GABATARWA.



WWW.TAFARKINSUNNAH.BLOGSPOT.COM

WANNAN SHAFI YANA DAUKE DA HADISAN ANNABI(SAW)ACIKIN HARSHEN HAUSA. IDAN ANGA MUNYI KUSKURE ASANAR DA MU.ALLAH YAYI MUNA JAGORA AMEEN!



DAMIN AIKO DA GYARA KO KARIN BAYANI;
{tafarkinsunnah@gmail.com]

Sep 14, 2011

ARBA'UNA HADITH (12) HADISI NA SHA BIYU

An karɓo daga Abu Hurairata (R.A) ya ce, Manzon Allah () ya ce, "Yana daga kyawun musuluncin mutum, barin abin da ba ya da muhimmanci a gare shi."(” Tirmizi (#2318) da Ibnu Majah (#3976).
                   
SHARHI
Faɗin Manzon Allah () cewa, "Yana daga kyawun musuluncin mutum, barin abin da ba ya da muhimmanci a gare shi." yana nufin, duk abin da ba shi da muhimmanci, to a rabu da shi. Wannan shi ke nuna kyautatuwar
musuluncinka. Wannan muhimmancin, ta fuskar addini ne, amma ta fuskar duniya, duk abin da ba shi da muhimmanci a duniyance, to kyawun musuluncinka, shi ne barin wannan al'amarin, amma duk abin da yake da muhimmanci ko ta fuskar addini ko ta fuskar duniya, to wannan ana buƙatar ka neme shi, dama an halicce ka ne domin Ibada. Allah yana cewa,

(Ban halicci mutum da aljan ba sai don su bauta mini) [Azzariyat 56] In ta fuskar duniya ne, Allah ya ce, (Kada ka manta rabonka daga duniya) [Al-ƙasas 77]. Amma duk abin da ba shi da muhimmanci a duniya ko lahira, to yana daga kyautatar imanin mutum, ya bar wannan shirmen, ya kama abin da zai amfane shi, ko a duniyarsa ko a lahirarsa. Waɗansu suna kafa hujja da wannan hadisin, cewa idan muna tattaunawa ni da wani ta addini, sai wani ya zo ya tsoma baki, sai mu ce ai Annabi () ya ce, "Yana cikin kyawun musuluncin mutum ya bar abin da bai shafe shi ba." don haka ba da kai muke magana ba, don me za ka tsoma baki? Ba haka hadisin yake nufi ba, abin da hadisin yake nufi, shi ne lallai mutum ya bar abin da ba shi da muhimmanci, ba wai abin da bai shafe shi ba. Domin tattaunawar da kuke yi, ko dai ta zamanto tana da alaƙa da ibada, to ta shafe ni, don ni ma musulmi ne, ina dangantuwa zuwa ga wannan addinin, ko ta zamanto tana da alaƙa da duniya, in na sani, dole in tsoma baki a ciki, ko ya zamanto a aikin saɓo kuke, ya wajaba a gare ni in yi hani daga mummunan aiki. To don me za ka ce ba ta shafe ni ba? Ta kowace fuska maganar ta shafe ni, sai dai idan saɓo kuke, na yi umarni kuka ƙi bari, sai in bar wajen. Wannan hadisi Imamu Tirmizi ya rawaito shi da sauran waɗansu malamai, kamar Ibnu Majah, da Imamu Ahmad a cikin Musnad, amma shi ya rawaito shi ba ta fuskar Abu Hurairata ba, ta fuskar Hasan Bin Aliyyu Bin Abi ɗalib ya rawaito shi. Hadisi ne ingantacce.

No comments:

Post a Comment

KITABUT-TAUHID (Babi Na Goma Sha Biyar15)

  SHARHI Babukan da suka wuce sun yi magana a kan yana daga dangin shirka neman taimako wajen wanin Allah. Wannan babi kuma zai nuna maka ...