GABATARWA.



WWW.TAFARKINSUNNAH.BLOGSPOT.COM

WANNAN SHAFI YANA DAUKE DA HADISAN ANNABI(SAW)ACIKIN HARSHEN HAUSA. IDAN ANGA MUNYI KUSKURE ASANAR DA MU.ALLAH YAYI MUNA JAGORA AMEEN!



DAMIN AIKO DA GYARA KO KARIN BAYANI;
{tafarkinsunnah@gmail.com]

Sep 12, 2011

ARBA'UNA HADITH (8) HADISI NA TAKWAS

An karɓo daga Abdullahi ɗan Umar (R.A) ya ce, "Lallai Annabi () ya ce, "An umarce ni in yaƙi mutane, har sai sun shaida babu abin bauta wa bisa cancanta sai Allah, (sun yarda Annabi) Muhammad Manzon Allah ne, su tsayar da sallah, kuma su bayar da zakka. Idan sun aikata haka, sun kare jininsu da dukiyoyinsu daga gare ni, sai da haƙƙin musulunci, hisabinsu yana wajen Allah Maɗaukaki." Bukhari (#25) da Muslim (#22) ne Suka ruwaitoshi.
                       
SHARHI
Da Annabi () ya ce, "An umarce ni in yaƙi mutane....", a nan kafuai ake nufi, ba dukkan mutane ba. Wannan wani salone na larabci, salo ne na Alƙur'ani, salo ne na hadisi, a
kawo gamammen lafazi, amma ana nufin keɓantanttun mutane, ko a kawo keɓantattun mutane ana nufin gaba ɗaya.

Faɗinsa kuwa cewa, "....sai da haƙƙin musulunci...." yana nufin sai sun karya wata dokar musulunci wacce ke sa a zubar da jinin mutum, to a lokacin sai a zubar da jinin nasu. Wato sai ya zama haddi ne, ba wai don kasancewarsu kafirai ba, Sai don kasancewar sun taka wani haddi. Kamar mutum ya kashe ɗan uwansa musulmi, kisa na ganganci, ka ga akwai haddi a kansa, sai dai idan waliyyan wanda aka kashe sun ce suna son diyya, to sai a
koma kan diyya a bar ƙisasi.
Fadifisa kuwa, "....hisabinsu yana wajen Allah." yana nufin shi (Manzon Allah () zahiri ya sani, bai san baɗininsu ba. In sun faɗi kalmar shahadar nan da gangan, a zuciyarsu babu ita, wannan su da Ubangijinsu ne, shi ne ya san abin da ke cikin zuciya, ni ban sani ba, in sun faɗa da yaƙini da gaskiya, to wannan Allah ya san abin da ke cikin zuciyarsu na imani, zai kuma yi musu sakamako gobe kiyama gwargwadon abin da ke cikin zukatansu. Wannan sai yake nuna idan mutum ya furta kalmar shahada, za ka ɗauke shi a asalin musulmi, har sai lokacin da ya yi wani abu da k warware ta, sannan ne za  cire shi daga wannan asali zuwa ga wani abin daban. Amma matukar mutum ka gan shi a yau musulmi, ka ce kai musulmi ne? Ya cc, "Eh! Ni musulmi ne.", to ba ka da damar ka ce da shi aƙidarka ba ta da kyau, har sai ka ga cikin maganganunsa ko ayyukansa, wani abu ya bayyana da ke warware musulunci, to a lokacin nan sai ka tambaye shi abu kaza, da kaza, da ka yi yana warware musuluncin mutum, saboda dalili kaza, da kaza. Amma ya ce, "Eh! Na sani yana warwarewa, amma duk da haka na yi." To wannan ya tabbatar wa kansa kafirci. Ko kuma ya ce ban sani ba, sai a yau, ko ya ce ai abin nan da ka faɗa yana warware musulunci, ni ban yarda ba, wannan dalilan da ka faɗa ban gamsu da su ba, ina da dalilan da aka faɗa min, wanda nake ganin sun fi naka karfi. To a nan wurin aiki ne ya same ka wajen gamsar da shi da dalilai, don ka nuna masa naka sun fi nasa.

Cikin wannan hadisin, akwai wani abu, Annabi () ya ƙirga, abubuwa guda uku: (Kalmar shahada, tsayar da sallah, bayar da zakka), sai ya ce, "....Idan sun aikata haka, sun kare jininsu da dukiyoyinsu daga gare ni, sai da haƙƙin musulunci...." Mu kuwa mun riga mun san cewa, kalmar Shahada kaɗai tana shigar da mutum musulunci. Yanzu idan mutum ya zo ana cikin yaƙi tsakanin kafirai, sai ya yi kalmar shahada, za ka kyale shi a matsayin ya musulunta, ba za ka ce a'a! sai ka yi sallah a gabana ko kuwa in kashe ka ba. Amma dangane da abin da ya sa Annabi () ya kawo abubuwa guda uku a jere, shi ne sai malamai suke cewa, asali idan mutum ya zamanto ba musulmi ba ne, sai ya zamanto ya furta kalmar shahada, kalmar shahadan nan ta biya, ta riga ta wadatar, ta shigar da shi musulunci. Yanzu idan ya ƙi yin sallah kuma, sai dai a ce haddi ne, za a kashe shi ne, don haddi ba don kasancewarsa kafiri ba. Idan mutane suka ƙi bayar da zakka har aka yaƙe su, to wannan ana kashe su ne don ladabtarwa, ba don kafirci ba. Don haka farko idan mutum ya zo zai shiga musulunci, kar ka yi masa dogon sharhin cewa musulunci yana da rukunai guda biyar, kalmar shahada, da sallah, da zakka, da azumi, da kuma hajji, ka ce wai sai in ya yarda da su gaba-ɗaya tukun. Ba haka ake karantarwa ba, abin da kawai za ka bayyana masa, shi ne ma'anar kalmar shahada. In ka sanar da shi ita, ya yarda, to sannan sai ka ce, to kuma abu na biyu da ke biyowa shi ne sallah. In ya yi sallah, sai zakka. Da haka, da haka, za ka isar masa musulunci. Amma lokaci guda, ba ka ɗora wa mutum dukkan waɗannan abubuwa gaba-ɗaya ba.

Ka duba hadisin Mu'azu bin Jabal () da aka tura zuwa Yemen, abin da Annabi () ya ce masa, shi ne, "In sun yi maka biyayya kan kalmar shahada, sai ka ba su labari an wajabta musu sallah biyar a yini da dare." Ya ce, "In sun yi maka biyayya kan wannan, ka ba su labari Allah ya wajabta musu yin zakka." Haka aka dinga ɗora masa, ka yi wannan, in an gama da wannan, sannan ka yi wannan. [Duba Bukhari (#1458)] A riwayar da Muslim ya rawaito (#19) a wannan hadisin, ya ce "Har sai sun shaida babu abin bautawa bisa cancanta sai Allah, kuma sun yi imani da ni, kuma sun bi abin da na zo da shi." Don haka malamai suka ce, duk wanda ya ƙi kalmar shahada, ya ƙi yin ta, to bai zama musulmi ba, amma idan mutum ya yarda da kalmar shahada ya ƙi yin sallah, sai malamai suka yi saɓani: Mai barin sallah, shin kafiri ne, ko ba kafiri ba ne? Amma wancan na farkon, babu saɓani. Haka idan mutum ya ƙi ba da Zakka, nan ma sun yi saɓani, kuma suka bambance idan mutum ɗaya ya ƙi ba da Zakka da kuma taron mutane in suka ƙi ba da zakka. Suka ce, idan mutum ɗaya ya ƙi bayar da zakka, to in akwai gwammatin musulunci, sai ta yi amfani da ƙarfi, ta fitar da zakkar ko ya ki ko ya so. In kuwa jama'a ne suka ƙi bayarwa, to su ma imma ya zamanto suna da ƙarfi, ta yadda za su iya ɗaukar makami su kare kansu, imma ya zamanto ba su da ƙarfi, a iya murƙushe su a karɓa, to sai a murkushe su a karɓa. In kuwa suna da karfi, sai a yaƙe su, kamar yadda sayyidina Abubakar (R.A) ya yaƙi waɗanda suka hana zakka a lokacinsa. Ya ce, "Ko da dabaibayi kuke bayarwa lokacin Annabi (), yanzu kuka hana, to sai na yaƙe ku a kai." [Duba Bukhari (#1399) da Muslim (#20)].

No comments:

Post a Comment

KITABUT-TAUHID (Babi Na Goma Sha Biyar15)

  SHARHI Babukan da suka wuce sun yi magana a kan yana daga dangin shirka neman taimako wajen wanin Allah. Wannan babi kuma zai nuna maka ...