa, giya, da
neman mata. Amma addini ya zo gabaɗaya ya haɗa kansu.
Don haka Allah
(SAW) ya tunasar da Annabi (SAW), ya ce da shi :
{وألف بين قلوبهم لو
أنفقت ما في الأرض جميعا ما ألفت بين قلوبهم ولكن الله ألف بينهم إنه عزيز حكيم}
"Kuma ya
sanya soyayya a tsakanin zukatansu. Da za ka ciyar da abin da yake cikin ƙasa,
gabaɗaya, da ba ka sanya soyayya a tsakanin zukatansu ba, amma kuma Allah ya
sanya soyayya a tsakaninsu. Lallai shi mabuwayi ne mai hikima."(Anfal;63)
Don haka
tauhidi shi zai gyara al'umma. Yau duniya tana bukatuwa i zuwa ga tauhidi irin bukatuwar
da ta yi kafin turo Annabi (SAW). Domin a lokacin, duniya na cike da rigima.
Farisawa da Rumawa a lokacin su ne duniya, suna faɗa da juna. Yahudu da nasara
suna faɗa da juna. Larabawa a karan kansu suna faɗa da juna. Sai da Annabi
(SAW) ya zo, Kur’ani ya sauka aka warware rikicin Makka, aka je Madina aka
warware gaba ɗaya rikicin Madina. Haka kuma, aka warwarc rikicin ƙasashen
(Gufl) gabas ta tsakiya. Daga nan sai musulunci ya sauka a kasar Sham (suna
Karkashin daular Rumawa) aka gama da su, aka je har Rum. Sannan musulunci ya yi
arewa ya kusa ya shiga Iraƙ, aka gama da nan, aka shiga aka karya daular
Farisawa, sai da musulunci ya haɗe duniyar bakiɗaya. Shugabanci ɗaya take bi.
Ba a taɓa samun haɗin kai a duniya ba irin wannan lokacin. Me ya kawo wannan haɗin
kan? Wallafar wani ne? ko dabarar wani ce? A’a, tauhidi aka tsayar sai kan kowa
ya haɗu.
Haka kuma,
duniya yau ta shiga rikici sakamakon raunin tauhidi. Babu inda ba a fada;
Afrika ta yamma, kudu, da ta tsakiya, rigima! Kasashen Larabawa rigima!
Kwantacciya tsakanin Saudiya da Yemen, tsakanin kasashen Larabawa da Iran,
yanzu kuma da lrak. Tsakanin Iran da Bahrain. Su kansu Turai ba su zauna lafiya
ba. Tsakanin Croatia da Serbia rigima! Northem Ireland, ‘Cambodia, rigima!
Tsakanin Korea ta Arewa da ta Kudu, rigima! India da Pakistan rigima! Ko’ina
ana bala’i! Majalisar dinkin duniya tana nan, majalisar haɗin kan ƙasashen
Afrika tana nan, kungiyar hadin kan Kasashe rainon Faransa da rainon Ingila
suna nan, ƙungiyar hadin kan Larabawa tana nan, majalisar zartarwa ta kasashen
(Gulf) gabas ta tsakiya tana nan. Dukkansu babu abin da suka tsinanawa duniya,
kuma babu abin da za su tsinana. Babu abin da zai kawar da rikicin duniya sai
tauhidi. Daga nan za ka gane muhimmancin
tauhidi.
Don haka,
tauhidi yana bukatar karatu na nutsuwa don shi ne zai Warwarewa al’umma dukkan
matsalolinsu, ya tabbatarwa da al’umma arzikin duniya da na lahira.
FASSARA DA SHARHI DAGA MARIGAYI
SHEIK JAFAR MAHAMUD ADAM (RAHIMULLAH)
No comments:
Post a Comment