GABATARWA.



WWW.TAFARKINSUNNAH.BLOGSPOT.COM

WANNAN SHAFI YANA DAUKE DA HADISAN ANNABI(SAW)ACIKIN HARSHEN HAUSA. IDAN ANGA MUNYI KUSKURE ASANAR DA MU.ALLAH YAYI MUNA JAGORA AMEEN!



DAMIN AIKO DA GYARA KO KARIN BAYANI;
{tafarkinsunnah@gmail.com]

Sep 14, 2011

ARBA'UNA HADITH (9) HADISI NA TARA

An karɓo daga Abu Huraira Abdur-Rahman ɗan Sakhrin (R.A), ya ce, na ji Manzon Allah () yana cewa, "Duk abin da na hane ku (da bari), to ku nisance shi. Abin da na umarce ku da shi, to ku zo da shi (wannan abin) gwargwadon iko. Abin da ya hallakar da waɗanda suke kafin ku, yawan tambayoyinsu, da saBawarsu ga Annabawansu."Bukhari (#7288) da Muslim (#1337) suka rawaito shi.

SHARHI

Wannan hadisi, an karɓo shi daga Abu Huraira, Iimamin masu hadisi cikin sahabban Annabi (). Sunansa shi ne Abdur-Rahman bin Sakhrin Addausiy. Malamai sun yi
saɓani wajen sunansa, amma wannan shi ne mafi inganci. Ya musulunta a shekara ta bakwai bayan hijirar Annabi (), amma tare da haka, ya haddace hadisai masu ɗimbin yawa cikin hadisan Annabi (). Abu Huraira ya ce, da ya zo Madina (da ma ba ɗan Madina ba ne) sahabbai waɗansu suna gonakinsu suna noma, waɗansu suna tafiya kasuwa, ya ce, "Ni kuwa abin da nake buƙata, in sami abin da zan ci kawai. In na sami abin da zan ci a wannan yinin, sai in zo in zauna a wurin Annabi (), ba na rabuwa da shi, duk abin da ya faɗa na riɗe." Har wata rana Annabi () ya sa ya shimfiɗa mayafinsa, da ya shimfida mayafinsa, Annabi () ya ce, "Daga yau ɗin nan, duk abin da ka ji daga bakina, ka haddace shi kenan. ɗauki mayafinka ka tafi!" Ya ɗauki mayafinsa ya yafa a jikinsa. Tun daga ran nan ya ce, "Duk abin da ya fito daga bakin Annabi () na haddace shi." [Duba Bukhari (#118, 119) da Muslim (#2492)]. Shi Abu Huraira, ba ya noma, ba ya kasuwanci. Ya ce, yana nan, duk abin da Annabi () ya faɗa ya riƙe. Ba don komai ba, sai don saboda ya sanar da al'umma wannan abin. Ya ce, "Sau da dama mutum zai fito daga masallaci, sai in bi shi ina tambayarsa fassarar wata aya, in bi shi ina tambayar sa wani hadisi, ba wai don ban san ayar ko hadisin ba, kila ma na fi shi sani, amma don saboda ko ya yi min tayi, ya ce, "Zo mu je gidana mu ci abinci." Shi dai ba zai ce masa, "In zo gidanka in ci abinci?" ba. [Duba Bukhari(#6452)].

Dangane da faɗin Manzon Allah () cewa, "Duk abin da na hane ku (da bari), to ku nisance shi... ,wannan da ma, duk abin da shari'a ta yi umarni iri biyu ne Ko abin da yake umarni ne ko abin da yake hani. To sai dai malamai suka ce, aikata abin da aka hana, ya fi girman laifi, sama da ka yi sakaci wajen ƙin aikata umami. Suka ce hani ba sassauci, tunda Annabi () ya ce, " Duk abin da na hane ku, ku nisance shi..,." bai ce kar ku yi shi ba, sai ya ce, "....ku nisance shi." ba ma ku kusanci wurin abin ba. Amma a wajen umarni, sai ya ce "....to ku zo da wannan abin gwargwadon iko...." [Dubaz Jami'ul Ulum Wal Hikam Na Ibnu Rajah 1/246]. Asalin sallah ka yi a tsaye, idan ba ka da lafiya, sai ka yi a zaune, ya halatta, in rashin lafiyar ya yi tsanani sai a kwance za ka iya yi, sai ka yi a kwancen, ya halatta. Asalin sallah shi ne ka fuskanci alƙibla. Amma sai ka zo baƙunta wani garin da ba ka san alƙibala ba, kuma ba ka samu wanda za ka tambaya ba, to duk inda ka ga dama ka yi sallah, ya halatta. Ko da yake akwai malamai da suke cewa ka yi sallah huɗu Ka kalli nan, ka kalli nan, ka kalli nan. Sai dai a nan, an tsananta da yawa! Abin da shari'a ta wajabta maka, shi ne, ina ne inda ka nutsu cikin zuciyarka cewa nan ne alƙibla, ko da ba nan ba ne ka yi sallah, ta wadatar, ba sai ka yi sallah huɗu ba. Haka nan lokacin sallah ya kusa fita, saura kaɗan, ba ka sami ruwan alwala ba, ko ruwan wanka, ba ka sami ƙasar da za ka yi taimama ba, sai ka yi sallah a haka, kada ka ce sai ka je nernan ruwan har lokacin sallah ya fita baka yi ba. Wannan kuskure ne! Allah yana cewa,

(Haƙiƙa sallah (ta kasance) a kan muminai, farilla mai ƙayyadajjen lokaci) [Annisa'i: 103].

Da Manzon Allah () ya ce, "....Abin da ya hallakar da waɗanda suke kafin ku, yawan tambayoyinsu....", tambaya a nan, akwai wacce ta halatta, akwai wacce ba ta halatta ba: Tambaya irin wacce ta halatta, ita ce irin wacce kake son ka fahimci wani

abu na hukuncin shari'ar musulunci, wanda ka jahilce shi. Irin wannan tambayar, wajibi ne ka yi ta! Allah ya ce,

(Ku tambayi ma'abota sani, in ba ku sani ba) [Al Anbiyya: 7]. In ba ka san abu ba, wajibi ne ka tambaya, kafin ka aikata shi Amma irin tambayar da mutanen Makka suke yi wa Annabi (), sun tambaye shi abin da suka san ba zai iya yi ba, su ce sai ya yi. Kamar yadda suka riƙa faɗa a aya ta 90 cikin suratul Isra'i.

(Suka ce ba za mu yi imani da kai ba har sai ka ɓuɓɓugo mana da idaniyar ruwa daga ƙasa) [Isra‘i: 90].

Ka ji abin da suka gindaya: Wai sai an fitar musu da maremarin ruwa yana gudana a cikinta, da kuma Korama a cikin sahara, inda ba a tsammanin ganin ruwa; ko kuma ya kasance, ka rufto mana da sama, kamar yadda kake faɗa; ko ka kasance kana da gida na zinare da azurfa, bulo ɗin da simintin, da fentin, da komai da komni na zinare; ko kawai mu ga an turo maka wata matattakala, ka tattaka kana hawa sama. Suka ce, "Ko da mun ga kana tattataka wa ɗin nan fa, ba za mu yi imani da hawan da ka yi sama ba, har sai ka sauko da wani littafi, ka ba mu muna karanta wa, mun ga an cebkai Manzo ne zuwa gare mu." To irin wannan tambayar, ita Manzon Allah () yake nufi da ya ce, "....Abin da ya hallakar da waɗanda suke kafin ku...." shine yawan tambayoyinsu. In ka ji an zargi tambaya a cikin nassin Alƙur'ani ko nassin hadisi, to irin wannan tambaya ake zargi, don ba tambaya ce ta neman fahimta ba. Haka kuma yana cikin tambayar da malamai ke zargi, shi ne ka tambayi abin da bai da amfani, ka riƙa tambaya a kan wasu al'amura da suka faru a baya, wanda bayaninsu bai zo ba ko a nassi, sai dai an kawo su a jimlace, kai kuma ka dinga neman bayaninsu dalla-dalla. Kamar alƙaluman da aka yi takara lokacin da aka kawo Maryam wajen ɗaliban Zakariyya, kan cewa waye zai riƙe ta. To sai wani ya zo ya tambaye ka, wannan alƙaluman na meye? Da kara aka yi su? Karan gero ko dawa? Ko gamba ce? Ko menene? Farare ne ko baƙaƙe ne? Yanzu in ka san wannan, me zai ƙara maka, kuma in ka jahilci wannan, mai zai rage maka? Duk wannan ba su da amfani! Ko bayanin cewa lokacin da Fir'auna ya bi Annabi Musa da runduna dubu nawa ya tafi da ita? Sannan wane irin sirdi ya ɗora wa dokinsa? Sannan dokin baƙi ne ko fari ne ko ja ne ko wankan tarwada ne? Me za ka ƙaru a cikin wannan, in an sanar da kai, kuma me za ka yi asara, in ka jahilci wannan?

Yana daga cikin tambayoyin da ba a so, ka yi tambaya a kan abin da bai riga ya faru ba. Haka kawai ka ƙirkiro, in da abu kaza zai faru, menene hukunci? Irin waɗannan tambayoyi, Manzon Allah () ya ce, su suka halakar da waɗanda suke gabaninmu. 

1 comment:

  1. Masha Allah, Allah ya saka da alheri 🤲

    ReplyDelete

KITABUT-TAUHID (Babi Na Goma Sha Biyar15)

  SHARHI Babukan da suka wuce sun yi magana a kan yana daga dangin shirka neman taimako wajen wanin Allah. Wannan babi kuma zai nuna maka ...