GABATARWA.



WWW.TAFARKINSUNNAH.BLOGSPOT.COM

WANNAN SHAFI YANA DAUKE DA HADISAN ANNABI(SAW)ACIKIN HARSHEN HAUSA. IDAN ANGA MUNYI KUSKURE ASANAR DA MU.ALLAH YAYI MUNA JAGORA AMEEN!



DAMIN AIKO DA GYARA KO KARIN BAYANI;
{tafarkinsunnah@gmail.com]

Sep 12, 2011

ARBA'UNA HADITH (6) HADISI NA SHIDA

An karɓo daga Abu Abdullahi, Nu'uman ɗan Bashir, (R.A) ya ce, "Na ji Manzon Allah () yana cewa, "Lallai halal a bayyane take, kuma lallai haramun a bayyane take, amma a tsakaninsu akwai al'amura masu rikitarwa, da yawa daga cikin mutane ba su san su ba. Duk wanda ya nisanci abubuwa masu rikitarwa, haƙiƙa ya nemi kuɓutar da addininsa da mutuncinsa. Wanda ya auka cikin abubuwa masu rikitarwa, to ya auka cikih haram. Kamar makiyayi ne da yake kiwo a gefen shinge, ya kusanta ya shiga (ya yi kiwo) a cikinsa. Ku saurara! Kowane sarki yana da iyaka. Ku saurara! Iyakar Ubangiji ita ce abubuwan da ya haramta. Ku saurara! Lallai a cikin jiki akwai wata tsoka, idan ta gyaru, dukkan jiki ya gyaru, idan ta lalace, dukkan jiki ya lalace. Ku saurara! (Wannan tsokar ɗaya) ita ce zuciya."
Bukhari #59 da Muslim (#1599).

SHARHI
Ma'ana, halal a bayyane yake a cikin Alƙur'ani da hadisai tabbatattu daga Annabi (), haka kuma haramun a bayyane yake a cikin Alkur’ani da hadisai tabbatattu daga Annabi (), amma a tsakanin halal da haram, akwai
waɗansu al'amura masu rikitarwa: Su ba su da siffa ta halal tsantsa, ballantana mu sa su a layin halal, ba su da siffa ta haram tsantsa, ballantana mu sa su a layin haramun. Akwai waɗansu daga cikin siffofinsu sun yi kama da halal ta wani ɓangare, ta wani ɓangaren kuma sun yi kama da haram, don haka sai suka zamanto masu kama da juna, ko masu rikitarwa, ta yadda ba ka san a ajin da za ka ajiye su ba. “aɗannan abubuwa masu rikitarwa, da yawa daga cikin mutane ba su san su ba, ba su san hukuncinsu ba. Wannan yana nuna akwai waɗansu kaɗan cikin mutane sun san su, su ne malamai tabbattu a cikin ilimi, su ba su da rikici a cikin abin, da sun ga abin za su gane. Amma da yawa cikin mutane za su rikitar da su, su kasa gane wane aji ya kamata su ba su. [Duba Jami'ul Ulum Wal-Hikam Na Ibnu Rajab 1/181]

A nan wurin abin da malamai suke cewa shi ne, akwai abubuwa da dama da asalinsu ana ɗaukar su a halal ne, ba ka da damar ka cire su daga halacci, sai da nassi, akwai kuma abubuwan da ake ɗaukar su a matsayin haramci, ba ka da damar ka cire su daga haramci, sai da nassi, Kamar misalin duk wani dangin abinci wanda zai karɓi sunan aɗɗayyib, wanda kuma bincike ya nuna ba ya cutar da tunani, ba ya cutar da lafiyar jiki, ba ya cutar da hankalin ɗan Adam, ba ya gurɓata masa tunani, to wannan abin halal ne. Idan ka ba da fatawa a kan halaccinsa, ba a bin ka bashin dalili, duk wanda ya bi ka bashin dalili, bai san abin da yake ba. Amma in wani ya zo ya yi da'awar haramci kan abin da yake yana cikin aɗɗayyiba, to wanda ya yi da'awar haramcin, shi ne aa a ce ina dalilinsa? Saboda haka, asali dangane da abinci ko abin sha, matuƙar ya zama ba ya cutar da jiki, ko hankali, to ya zama ɗayyib, shi kuma halal ne, Allah ya ce;
(Ka ce an halatta muku dukkan dangin abinci ki abin sha wanda yake daddaɗa) [Suratul Ma'ida 4].

Asali kuma cikin dukkan abinci ko abin sha wanda zai cutar da hankali, ko zai cutar da lakar jiki, yana shiga cikin babin haramun, idan ka ba da fatawa da haramcinsa, ba ka neman dalilin da zai ƙarfafa maka fatawarka. Sai dai zai iya yiwuwa ka samu wani abu da ba ya cutarwa a jiki ko a hankali, amma duk da haka haram ne, saboda ba mallakarka ba ne, sato shi ka yi, ko kwato shi ka yi. To a nan wurin sai ya zama ya tashi daga suna halal, ya zama haram.

Waɗannan al‘amura masu rikitarwa, malamai sun yi maganganu a kansu: Waɗansu suka ce kamar a sami wani abu wanda nassi guda biyu suka zo a kansa, ɗaya nassin yana nuna halaccinsa, ɗaya nassin yana nuna haramcinsa, kuma mun kasa tantance wanne nassi ne ya riga zuwa, ballantana mu ce nassin ƙarshe ya shafe na farko. Wato an sami Annasikh Wal Mansukh! To wannan yana cikin al'amura masu rikitarwa, in mun ce halal ne, ga wani nassin can ya ce haramun ne, in mun ce haramun ne, ga wani nassin can ya ce halal ne! [Don karin bayani duba: Jami‘ul Ulum Wal-Hikam Na Ibnu Rajab 1/183]. Amma idan ka je wajen malamai masu zurfin ilimi sai su ce, wancan nassi na farko da ya ba da halacci, nassi ne na Makka, wancan nassin ɗayan da ya ba da haramci, nassi ne na Madina, na Madina ya shafe na Makka, don haka ya zama haramun.

Waɗansu suka ce "....al'amura masu rikitarwa...." da aka ambata a wannan hadisin, sun ƙunshi sabon abu da zai faru, wanda bai taɓa faruwa ba lokacin Annabi () a yanzu kuma sai muka kasa sanin a ina za mu ajiye shi. Ya yi kama da halal, ya yi kama da haram, kuma mun kasa sanin a ina za mu ajiye shi? To irin waɗannan su ne, "....al‘amura masu rikitarwa....", kuma suna buƙatar malamai masu zurfin ilimi, masana game da nassosin shari'a, masana game da abin da ke faruwa a duniyar yau, a zamanin yau, sai su haɗa nassosin shari'a da sababbin abubuwa da ke faruwa don a san wane irin hukunci ya kamata a ba su.
Faɗin Manzon Allah () cewa, "....Duk wanda ya nisanci abubuwa masu rikitarwa, to haƙiƙa ya nemi kuɓutar da addininsa da mutuncinsa...." yana nuna kai musulmi, yayin da duk ka ga wani abu wanda ba ka iya tantance halacci ko haramcinsa ba, ya rikitar da kai, to a nan tsira da addininka, tsira da mutuncinka, shi ne ka bar wannan abin. Yayin da duk abu ya rikitar da kai, sai ka guje shi gaba ɗaya don ka kuɓuta da addininka. Misali kai ne kake da wani samfuri na takalmi, sai ka zo ka shiga masallaci, da ka fito, sai ka nemi takalminka ka rasa, can sai ka hangi wani takalmi inda ba nan ka ajiye naka ba, da nisa daga inda ka ajiye naka. Amma da ka je sai ka gan shi kamfani ɗaya, ƙira ɗaya, ƙila har sabunta iri ɗaya da naka, sai dai in da matambayi zai tambaye ka, shin kana da tabbas wannan takalminka ne? Za ka iya rantsewa kan takalminka ne? Za ka ce "Eh! Irinsu dai ɗaya da nawa, amma ba zan iya ba ka tabbas cewa nawa ne ba." To wannan ya shiga cikin "....al'amura masu rikitarwa...." Idan kana da tabbas ɗin naka ne, ko kana da yaƙini cewa mai wannan shi ya ƙauki naka, in kana da yaƙinin wannan, to dama-dama, ka iya ƙauka ka riƙe kafin ka je ka yi bincike, amma in ba ka da wannan yaƙini, ba ka da wannan tabbas ɗin, zato ne kake da shi, ba za ka gina hukunci kan zato ba.

Na biyu suka ce, kamar yara ne guda biyu 'yan tagwaye mata, aka haife su a gida ɗaya, ɗaya daga cikin yaran matan, kun yi tarayya da ita wajen shan mama. Ma'ana mace ɗaya ta shayar da ku, kai da ita. Ka ga ya zama tabbas wannan ta zama haram, ba za ka aure ta ba, saboda an shayar da ku, sai aka mai da ita gidansu, bayan an yaye ta, ta girma tare da 'yar uwana wacce aka shayar da ita a wani gida na daban. Da suka girrna, sai ka ga ɗaya daga cikinsu kana so, amma da aka zo bincike sai aka kasa gane wacce ce kuka sha nono tare da ita, wacce ce ba ku sha tare da ita ba, tunda ga shi Hasana da Usaina ne gida ɗaya suka taso. Wacce aka samu tabbas ba ku sha tare da ita ba, ya halatta ka aure ta, wacce aka samu tabbas kun sha mama tare da ita, bai halatta ba ka aure ta. Yanzu kuma ba ka da tabbacin da za ka tantance wannan. Abin da ya kamata ka yi, sai ka bar su duka biyun, ka je wani gidan ka yi aure. Wannan shi ne zai tabbatar da ka kuɓutar da addininka, ka kuɓutar da mutuncinka, ba ka faɗa cikin abin da Allah (SWA) ya haramta maka ba.

Shi kuwa faɗin Manzon Allah () cewa, "....Wanda ya auka cikin abubuwa masu rikitarwa, to ya auka cikin haram...." da shi ne malamai suke cewa duk abin da ya rikitar da kai, ka kasa gane halaccin ko haramci, to nisantarsa shi ne addini. Ka nisanci abin gaba ɗaya don ka huta wa kanka, don idan ka afka ciki, mai yiwuwa ka iya afkawa cikin haram, ba tare da ka sani ba. Kamar makiyayi ne da yake kiwo a gefen shinge, wato iyaka. Duk makiyayin da ya zo dabarsa na cin ciyawar da ke kan iyaka, idan dabbar nan ta cinye ciyawar da ke kan iyaka, to za ta shiga cikin gona ne kai tsaye. To tun asali da ta je iyaka, sai ka hana ta. Duk abin da yake kusa da haram, mafi kyau ka nisance shi, saboda kusantarsa, shi ne zai iya aukar da kai cikin haramun gaba ɗaya tsundum.
A gaba sai Manzon Allah () ya ce, "....Lallai kowane sarki yana da iyaka...." ta ikonsa, yana da iyakar ƙasarsa, iyakar da Ubangiji ya ɗora, ba ya son a ƙetare ta, shi ne, "....abubuwan da ya haramta...." Ma'ana, yadda ka san sarki ba zai so ka shigo ƙasarsa ba, to haka Ubangiji Ta'ala ba ya son ka ƙetare abin da ya haramta maka: Abin da duk ya haramta, mafi kyau ka nisance shi, kar ka kusanci inda yake. Dukkan abin da yake mai rikitarwa, to ana so muturn ya nisance shi, saboda ya tabbatar da kariyar mutuncinsa. Shi ya sa wata rana Annabi () yana i'itikafi a masallaci, sai matarsa Safiyya ta kawo masa ziyara. Bayan ta daɗe tana hira da Annabi (), sai ta tashi cikin duhun dare za ta tafi, sai Annabi () ya ce, "Mu je in raka ki, zuwa ƙofar masallaci." Ya raka ta har wajen masallaci, sai ga waɗansu mutane guda biyu daga nesa. Sun gane Annabi ne, amma ba su san waccce wadda Annabi () yake tare da ita ba, sun dai gan shi da wata mace. Da suka ga haka, sai suka ja baya, za su tafi. Sai Annabi () ya ce, "Ku tsaya, inda kuke!" Suka tsaya. Ya kama hannun matarsa, suka je, ya ce, "Ni ne Muhammad Rasulullahi, wannan kuma Safiyya ce, matata. Sai suka ce, "Ya Annabin
  (2)Hadisi Na Shida

Allah! Me ya kawo haka? Ai ba za mu munana zato gare ka ba," Sai ya ce, "A'a! Shaiɗan na gudana cikin jikin ɗan Adam. Duk inda jini yake zirga-zirga, Shaiɗan yana shiga, sai na ji tsoron kada ya jefa muku wani sharri a cikin zuciyarku." [Duba Bukhan' (#2035) da Muslim (#2174)]. Ka ga wannan shubuha ce ta faru, don wani na iya zuwa ya ce ya gan shi da wance, sai ya yi maza ya kare kansa, ya nuna cewa matarsa ce.
Haka kuma Anas ɗan Malik za shi masallacin juma'a, ashe ya makara bai sani ba, yana fitowa, ya kusa zuwa masallaci, sai ya ga ana dawowa, an gama sallah a masallaci. A matsayinsa kuma, idan waɗansu suka gan shi, za su ce, ka ga ma ko juma'a ba ya zuwa, sai ya ruga a guje, ya sami wani lungu ya Buya. Don kar ya tsaya a inda za a gan shi wurin tuhuma, a ce ga shi ma yanzu yake zuwa masallaci, yanzu ya zo, ƙila ba ya son ya bi limamin ne, ƙila kaza ne, ƙila kaza ne! Don ya kore wa kansa wannan tuhumar, sai ya ɓuya bai flto fili jama'a sun gan shi ba.
Faɗin Manzon Allah () cewa, "....Lallai a cikin jiki akwai wata tsoka, idan ta gyaru, dukkan jiki ya gyaru". idan ta lalace, dukkan jiki ya lalace. Ku saurara! (Wannan tsokar ɗaya) ita cc zuciya." yana nufin, ba abin da ke sa a shiga aljanna sai gyaruwar zuciya, ba gyaruwar jiki ba; ba abin da ke sa a shiga wuta, sai lalacewar zuciya, ba lalacewar gangar jiki ba. Ka rasa hannu, ko ka rasa ƙafa, ko ka rasa ido, in dai zuciyarka a raye take da imani, wannan ba abin da zai kawo maka cikas wajen shiga aljanna ba ne, kuma ranar alƙiyama duk sai an mayar ma da gaɓɓanka kamar yadda suke lafiyayyu. Ko gurgu sai an tayar da ƙafarsa ta mike, saboda zuciyarsa ta rayu da imani, sai a gyara jikinsa gaba ɗaya. Amma kana da dafin zuciya, shirka ta mamaye zuciyarka ta ko'ina, ga laflyar gaɓɓai, wannan ba abin da zai hana mutum ya shiga wuta. Shi ya sa Allah ya ce,
(Ranar da dukiya da ‘ya'ya ba sa amfani. Sai wanda ya je wa Allah da zuciya lafiyayya) [Asshu'ara 88-89]
A nan Allah (SWA) bai ce, "Sai wanda ya zo da jiki lafiyayye." ba, cewa ya yi, "Sai wanda ya zo da zuciya lafiyayya." warkakkiya, wankakkiyar zuciya, tatas, babu hassada, ba ganin ƙyashi. To dangane da gyaruwar zuciya kuwa, zuciya ba abin da zai gyara ta, sai bin abin da Allah ya saukar na wahayi, sai sunnonin Annabi (). Kullum ka yi ƙoƙarin raya zuciyarka da Alƙur'ani mai girma, ka yi ƙoƙarin raya zuciyarka da sauraron hadisan Annabi ().

1 comment:

KITABUT-TAUHID (Babi Na Goma Sha Biyar15)

  SHARHI Babukan da suka wuce sun yi magana a kan yana daga dangin shirka neman taimako wajen wanin Allah. Wannan babi kuma zai nuna maka ...